Madalla da yunkurin amfani da sufuri don bunkasa ilimi a Katsina

A wannan makon, mun samu tsokacin ne daga Malam Hassan B. Nagado, mazaunin Dutsin-ma, ta hanyar adireshinsa na I-mel: [email protected] Ga abin da tsokacin nasa ya kunsa: Sufuri na daya daga cikin muhimman ayyukan raya kasa da kan kawo ci gaban al’umma, ya kuma samar da habbakar arziki, samar da ayyuka, habbaka aikin noma da […]

Madalla da yunkurin amfani da sufuri don bunkasa ilimi a Katsina

Dandazon Gizagawan Zumunci, a zauren taron bana da aka gudanar a Sakkwato, kwanakin bayaA wannan makon, mun samu tsokacin ne daga Malam Hassan B. Nagado, mazaunin Dutsin-ma, ta hanyar adireshinsa na I-mel: [email protected] Ga abin da tsokacin nasa ya kunsa:
Sufuri na daya daga cikin muhimman ayyukan raya kasa da kan kawo ci gaban al’umma, ya kuma samar da habbakar arziki, samar da ayyuka, habbaka aikin noma da rage tururuwar jama’a daga kauyuka zuwa birane.
Sanin wannan ne ya sa gwamnatoci a duk fadin duniya suke maida hankulansu domin samar da ingantattacen sufuri domin samar wa jama’arsu hanyoyin ci gaba da al’ammuransu gaba daya. Wannan ya sa ake samar da makudan kudade domin samar da hanyoyi da kuma motocin sufuri, a matsayin daya daga cikin muhimmman abubuwan more rayuwa da gwamnatoci ke samar wa al’umma.
Wannan ne ya sa Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Barrister Ibrahim Shehu Shema ta samar da motocin sufurin da babu irinsu a kasar nan, domin rage yawan hadurran motoci, mutuwar al’ummarta, tallafa wa tafiyar da harkokin samar da arziki, rage tururuwar mazauna kauyyuka zuwa birane da kuma samar da aikin yi ga jama’a.
Jihar Katsina ta kasance mai fadin gaske kasa da yawan al’umma da kuma yawan makarantu da kauyuka da tazararsu ta fi na mafi yawan jihohi da ke kasar nan. Wannan ya sa samar da ingantattar hanyar sufuri ya zamo wani aiki da ya ta’allaka da ci gaban kasa. Kodayake gwamnatoci da dama sun yi kokarinsu wajen samar da irin tasu fahimtar da bangaren sufuri, an ci gaba da samun kalubale ta hanyar sufuri a jihar.
Sakamakon wannan ne ya sa daga 2003 zuwa yau, Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina ta yi garanbawul ga motocin sufurin da ta tarar a baya, sannan ta kawo fiye da motoci 120 domin rage wahalhalun da ke faruwa ga al’ummar Katsina; sakamakon rashin sufuri mai inganci. Kudin sufuri ya ragu, motoci sun samu, ayyuka ga jama’a sun karu, wahalhalu domin tafiye-tafiye sun ragu, safarar kayayyaki sun habbaka, sannan uwa uba, kamfanin sufuri na jiha ya zamo gagara gasa, in an kwatanta shi da takwarorinsa na sauran jihohi.
A yau, sufuri da tafiye-tafiye a Jihar Katsina da kuma fadin Najeriya ya zamo cikin sauki da araha da kuma holewa saboda motocin ba wai sababbi ba ne kawai, a’a, an kawata su da kayan shakatawa da kan sa fasinja jin dadin tafiyarsa. Bugu da kari, a cikin Jihar Katsina, babu wani lungu da a yanzu motocin nan ba sa zuwa, ta yadda a ayau kayan noma da ’yan kasuwa na iya shiga ko’ina domin saye da sayarwa.
Wannan bai tsaya nan ba, a makon nan, Gwamna Ibrahim Shehu Shema, tare da taimakon Janar-Manaja na kamfanin sufuri na jiha, Alhaji Gambo Rimi; suka kaddamar da motocin sufuri da aka yi wa lakabi da “Sufuri Mai Sauki Domin ’Yan Makaranta.” Tsarin ya samar da motocin masu dimbin yawa domin ’yan makaranta, ta yadda za su iya zuwa karatu ba tare da bata lokaci ba. Shirin, wanda kacokan na Gwamnatin Jihar Katsina ne, karkashin jagoranci da hange mai nisa na Gwamna Ibrahim Shema, zai taimaka gaya wajen habbakar ilmi da rage matsalolin sufuri da ’yan makaranta ke samu.
Shi wannan shiri, tuni ya samar da dogayen motocin Coaster ga kowace makaranta da ke jiha, domin inganta sufuri da yadda makarantu za su samu saukin tafiye-tafiye domin samun ilmi mai inganci a jihar baki daya.
Da yake kaddamar da shirn, Gwamnan, wanda da kansa ba aike ba ya kaddamar da shirin, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar wa al’umma da ababan more rayuwa; ta yadda nan gaba kadan Jihar Katsina za ta zamo mafi ci gaba a harkokin samar da ababen more rayuwa a duk fadin kasar nan.
Ya ce samar wa makarantu wadannan motoci wata hanya ce ta inganta harkokin ilmi, ta yadda ’ya’yanmu za su samu natsuwar koyo da yin karatu ba tare da fadawa cikin wahalhalu ba, a lokacin zuwa makaranta.
Ya kuma yi albishir ga sauran bangarorin al’umma cewar gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da kayan more rayuwa, ta yadda nan gaba kadan jihar za ta zamo abar sha’awa ga sauran jihohi, ta hanyoyi daban-daban. Gwamnan ya kuma tabbatar wa al’umma cewar gwamnatinsa za ta gama duk wasu ayyukan ci gaba da ta fara ta, yadda Katsina za ta ci sunanta na jagora ga harkokin ilmi da zamantakewa da kuma zaman lafiya.
Tuni an gama shirye-shirye, ta yadda za a raba motocin ga makarantu domin inganta harkar sufuri da ilmi da kuma rage wahalhalu ga daliban wadannan makarantu da ke cikin jihar gaba daya. Maganar makara zuwa karatu ta kare a Jihar Katsina.
Wannan ba karamin ci gaba ba ne ga harkar ilmi da kuma sufuri baki daya. Rokonmu a nan shi ne, wadanda aka damka wa alhakin tafiyar da motocin za su rike amanar da aka ba su, ta yadda ba za su karkatar da akalar motocin
domin gashin kansu ba, ba kuma za su karkata su zuwa wasu wurare ba da zai hana dalibai cin albarkacin wannan muhimmi kuma kyakkyawan kudiri na gwamnati, mai albarka, mai kuma kula da jama’arta.