Madalla Malam Mansur Liman da wannan adalci

“Assalam Alhamdulillah ina farin cikin shaida ma  cewa, Ni, da Falalu yanzu hakarmu ta cimma ruwa. Falalu ma, har ya karbi takardarsa ta komawa aiki tun a cikin makon da ya wuce, ta wa kuma na bisa hanya In sha Allahu. Muna dada godiya gareku masoya na hakika, bisa ga gudummuwa da taimako da kuka […]

Madalla Malam Mansur Liman da wannan adalci

“Assalam Alhamdulillah ina farin cikin shaida ma  cewa, Ni, da Falalu yanzu hakarmu ta cimma ruwa. Falalu ma, har ya karbi takardarsa ta komawa aiki tun a cikin makon da ya wuce, ta wa kuma na bisa hanya In sha Allahu. Muna dada godiya gareku masoya na hakika, bisa ga gudummuwa da taimako da kuka yi ta ba mu don nema mana mafita daga wannan iftila`i. Allah Ya saka muku da mafificiyar Aljanna (Firdausi). Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya sa mu cikin masu ikhilasi da takawa don samun rabauta da mafifitan falalolinSa da rahamominSa na duniya da lahira. Ameen! Na gode Abubakar Abdurrahaman.”     

Mai karatu wadannan kalamai da makamantansu na daga cikin sakon kar ta kwanan da tsohon Janar Manajan tashar FM ta Radiyon tarayya wato FRCN da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara kuma tsohon abokin aikin aiki Malam Abubakar Abdurrahaman, ya turo mini, yana mai addu`a ga Allah, tare da yi mini albishir da irin yadda Allah Ya kawo musu karshen korar karen da tsohon Darakta Janar na Hukumar gidajen Rediyon FRCN din Malam Ladan Salisu ya yi masa shi da Alhaji Falalu Ibrahim Babban mai binciken kudi wato Cif, kuma mai rikon mukamin mataimakin Darakta na fannin a gidan Rediyon tarayya na Kaduna, tun a ranar 23 ga watan Disamban 2014

Malam Ladan Salihu, dan jarida ne da ya dade yana aikin jarida, daga cikin irin wuraren da ya yi aiki har da Tashar talabijin ta kasa wato NTA, daga bisani kuma ya koma Hukumar kula da gidajen yada labarai ta NBC, inda ya kai mukamin Darakta. Yana kan wannan mukami ne a cikin watan Fabrairun 2007, gwamnatin PDP, a lokacin mulkin shugaban kasa Cif Olusegun Obasnjo ta nada shi Daraktan shiyya na gidan Rediyon tarayya na Kaduna. A iyakacin sani na Malam Ladan, shi ne mutum na farko daga waje da ya taba rike tashar ta Kaduna, a tarihin kafuwarta na shekara 45, a lokacin (1962 zuwa 2007).

Likkafar Malam Ladan ta ci gaba, a cikin watan Fabrairun 2014, lokacin da Gwamtin Shugaba Dokta Goodluck Jonathan, ta daga likkafarsa ya zama  Oga kwata-kwata, wato Darakta Janar na Hukumar gidajen Radiyon tarayya wato FRCN, mukamin da ya rike har zuwa cikin watan Fabrairun 2016, da Gwamnatin sShugaban kasa Muhammadu Buhari ta sauke shi, bayan ya samu shekaru bakwai tsakanin Kaduna da Abuja.

Bayan komawarsa Abuja ne a watan Fabrairun 2014, a matsayin  sabon Darakta Janar na FRCN, Malam Ladan, an wayi gari a  ranar 23  ga Disambar 2014, ya ba da shelar korar Alhaji Falalu Ibrahim da Malam Abubakar Abdurrahaman daga aiki, kamar yadda na ambata tun farko, ba tare da bin ka`idoji balle sharudda da tanade-tanaden sallamar ma`aikacin gwamnati suka tanada ba, kamar na bayar da tuhuma da gargadi na daya har zuwa na uku, duk kafin akai ga kora.

Laifin Malam Falalu, shi ne a zamansa na babban mai binciken kudi na Radiyo Kaduna, shi ya ba da gamsasshiyar shaidar Malam Ladan ya yi amfani da rasidin karya mai lamba 15051 da sunan na gaskiya ne a gidan rediyon ga tsabar kudi Naira miliyan biyar da dubu dari shidda da ashirin (N5,620,000), da Gwamnatin Jihar Katsina ta biya tashar a kan wani shirinta na GABA DAI GABA DAI JIHAR KATSINA, bayan karbar kudin ne ya sa wa ajiyar gidan Rediyon Kadunan Naira dubu dari biyar (N500,000). Bayyanar wannan sata ko zamba da aka zargi Malam Ladan da aikatawa  ta sanya Ministar Yada labaran wanccan lokacin marigayiya Farfesa Dora Akunyili ta sa aka dakatar da Malam Ladan har tsawon watanni shidda. Ana zaman jiran jin an kori Malam Ladan daga aiki, bisa ga sakamakon binciken da aka yi, kwatsam, sai aka ji an maido da shi bakin aiki.

Shi kuwa Malam Abubakar a zamansa na Janar Manajan tashar FM ta gwamnatin tarayya a Gusau babban birnin Jihar Zamfara, babban laifinsa shi ne an ce ya dawo Kaduna, amma bai dawo ba. Mai karatu ka iya cewa kin bin umurni babban laifi ne a cikin tsarin aiki, amma kuma wani hanzari ba gudu ba, shi ne rashin bi-biyarsa da tuhuma kamar yadda tsarin aiki ya tanada, har a kai makura, ta rusa korar da a ka yi masa.

Hasali ma yanzu da sabon Daraktan FRCN Malam Mansur Liman da aka nada a cikin watan Mayun bara, ya waiwayi korafe-korafen su Malam Falau da Malam Abubakar suka sake gabatar masa don samun adalcin da ya kamata. Kwamitin da ya bi sawun al`amarin ya gano cewa, da rana daya ba a ba wadancan ma`aikata biyu damar kare kai ba. Ita kanta ma`aikatar Yada labarai da Hukumar Daraktocin FRCN da Malam Ladan yake mamba, kuma Sakatarenta  ba su da masaniyar korar ma`aikatan biyu, daga baya kuma duk kokarin da Ma`aikatar ta yi na ganin an mayar da ma`aikatan, ta kwamitin da ta kafa, Malam Ladan ya yi ta shiga yana fita, ya kuma yi amfani da matsayin da yake kai na Darakta Janar, ya yi ta tadiye ayyukan kwamitin, tare da hadin bakin wasu daga cikin manyan ma`aikatan ma`aikatar da wasu Daraktocin gudanarwarsa.

Haka aka yi ta zama har zuwa lokacin da aka sallami Malam Ladan daga mukamin Darakta Janar na FRCN a farko-farkon watan Fabrairun bara aka nada Malam Mansur Liman watanni uku bayan sallamar Malam Ladan, wato cikin watan Mayun baran. Zuwan Malam Mansur Liman din ne ya sa su Malam Falalu suka sake gabatar da koke-kokensu, da Allah Ya amsa musu zuwa yanzu har suke hamdala ga Allah da sabon Daraktan Janar Malam Mansur Liman da Allah Ya nuna masa karshen iftila`in da suka shiga a hannun tsohon Darakta Janar Malam Ladan.

Ina fatan mai karatu zai iya tunawa cewa a wani lokaci cikin shekarar 2015, a wannan fili, na yi rubuce-rubuce har sau biyu  da kuma a jaridar Leadership Hausa, a zaman martani ga abokin aiki Malam Babangida Kakaki, da ya yi rubutu a jaridar Leadership Hausa, din yana ta yaba kyawawan ayyukan ci gaba da shugabanci nagari irin na Malam Ladan a cikin `yan watannin da ya yi na zamansa Darakta Janar na FRCN, ba tare Malam Kakaki ya waiwayi barnar da Malam Ladan ya tafka a Kaduna ta zamba da korar karen da ya yi wa wadancan jajirtattun ma`aikatansa na tashar Kaduna ba. Ma`aikatan da a kasar da aka san kima da martabar aiki ce da bayan ba su lambobin yabo har karin girma sai an yi musu, shi kuma Malam Ladan da an sauke shi daga kan mukaminsa, kuma a gurfanar da shi gaban Kuliya, amma sai ma daga likafarsa aka yi, kamar yadda ka`idar aiki ta tanadi a saka wa ma`aikaci mai kwazo, karin girman da ya ba Malam Ladan damar ya ci gaba da cin karensa ba babbaka yana barje guminsa.

Kai tsaye ka iya cewa Malam Ladan ya dauki wadancan matakan a kan ko dai don bai san dawon garin ba, ko kuma shaidan ya rika zuga shi a kan ba wanda ya isa sai shi, to yanzu ina fata zai san cewa Allah ne Isasshe. Allah kuma Ya sa ya fara koyon karatun zama da karatu. Su kuma da yanzu suka samu biyan bukata, Allah Ya sa kaffara ne gare su bisa ga jarrabar da suka shiga. Ga Malam Mansur Liman ina mai cewa Madalla! Madalla!! Madalla!!! da addu`ar Allah Ya kara masa jagora da daukaka ya gama lafiya, Ya raba shi da miyagun mashawarta, manya da kanana na ciki da wajen FRCN. Amin summa amin.