Madara ko omo?

Wani Bahadeje ne da ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jikkar omon ‘Good Mama’ ya ce a ba shi jikka daya. Shi ya zaci madarar gari ce ta leda. Ya amsa ya nufi teburin mai shayi, ya samu wuri ya zauna. Ya […]

Madara ko omo?
Madara ko omo?

Wani Bahadeje ne da ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jikkar omon ‘Good Mama’ ya ce a ba shi jikka daya. Shi ya zaci madarar gari ce ta leda. Ya amsa ya nufi teburin mai shayi, ya samu wuri ya zauna. Ya ce wa mai shayi a zuba masa amma kar a sa madara. Bayan an ba shi ruwan shayi, sai ya dauki kofi daya daban ya zazage farin omon nan, ya zuba ruwan shayi ciki ya fara shekawa. Kafin ka ce kwabo sai kumfa ta cika kofin har tana zuba. Shi kuwa sai ya ce: “Aradu wannan ai fitsarin jaki ne!”

Daga T. A. Buhari 08092055700