Madigo: Wannan bala’i har ina?!
Ba boyayyen abu ba ne ga masu sauraren kafafen watsa labarai cewa wasu mata musulmai sun auri junansu (madigo) a kan abin da malamai ba za su so a kira shi da sadaki ba na Naira 5,000 kacal a nan Najeriya a kuma cikin wata jiha a Arewa!Tun kafin haka, wannan bala’in na madigo ya […]
Ba boyayyen abu ba ne ga masu sauraren kafafen watsa labarai cewa wasu mata musulmai sun auri junansu (madigo) a kan abin da malamai ba za su so a kira shi da sadaki ba na Naira 5,000 kacal a nan Najeriya a kuma cikin wata jiha a Arewa!
Tun kafin haka, wannan bala’in na madigo ya dade da baje kolinsa kuma yana cin karensa ba babbaka a
cikin makarantun kwana na ’yan mata da makarantun gaba da sakandare da garuruwa da unguwanni da gidaje. Kai, har a tsakanin ya da kanwa ma ana yi, balle kawa da kawa ko babba da karama!
Kada ka yi min gardama domin suna ba da kyaututtuka tare da nuna soyayyarsu da kishinsu a fili da (kuma a) waya, kai ka ce saurayi da budurwa ne, su ma wadanda ba su san ciwon kansu ba. Za ka iya gaskata ni idan na ce suna kiran kansu da ‘lobers’ da ‘daughters’.
Wallahi, wannan ne ya sa na kasa hakura, sai na yi aniyar jawo hankalin masu yi da al’umma gaba daya da
alkalamina, domin neman tsira a gobe kiyama. Bisa ga haka ne na kalli madigo a fuska uku kamar haka:
1. A Musulunce
A tarihi, ba a yi wannan ta’asar ba a lokacin Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam -S.A.W), sai a yanzu da duniya ta zo karshe, amma duk da haka, ga wani hadisin Abi Sa’id, Allah Ya yarda da shi, cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Kada namiji ya kalli al’aurar namiji, kada mace ta kalli al’aurar mace, kuma kada namiji ya kunsu da namiji cikin tufa (bargo) daya, kuma kada mace ta kunsu da mace cikin bargo daya”. Muslim daTirmizi da Abu Dawud ne suka ruwaito shi.
’Yan uwa mu dubi hanin da aka yi da kyau, to kuma ina ga mace ta ji dadi da mace ’yar uwarta har ta samu biyan bukata? Don haka dukkanin malamai sun hadu a kan cewa madigo haramun ne. Hukuncinsa kuma alkali shi zai ga abin da ya dace ya yi musu, watau ko dai dauri ko tara ko bulala ko duka ukun ko wani abin daban wanda ya dace. Ta yadda, idan an yi hukuncin, ba wadda za ta so cin kashin da aka yi musu, a yi mata. A tunani mai kyau ma, abin bai dace ba, domin Allah Ya halitta maza da mata, ke nan babu dalilin da zai sa mace ta je wa ’yar uwarta, ban da rashin tunani. Allah Ta’ala Ya ce, “Kuma daga komai Mun halitta nau’i biyu, watakila za ku yi tunani”. (Dhariyat:49).
2. A Likitance
A. Binciken da wani masani mai suna Rankow ya gudanar a shekarar 1995 ya nuna cewa ana samun karuwar wadannan cututtukan a tsakanin masu madigo:- Sankara ta cikin jini; tunjere da kuma kwayoyin cuta masu yawa (birus). karshe ma likitoci sun tabbatar da cewa ana daukar cutar nan ta kanjamau (HIb/AIDS) ta hanyar madigo.
B. Ciwon sankara ko ciwon daji (cancer)
Wani bincike da aka gudanar a Amurka, a wata jami’a mai suna U.S. National Cancer Institute a shekarar 1993 ya nuna cewa a cikin ’yan madigo, an samu karuwar sankarar nono, idan aka kwatanta su da wadanda ba ’yan madigo ba. Haka kuma binciken ya nuna karuwar sankarar bakin mahaifa da sankarar jakar kwai da sankara ita mahaifar kanta da kuma sankarar uwar hanji. Dukkanin wadannan cututtukan sun fi yawa a tsakanin ’yan madigo.
C. Ciwuka masu dadewa a jiki
An gano, a taron kara wa juna sani da aka yi a Landan, a ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 2002, cewa ’yan madigo su ne suka fi kamuwa da ciwace-ciwace irin su ciwon zuciya da ciwon suga da asma da kuma ciwon wajen ’yan hanji wadanda suke matukar dadewa a jiki.
D. Abin da ya shafi kwakwalwa
Bugu da kari, a wani taron kara wa juna sani da aka gudanar a Caldadale Pride a shekarar 2001, an nuna cewa kashi 87 na ’yan madigo na samun ciwon damuwa ta kwakwalwa, wadda kan dade a tare da su. Sannan kashi 80 suna tunanin kashe kansu. Haka kuma an samu kashi 67 na samun damuwa akai-akai mai cin rai, sannan kuma kashi 13 daga cikin dari sukan kashe kansu.
3. A zamantakewar al’umma
a. Gurbata Tarbiyya: Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa kawance tsakanin mata abu ne da suke girmamawa. Wannan kuwa yana taka muhimmiyar rawa a wajen yada madigo a tsakaninsu, ta yadda wadda ke yi, ke yi wa kawayenta hudubar shaidan domin jawo hankalinsu ga yin barna. Wannan, ko shakka babu, ya rura wutar wannan bala’in har ta koma ta daji,d omin hakan ya jawo mata da yawa sun kusta kai a cikin kogon wannan barna, daga matan aure da ’yan mata da zawarawa da ma manyan mata, har ma ya sa masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum ke ganin an fi yin madigo fiye da yadda ake yin luwadi!
Wannan, ko ba a fada ba, an san madigo na bata tarbiyyar da iyaye suke yi wa ’ya’yansu mata wadanda kuma su ne uwayen al’umma duka, wanda bacinta kan kai su ga aikata miyagun laifuffuka.
b. Yana raba aure
Fadi da ihu, ka kara da busa, cewar madigo yana rarraba ma’aurata da yawa, don kuwa duk namijin da ya samu matarsa da laifin aikata madigo, to mafi yawanci yana sakinta ne, saboda zai yi wuya ta bari, don matan da ke wannan sabon, wai sun fi jin dadin mace fiye da namiji.
Inda ya kamata a gaskata ni shi ne, kafin na fara rubutun nan, sai da na gana da
wani malamin jami’a, wanda, cikin takaici, ya shaida min cewa amininsa dan kasuwa ne da yake fita kullum da safe zuwa kasuwa, ashe matarsa kuma tana amfani da wannan lokacin idan ya fita suna yin madigo da matar makwabcinsa. Ranar da dubunsu ta cika ne, bayan fitarsa, sai ya gane ya yi mantuwa, ya dawo gida domin ya dauka. Saboda gushewar hankalinsu, har ya shigo ba su ji shigowarsa ba. Matakin gaggawar da ya dauka a lokacin shi ne ya sake ta. Wanda hakan ya tabbatar mana da yana raba aure.
c. Yana hana aure
Aure ibada ne, to amma sai dai kash!, ’yan madigo sun yi hannun riga da shi, suna kyamar sunnar Manzon Allah (S.A.W), domin su, a rubabben tunanisu, tunda dai suna biya ma kansu bukata, to meye kuma na yin aure (haka su ma ’yan luwadi suke). Wannan ne ma ya sa ba karamin tilasci ne ke sa wa ’yan madigo su yi aure ba, domin su suna fifita madigon a kan aure. Wata dalibar jami’a, ’yar madigo, ta shaida cewar ita kwata-kwata ba ta sha’awar namiji, shi ya sa ma ba ta kula shi.
Ba ma haka ba, har mace ke auren mace, don tabewa.
Daga karshe, ina kira ga dukkanin bangarorin al’umma da su farka daga barcin da suke yi, su tashi tsaye don ganin sun yi wa wannan tufkar hanci ta kowace irin hantar da ta dace. Ina rokon Allah Ya shiryar da mu, Ya shiryar da masu yin wannan sabo, ba don halinsu ba, Ya sa mu fi karfin zukatanmu, amin summa amin.
Kabir Sa’idu dandagoro (Bahaushe), wakilin Mujallar Muryar Arewa a Katsina
08038387516 -kibdau:[email protected]