Madogara ga Ubangiji

‘Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukkan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.” Karin Magana 3:5-6 Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka. Barkanmu da sake saduwa a wannan lokaci […]

Madogara ga Ubangiji
Madogara ga Ubangiji

Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukkan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.” Karin Magana 3:5-6

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka. Barkanmu da sake saduwa a wannan lokaci da za mu yi nazari a kan dogara ga Ubangiji. A kowace rana mukan yi shirye-shiryen harkokin mu na yau da kullum, wadansu ma ba sa iya barci sai sun ga cewa sun lissafa, sun shirya harkokinsu na gobe. Yin shiri na da kyau kwarai da gaske amma idan muka sa komai cikin hannun Ubangiji Allah muka kuma dogara gare Shi cewa da ikonSa ne za mu ci nasara cikin shirye-shiryenmu. Karin Magana 16:1-3: Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce. Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji Yana auna manufarka. Ka roki Ubangiji Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za kuwa ka yi nasara cikin aikata su.

Duk shirin da mutum ke yi ba tare da nufin Ubangiji ba, to, wannan duk a banza ne dalili kuwa shi ne ba mu san abin da zai faru a yanzu ko nan da jimawa ba, Ubangiji kadai Ke da ikon sanin wannan. Shi ya sa yana da muhimmanci kwarai da gaske mu nemi nufinSa da jagorancinSa cikin rayuwarmu a koyaushe.

Bari mu ga misalin wani mai dukiya da Yesu Almasihu ya bayar cikin Littafin Luka 12:16-21. Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai dukiya ta yi albarka kwarai. Sai ya ce a ransa, ‘To, kaka zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina wasu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. Zan kuma ce wa raina, “Lallai ina da kaya masu yawa a jibge, tana nan shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagalina.” Amma Allah Ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karbi ranka. To, kayan da ka tanada, nawa za su zama?’ Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba ya kuwa da wani tanadi a gun Allah.” Haka rayuwar mutane da dama take a yau, mukan kwallafa ranmu ga tattalinmu ko mu ce arzikin da muke da shi, shin, wa ke ba da arzikin? Wa kuma ke da ikon karba? Idan fa haka ne, me zai hana mu neman wanda ke da ikon tanada wa Ya kuma karbe cikin kiftawar ido?

Kariya fa? Mun ga wadansu da sukan gina kariya kewaye da su, za ka gansu tafe da sojoji, ko ’yan sanda, motoci masu agaji, duk wannan na nufin ba wanda zai iya taba rayuwarsu. Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ke fadi game da irin wadannan mutane.

Irmiya 17:5-8, Ubangiji Ya ce, “La’ananne ne mutumin da ke dogara ga mutum, Wanda jiki ne makaminsa, Wanda ya juya wa Ubangiji baya, Gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A kasar gishiri, inda ba kowa. “Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa. Shi kamar itace ne wanda aka dasa a bakin rafi, Wanda ke mika saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin ’ya’ya ba.

Zabura 20:7-8, Wadansu ga karusan yakinsu suke dogara, Wadansu kuwa ga dawakansu, Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara! Za su yi tuntube su fadi, Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!

To ka ji, dogara ga karfi ko kariyar kanmu ba za ta hana mutuwa ko asara ba, bari madogararmu ta zama cikin Ubangiji da ke da iko bisa komai, gama zai aiko da mala’ikunSa su kare ka daga kowane irin bala’i.

Za mu rufe da Zabura 62:5-12:

Ga Allah kadai na dogara, A gare Shi nasa zuciyata. Shi kadai ne Mai kiyaye ni, Mai cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam. Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne Kakkarfan Makiyayina, Shi ne Mafakata. Ya jama’ata! Ku dogara ga Allah a kowane lokaci! Ku fada maSa dukkan wahalarku, Gama Shi ne Mafakarmu. Talakawa kamar shakar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma’auni, sam ba su da nauyin komai, Sun fi numfashi shakaf. Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar komai ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta ƙaru, Kada ku dogara gare ta. Sau daya Allah Ya fada, Sau biyu na ji, cewa Allah Yake da iko. Madawwamiyar kauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji! Kake saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa.

Shalom!

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos