Madrasatu Imam Malik Kafanchan ta yaye dalibai
Shugaban Makarantar Islamiyya ta Madrasatu Imam Malik da ke garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Malam Umar Faruk Jibril ya bayyana sakacin da iyayen yara wajen rashin nuna wa ’ya’yansu muhimmacin karatun addinin da cewa hakan ke taimakawa wajen cire wa yaran son karatun addini tun suna kanana. Malam Faruk ya bayyana […]
Shugaban Makarantar Islamiyya ta Madrasatu Imam Malik da ke garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Malam Umar Faruk Jibril ya bayyana sakacin da iyayen yara wajen rashin nuna wa ’ya’yansu muhimmacin karatun addinin da cewa hakan ke taimakawa wajen cire wa yaran son karatun addini tun suna kanana.
Malam Faruk ya bayyana haka ne a wajen bikin saukar karatun Alkur’ani Mai girma karo na biyu da makarantar ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce yin hakan na gurgunta karatun yaran domin suna ganin yadda iyayensu ke kashe dubban nairori wajen karatun boko amma a kan karamin kudin da za su biya musu a makarantar addini sun gwammace a kori yaran daga makaranta. Ya ce ta haka ne yaran ke lura da inda iyayensu suka fi ba muhimmanci.
Da ya waiwaya kan tarihin makarantar, Malam Umar ya ce ya kafa makarantar ce a 1999 da dalibai mata guda hudu kawai amma zuwa yanzu tana da dalibai akalla 200.
Yayin da daya daga cikin daliban da suka yi sauka mai suna Haruna Aliyu ke yi wa Aminiya karin bayani, ya yi kira ga matasa ’yan uwansa su yi amfani da kuruciyarsu wajen neman ilmin addini tun kafin dama ta kubuce musu.
Matashin ya ce ya yi amfani da lokacin da sauran takwarorinsa suke zuwa wasu harkoki ne ya dage da zuwa makaranta.
Ita ma Abida Muhammad da ta yi sauka ta yi kira ga ’yan uwanta mata su tashi tsaye wajen neman ilimin addini a matsayinsu na wadanda tarbiyyar yara ya rataya a kansu a matakin farko. Ta yi kira ga ’yan mata su dage da neman ilimi koda sun shiga dakunan mazansu ne kada su yi wasa da neman ilimi, inda ta ce duk da kasancewarta marainiya ba ta yi wasa ba ga shi har Allah Ya taimake ta.