Madrasatu Sheikh Hassan Surajo ta yaye 120 a Kaduna

A ranar Lahadin da ta gabata ne makarantar Islamiyyar nan da ke Titin Surajo a Tudun Wada, Kaduna wanda aka fi sani da Madarasatu Sheikh Hassan Surajo ta yaye dalibai 120, inda biyu daga cikin daliban suka haddace Alkur’ani Mai girma. An gudanar da bikin saukar ne a harabar filin Makarantar Firamare da ke titin […]

Madrasatu Sheikh Hassan Surajo ta yaye 120 a Kaduna
Madrasatu Sheikh Hassan Surajo ta yaye 120 a Kaduna

A ranar Lahadin da ta gabata ne makarantar Islamiyyar nan da ke Titin Surajo a Tudun Wada, Kaduna wanda aka fi sani da Madarasatu Sheikh Hassan Surajo ta yaye dalibai 120, inda biyu daga cikin daliban suka haddace Alkur’ani Mai girma.
An gudanar da bikin saukar ne a harabar filin Makarantar Firamare da ke titin Faki Road a Tudun Wada Kaduna, inda manyan baki da dama suka samu halarta.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin saukar, daya daga cikin manyan Malaman Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ibrahim Nakaka ya ce akwai jan aiki a gaban iyayen yara musamman wajen biyan kudin makarantar ’ya’yansu.
“Domin in ba ka biya kudin makaranta ba, yaya za a yi a biya malaman da suke koyar da danka? Saboda haka ina jawo hankalin iyayen yara su tabbatar suna biyan kudin makarantar ’ya’ansu. Biyan kudin makaranta yana da falalar gaske. Domin shi sha’ani na kowayarwa, abu ne mai muhimmanci, kuma mai matukar lada a wajen Allah,” inji shi.
Shugaban Malaman Makarantar, Malam Muhammad Hafizu Abdullahi ya ce makarantar tana daya daga cikin makarantun da suka jima suna bayar da ilimi a jihar.
Ya ce wannan ne saukan karatu karo na 47 a makarantar, kuma zuwa yanzu ta yaye dalibai 1,485, sannan yanzu haka tana da dalibai da suka kai 1,500.