Madrasatus Sabilir Rishad Suleja ta yi walimar saukar karatun Alkur’ani

A ranar Lahadin da ta gabata ce, Makarantar Madarasatus Sabilir Rishad da ke Unguwar Bakin Yara kusa da Fadar Sarkin Suleja, a Suleja Jihar Neja ta gudanar da bikin saukar karatun Alkur’ani Mai girma ga dalibanta 40. Walimar saukar karatun wadda ta gudana a karkashin Uban Taro Mai martaba Sarkin Suleja Alhaji Awwal Ibrahim wanda […]

Madrasatus Sabilir Rishad Suleja ta yi walimar saukar karatun Alkur’ani

A ranar Lahadin da ta gabata ce, Makarantar Madarasatus Sabilir Rishad da ke Unguwar Bakin Yara kusa da Fadar Sarkin Suleja, a Suleja Jihar Neja ta gudanar da bikin saukar karatun Alkur’ani Mai girma ga dalibanta 40.

Walimar saukar karatun wadda ta gudana a karkashin Uban Taro Mai martaba Sarkin Suleja Alhaji Awwal Ibrahim wanda Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Awwal Musa Ijakoro ya wakilta daliban da suka yi saukar sun rika karanto abin da ya sauwaka daga Alkur’ani Mai girma.

Malamin da ya gabatar da nasiha a wurin walimar Ustaz Muhammad Awwal Idris ya tunatar da jama’a ne kan muhimmancin koyon karatun Alkur’ani da falalar wadanda suke da ilimin Alkur’ani inda ya bukaci al’ummar Musulmi su guji fifita ilimin duniya a kan na addini.

Lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa Babban Limamin Suleja Sheikh dahir D. Shu’aibu ya yi fatar alheri ga daliban da suka yi saukar inda ya tunatar da su bayanan da Mai martaba Sarkin Katsina ya yi a yayin da suka halarci gasar Musabaka ta kasa da aka kammala a Katsina a makon jiya cewa, yanzu gasar ta game ko’ina a Najeriya, kuma wakilan Najeriya suna taka rawar gani a gasar ta duniya. Ya ce, Sarkin ya kawo misali da yadda zakarun gasar na bara mace da namiji suka zo na biyu a gasannin da aka gudanar a Saudiyya da Malesiya.

A tattaunawar Shugaban Makarantun Madarsatu Sabilir Rishad Malam Salihu Yakubu Liman Iya ya ce an kafa makarantar ce sama da shekara 100 da suka gabata, lokacin da kakansu marigayi Sheikh Adam Ahmad ya bude ta a matsayin makarantar allo a gidansa.

Malam Salihu Liman Iya mahaifinsu Malam Yakubu Adam Liman Iya tsohon Limamin Abaji ne ya fadada makarantar zuwa ta Islamiyya shekara 25 da suka gabata.

Ya ce wannan ne saukar Alkur’ani karo na 25, kuma daga mayar da ita Islamiyya dalibai 216 ne suka sauke Alkur’ani Mai girma inda dalibai maza da mata 40 suka sauke a bana.

Ya bukaci iyaye su rika tallafawa wajen daukar dawainiyar walimar daliban, kasancewa suna gudanar da makarantar ce kyauta kamar yadda magabatansu suka yi.