Madrid ba ta fitar da rai a kofin La-Liga ba – Zidane

Kocin kulob din Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi game da kofin La-Liga na Sifen a bana, inda ake sa ran a gobe ne kungiyarsa ta Real Madrid da kuma ta FC Barcelona za su yi wasanninsu na karshe don tantance kungiyar da […]

Madrid ba ta fitar da rai a kofin La-Liga ba – Zidane
Madrid ba ta fitar da rai a kofin La-Liga ba – Zidane

Kocin kulob din Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi game da kofin La-Liga na Sifen a bana, inda ake sa ran a gobe ne kungiyarsa ta Real Madrid da kuma ta FC Barcelona za su yi wasanninsu na karshe don tantance kungiyar da za ta dauki kofin a bana.
Kawo yanzu FC Barcelona ce take saman teburin gasar da maki 88 kuma za ta hadu a wasan karshe da kulob din Granada ne a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu.  Haka kuma Real Madrid ce take biye a teburin gasar da maki 87 yayin da ita ma za ta buga wasanta na karshe da kulob din Deportibo La-Coruna a gobe Asabar.  Dukkan wasannin za su gudana ne a lokaci daya da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya.
Idan FC Barcelona ta yi kunnen doki ko kuma ta samu rashin nasara a wasanta da Granada kuma Madrid ta samu nasara akan Deportibo, to Real Madrid ce za ta dauki kofin.  Amma idan FC Barcelona ta samu nasara a wasanta, ko Madrid ta samu nasara sai dai ta zama ta biyu.
Don haka yanzu masoya kwallon kafa a sassan duniya sun zuba ido su ga yadda wasannin za su kaya a gobe Asabar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa