Madrid ta cire rai a kofin La-Liga – Zidane
Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce kulob din ya fitar da rai a yiwuwar lashe kofin La-Liga a bana bayan kulob Atletico Madrid ya yi musu kafar ungulu da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar da ta gabata.A wata hira da kocin ya yi da kafar watsa labaran wasanni ta […]
Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce kulob din ya fitar da rai a yiwuwar lashe kofin La-Liga a bana bayan kulob Atletico Madrid ya yi musu kafar ungulu da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar da ta gabata.
A wata hira da kocin ya yi da kafar watsa labaran wasanni ta Fod Sport a Faransa ya ce zai yi wuya a yanzu kulob din ya wuce na FC Barcelona a teburin gasar ganin yadda Barcelona ta ba shi tazarar maki 12 yayin da saura wasanni 11 a kammala gasar.
Kawo yanzu Barcelona ce take saman tebur sai Atletico a matsayin ta biyu sannan sai Madrid ta kasance a matsayi na uku.
Sai dai a lokacin da manema labarai suka tambaye shi, ko yanzu ta karewa Madrid ke nan a kokarin lashe kofin sai ya ce komai zai iya faruwa, amma dai abu ne mai wahala a yanzu Madrid ta kamo Barcelona kuma har ta wuce ta.
Tun bayan wasan da Madrid da Atletico ne magoya bayan kungiyar suna nuna shakkunsu a kan kulob din na yiwuwar lashe wani kofi a bana.