Madrid ta fara yunkurin korar Zidane
Bayan kulob din Girona ya lallasa na Real Madrid da ci 2-1 a gasar La-Liga ta Sifen a ranar Lahadin da ta gabata, dan kwallon gaba a kulob din Cristiano Ronaldo ya koka da yadda kocinsu Zinedine Zidane yake tafiyar da ragamar kungiyar inda ya nuna yadda kocin yake sanya ’yan kwallon yin wasa sam […]

Bayan kulob din Girona ya lallasa na Real Madrid da ci 2-1 a gasar La-Liga ta Sifen a ranar Lahadin da ta gabata, dan kwallon gaba a kulob din Cristiano Ronaldo ya koka da yadda kocinsu Zinedine Zidane yake tafiyar da ragamar kungiyar inda ya nuna yadda kocin yake sanya ’yan kwallon yin wasa sam babu armashi.
Ronaldo ya ce a gaskiya ba ya jin dadin yadda kocin yake sanya su suke yin salon wasa a yanzu, da hakan ta sa kungiyoyin kwallon kafa a yanzu ba sa shakkarsu idan sun hadu.
Wadannan kalamai da dan kwallon ya yi, sun yi daidai da ra’ayin shugaban kulob din Florentino Perez inda ya nuna za su dibar wa kocin wa’adi idan hakan ta ci gaba da faruwa ko shakka babu za a maye gurbinsa inda ya ce tuni suka fara tantance sunayen kococin da za su iya maye gurbin Zidane idan an sallame shi.
Sai dai Ronaldo ya nemi Zidane ya canza taku, muddin yana son ci gaba da samun nasara a kakar wasa ta bana.
Magoya bayan kulob din Madrid da dama ba su ji dadin yadda kulob din Girona ya doke na Madrid a ranar Lahadin da ta wuce ba, da hakan ta sa yanzu kulob din FC Barcelona ya ba na Madrid tazarar maki 8 a gasar La-Liga a wasanni 10 kacal da aka yi.