Madrid ta kori kocinta Carlo Ancelotti

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar korar kocinsa Carlo Ancelotti bayan kulob din ya gama wasansa na karshe a kakar wasa ta bana a ranar Asabar da ta gabata. Carlo Ancelotti, dan kimanin shekara 55 ya samu nasarar lashe wa Madrid kofuna hudu […]

Madrid ta kori kocinta Carlo Ancelotti
Madrid ta kori kocinta Carlo Ancelotti

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar korar kocinsa Carlo Ancelotti bayan kulob din ya gama wasansa na karshe a kakar wasa ta bana a ranar Asabar da ta gabata.

Carlo Ancelotti, dan kimanin shekara 55 ya samu nasarar lashe wa Madrid kofuna hudu a bara da suka hada da kofin kalubale da aka fi sani da Copa Del Rey da kofin zakarun kulob-kulob na Turai watau (UEFA Champions League) a karo na 10 da kofin Club World Cup da kuma kofin UEFA Super Cup.
Sai dai a bana, kocin bai lashe wani kofi ga kulob din ba da hakan ta sa kulob din ya raba gari da shi.
Madrid ta yi ban kwana da kocin ne bayan ta rasa kofin Copa Del Rey da take rike da shi a matakin kusa da na karshe (kwata-Fainal) bayan kulob din Atletico Madrid ya fitar da ita, yayin da kulob din Jubentus na Italiya kuma ya fitar da na Madrid a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (shi ma kofin da Madrid take rike da shi) a matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal) a wasa zagaye na biyu sai kuma uwa-uba yadda FC Barcelona ta lashe kofin La-Liga na Sifen bayan Madrid ta ba ta tazarar akalla maki bakwai a lokacin da gasar ke gudana amma kulob din ya yi sakaci har Barcelona ta wuce shi inda ta lashe kofin da tazarar maki biyu a tsakani. Hakan ta sa kulob din ya tashi a tutar babu a kakar wasa ta bana.
Shugaban kulob din Madrid Florentino Perez a wani jawabi da ya yi wa gidan talajibi na Madrid (Madrid Tb) na korar kocin a ranar Talatar da ta wuce ya ce: “Muna sanar da ku cewa Hukumar gudanarwar kulob din Madrid ta yanke shawarar korar kocinta Carlo Ancelotti. Mun san wannan mataki da muka dauka zai ba kocin da wadansu daga magoya bayanmu mamaki amma babu yadda za mu yi, don ya zama al’adarmu ce a duk lokacin da wani koci ya kasa tabuka abin-a-zo-a-gani mukan sallame shi ne ba tare da bata lokaci ba, don Madrid ba karamin kulob ba ne a bangaren kwallon kafa a duniya. Don haka mahukunta kulob din suka yanke shawarar nemo sabon kocin da muke jin zai canza yadda al’amurra suke gudana a yanzu a kulob din, ta hanyar kawo sababbin dabarun da za su sa kulob din ya cigaba da lashe manyan kofuna a ciki da kuma wajen Sifen”.
Shugaban ya cigaba da cewa: “A shekarun biyun da koci Carlo Ancelotti ya yi da mu, ya samu amincewar mahukunta kulob din inda suka ba shi dama ya taka rawar da ta dace da shi, amma yanzu da al’amurra suka rincabe masa ne ta sa da yawa daga magoya bayan kulob din suka rika kiran da a kore shi kuma a maye gurbinsa da wani. Tun da mahukunta kulob din suna yi ne don farantawa magoya bayan kulob din a ko’ina a duniya rai ta sa muka yanke shawarar sallamar kocin a halin yanzu, kuma muna yi masa godiya a kan irin gudunmawar da ya ba kulob din da kuma yi masa fatan alheri a duk inda zai tsinci kansa a harkar horar da kwallo”.
Sai dai rahotannin da ke fitowa sun nuna akwai yiwuwar kulob din ya maye gurbin kocin da Rafeal Benitez, tsohon kocin Liberpool da yanzu haka yake horarwa a kulob din Napoli da ke Italiya. Shi kuma Ancelotti ana sa ran zai koma tsohon kulob dinsa a Italiya watau AC Milan don cigaba da horarwa.
Masana harkar kwallo suna ganin abin kunya ne a ce yadda Madrid take kashe makudan kudi wajen sayo zaratan ’yan kwallo a duk shekara amma kulob din ya kasa lashe ko kofi daya ne a kakar wasa.