Madrid ta soma nazarin dauko Haaland daga City

Ana rade radin kocin Madrid, Carlo Ancelotti na iya barin kungiyar a kaka mai zuwa.

Madrid ta soma nazarin dauko Haaland daga City

Erling Haaland

Real Madrid na nazari a kan dauko dan wasan gaba na Manchester City da Norway, Erling Brut Haaland a kaka mai zuwa.

Haka dai wani kokarin da kungiyar ke yi na kawo sabbin jini kungiyarta, wadanda suka hada da dan wasan tsakiya dan kasar Ingila, wanda ke wasa a Borussia Dortmund, Jude Bellingham.

Zakarun na nahiyar Turai sun yi amannar cewa su ne ke kan gaba daga cikin masu neman dan wasan gaban na Manchester City biyo bayan jerin tattaunawa da kungiyarsa.

Real Madrid din na kokarin dauko Haaland ne a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan gabanta, Karim Benzema mai shekaru 35.

Tun da farko Kylian Mbappe ne Madrid suka yi niyyar daukowa, amma shawarsa ta ci gaba da zama a Paris Saint Germain ta janyo tankiya da rashin jituwa tsakaninsu, kuma hakan ya sa shugaban Madrid, Florentino Perez ya kudiri aniyar mayar da hankali a wani wuri.

Ana rade radin kocin Madrid, Carlo Ancelotti na iya barin kungiyar a kaka mai zuwa, kuma hakan zai zo ne da sayen ‘yan wasan gaba da na tsakiya ciki har da Bellingham.

Tun da farko Perez ya yi niyyar dauko Haaland da Mbappe a lokaci guda.