Madrid za ta dauki Kane, Messi zai sake komawa Barcelona

Ana kuma alakanta Messi da cewar zai koma buga gasar kwallon kafa ta Amurka.

Madrid za ta dauki Kane, Messi zai sake komawa Barcelona

Harry Kane yana cikin jerin ’yan wasan da Real Madrid ke son zabar wanda zai maye gurbin Karim Benzema.

Kane, mai shekara 29, yana da sauran kunshin kwantiragin kaka daya da ta rage masa a Tottenham, wanda bai fayyace makomarsa ba kawo yanzu.

Benzema wanda ya bar Real Madrid, bayan shekara 14 a Santiago Bermabeu, ya bar gurbin da kungiyar ya kamata ta cike kafin fara kakar badi.

Sauran ’yan wasan da Real ke son tuntuba sun hada da dan wasan Napoli, Victor Osimhen da na Inter Milan, Lautaro Martinez da na Chelsea, Kai Havertz da kuma na Juventus, Dusan Vlahovic.

Real mai kofin zakarun Turai 14 ta dade tana son daukar Kane, bayan da fitattun ’yan kwallonta da yawa ke shirin barin Bernabeu a ƙarshen kakar nan.

Bayan Benzema da zai bar Real Madrid a kakar nan, sauran sun hada da Eden Hazard da Marco Asensio da kuma Mariano Diaz.

Idan wadannan ’yan wasan suka bar Real, kungiyar za ta samu rarar fam miliyan 77 da take biyansu ladan wasa da albashi da sauran tsarabe-tsarabe.

Har yanzu Real Madrid na ci gaba da tattaunawa da Borussia Dortmund kan daukar Jude Bellingham.

Shugaban Tottenham, Daniel Levy na fatan Kane zai ci gaba da taka leda a kungiyar, amma sai Real ta biya fam miliyan 100 kafin ta bari dan kwallon ya bar Tottenham.

Kane ya ci kwallo 280 a wasa 435, kuma saura kwallo 47 tsakaninsa da yawan ta Alan Shearer a Premier League na farko a cin kwallaye a gasar mai 260.

Benzema, wanda ke rike da Ballon d’Or, mai shekara 35, ya koma Real Madrid daga Lyon a 2009, inda ya lashe Champions Leagues biyar da La Liga hudu a Madrid.

Akwai yiwuwar Messi zai sake komawa Barcelona

Watakila Lionel Messi ya sake koma wa Barcelona bayan ya buga wa Paris St Germain wasan karshe ranar Asabar, in ji mahaifinsa Jorge Messi.

Barcelona ta hakura da dan wasan ya bar kungiyar a 2021, bayan da kungiyar ta fada matsin tattalin arziki, yayin da La Liga ta bukaci kungiyar da ta bi dokar kashe kudi daidai samu ta financial fair play.

Messi, wanda ya koma Barcelona tun yana dan karami mai shekara 13 a lokacin ya zama kan gaba a ci wa kungiyar ta Camp Nou kwallaye 672 a wasanni 778 a duka gasanni.

Daga nan ya koma PSG bayan yarjejeniyarsa ta kare a Camp Nou, inda ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyu.

Tattalin arzikin Barcelona na farfadowa, amma dai La Liga ta sanar da kungiyar cewa har yanzu da sauranta wajen kashe kudi, hakan ya sa ta kasa tsawaita yarjejeniyar Ronald Araujo da kuma Gavi.

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sha nuna sha’awar sake daukar tsohon kyaftin din kungiyar, amma kuma hakan zai sake shafar dokar Fair Play da take kokarin bin turba

Messi, wanda ya lashe Kofin Duniya tare da Argentina a Qatar a 2022 da daukar Ballon d’Or bakwai, ya ci League 1 sau biyu a PSG da French Super Cup a watan Julin 2022.

Sai dai Messi bai amince ya tsawaita yarjejeniyarsa da PSG ba, wadda za ta kare a kakar bana.

An dade ana alakanta Messi da cewar zai koma Saudi Arabia da taka leda a Al Hilal, wadda ta gabatar masa da yarjejeniya mai dan karen tsoka.

Idan Messi ya koma Saudi Arabia zai taka leda a gasar tare da Cristiano Ronaldo da ke wasa a Al Nassr, yayin da ake hasashen cewar shima Karim Benzema zai koma wasa a kasar da ke Gabas ta tsakiya.

Ana kuma alakanta Messi da cewar zai koma buga gasar kwallon kafa ta Amurka, wato Major League Soccer a Inter Miami.