Madubi: Kafin ka fara zagin shugaba ka kalli kanka!

Shin wace irin dabi’a ce ta same mu? Me ya sanya muka kasance masu aibata shugabanni a duk lokacin da muka ga dama? Shin wannan dabi’a ta dace kuwa, ko me za ta haifar mana a kasa? A shekara biyu da suka gabata, GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci kan illolin da ke tattare da wannan […]

Madubi: Kafin ka fara zagin shugaba ka kalli kanka!

Shugaba Muhammadu Buhari, yana jinjina ga Shehun Borno, Shehu Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi a ranar Litinin da ta gabata

Shin wace irin dabi’a ce ta same mu? Me ya sanya muka kasance masu aibata shugabanni a duk lokacin da muka ga dama? Shin wannan dabi’a ta dace kuwa, ko me za ta haifar mana a kasa? A shekara biyu da suka gabata, GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci kan illolin da ke tattare da wannan dabi’a ta zage-zage da la’antar shugabanni, saboda muhimmancin wannan tsokaci, ga shi mun sake kawo shi:

 

Mun kware sosai wajen zagin shugabanni da la’antarsu kan yadda suke gudanar da mulki ko kan wani al’amari da suka zartar. Ni kuwa na yi dogon nazari, na ga cewa ba haka ya kamata mu kasance ba. Abin da ya kamata mu yi shi ne, kafin mu zagi shugabanni, mu kalli kanmu, shin yaya muke gudanar da dan karamin shugabancin da Allah Ya dora mana, na ma’aikatarmu ko na sana’armu ko na iyalanmu ko na abokanmu da sauransu?

Kamata ya yi kafin mu shiga cikin wannan muguwar harka ta zagi ko la’antar shugabanninmu, mu nazarci halayenmu da ayyukanmu da dabi’unmu. Idan har muka kalli wadannan siffofi namu, za mu gano cewa, shin ya dace mu aibata shugabanninmu ko kuwa? Idan mun kasance masu kirki, masu gaskiya, masu adalci, masu sanin ya kamata; babu shakka wadannan hotuna da muka gani a jikinmu, ba za su ba mu damar zagi ko la’antar shugabanni ba, domin kuwa na tabbata haka za mu rika ganin shugabannin namu, kamar yadda muke.

Idan da muka duba madubi, sai muka samu akasin halayen da aka zayyana a baya, to ke nan kada mu raba daya biyu, haka shugabanninmu suke. Kila mu ga cewa muna aikata rashin gaskiya, muna cin amana, muna ha’inci da sauran miyagun halaye da dabi’u. Babu shakka nan ma za mu ga cewa shugabanninmu haka suke, don haka idan na zagi shugaba mara gaskiya, kuma ni ba ni da gaskiya, to na zagi kaina ke nan. Idan na la’anci shugaba, saboda ya ci amana ko ya ha’ince ni, alhali ni ma maci amana ne kuma maha’inci ne ni, babu abin da na yi ke nan sai zagin kaina. Burum-ta-ci-burum ke nan! Babu kuma abin da haka za ta haifar wa kasarmu sai karin lalacewa da gurBacewa, domin kuwa la’antar nan ce za ta ci gaba da bin mu.

Ya kai ma’aikacin gwamnati ko na kamfani! Kafin ka soki gwamnati, ka dubi kanka, shin kana aiwatar da aikin da aka dauke ka bilhakki da gaskiya da amana da kiyayewa? Kana zuwa aiki a kan kari kuma ka tashi a kan kari? Kana bin dokoki da ka’idojin aikin? Idan dai amsarka a’a ce, to bai kamata ka zagi Shugaban Kasa ko Gwamna ko Ciyaman na karamar hukumarku ba.

Kai ne cin hanci da rashawa, kai ne Boye fayil din ma’aikata. A matsayinka na akawu, kai ne aringizon kwangila, kai ne danne albashi ko fanshon ma’aikatan hukumarku, shin ta yaya kake zaton shugaban da ke mulkarka zai kasance? Lallai idan kana da wadannan halaye, ba ka da hujjar zagin Shugaban Kasa ko Gwamna don sun sace dukiyar kasa. A hannu daya, idan ka zama akasin haka, wato halayenka suka kasance masu kyau, babu shakka ba ma za ka samu dalilin la’anta ko zagin shugabannin da ke samanka ba, domin kuwa su ma za su kasance na kwarai,

Ya kai dan kasuwa! Kada in sake jin ka bude Burmammen bakinka kana sukar gwamnati. Kafin ka yi haka, ka fara duba kanka, shin yaya kake gudanar da kasuwancinka? Ba ka cin riba’u? Ba ka yin algusu? Ba ka yin amaja? Kana biyan haraji? Idan kana gudanar da kasuwancinka yadda ya dace, na tabbata ba za ka samu zarafin zagin Shugaban Kasa ko Gwamna da sauransu ba, domin kuwa kasuwancinka zai yi haiba kuma za ka samu albarka!

Ya kai talaka! Saboda me za ka Bata lokacinka wajen aibata shugabaninka, alhali ba ka kalli yadda ka banzatar da kanka ba? Kafin ka zagi attajiri don bai ba ka abin hannunsa ba, ka waiga baya ka kalli kanka, shin kana tashi kana neman na kanka? Ko kuwa ka bari zuciyarka ta mutu? Kana yin abin da ya dace da rayuwarka ko kuwa kai ne kullum a gindin inuwa ko gindin zauren mutane kana tumasanci da roko? Lallai kamata ya yi ka tashi ka nema a wurin Allah, ka tashi ka nemi aiki ko sana’a, tabbas za ka samu. Idan ka shgaltu da aikinka ko sana’arka, babu shakka ba za ka samu zarafin hangen abin hannun wani attajiri ba, balle nukura ko hassada ta kashe maka ruhi. Kuma ba za ka samu zarafin zagi ko la’antar shugabanni ba.

Ya ke ’yar uwa! Saboda me za ki Bata lokacinki wajen bi-ta-zaizai? Saboda me za ki zama mai Burmammen bakin zagi da la’antar shugabanni? Kafin ki yi haka, ki kalli kanki, shin yaya kike tafiyar da rayuwarki? Kina daraja mijinki? Kina yi masa biyayya? Kina da aiki ko sana’a? Idan ba ki da ko dayan abin da na lissafa, to ki shafa wa kanki lafiya, kada ki zagi shugaba, ki dora masa laifin da ba nasa ba, domin kuwa shugabanci kamar madubi ne, yadda kake, haka shugabanka yake!

Idan kana yi aikin kwarai, babu shakka shugaban kwarai zai yi maka jagoranci. Idan kana akasin haka, to abin da dai kake ciki, shi ne abin da za ka samu daga shugabanka!

Kafin mu yi kuka da wani, mu fara yin kuka da kanmu, domin abin da muke shukawa, shi ne muke girbewa! Idan muna shuka ayyukan kwarai, babu shakka sakamakon kwarai za mu rika gamuwa da su kuma mu girbe su. Idan muna aikata munanan ayyuka, ba za mu taBa ganin alheri ba, kuma babu yadda za a yi mu samu shugabanni masu amana da tausayi da jinkai. Ashe ke nan kamar ta masu salon magana ne da suke cewa, abin da ka shuka, shi za ka girba, idan hairan,  hairan, idan sharran, sharran.

Lallai kam zamanin da za mu zauna dirshan muna neman abu ya zo mana a Bagas ya wuce. Lokaci ne da ya kamata mu jajirce, mu tashi tsaye, mu yi aiki wurjanjan. Lokaci ne da za mu kasance masu kishin kanmu, masu kishin al’ummarmu, masu kishin kasarmu. Idan mun kasance haka da gaske kuma muka rayu a bisa kudirorin alheri da gaske, to babu shakka za mu samu jagorori irinmu, masu gaskiya da amana. Za mu kasance tsakaninmu da shugabanninmu sai salaman-salaman. Idan haka ta kasance kuwa, babu abin da za mu samu sai alheri, sai arziki, sai zaman aminci da lafiya da mutunta juna.