Mafarauta sun ceto Hakimi daga hannun ‘yan bindiga a Taraba

Mafarautan sun yi artabu tare da ceto hakimin da aka sace.

Mafarauta sun ceto Hakimi daga hannun ‘yan bindiga a Taraba

Mafarauta sun ceto Hakimin garin Lau Galdima Danladi Tau, da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba daga hannun ‘yan bindiga.

Aminiya ta ruwaito cewa yadda wasu mahara suka kai farmaki fadar hakimin da tsakar daren ranar Asabar, inda suka yi awon gaba da shi.

Sai dai bayan sace basaraken, mafarauta a garin sun taru, inda suka bi sahun ‘yan bindigar har suka yi artabu.

Mafarautan sun fatattaki maharan, inda suka yi nasarar ceto basaraken da ransa bayan ya samu rauni.

Maharan sun sake kai hari garin jim kadan bayan ceto basaraken, amma mafarautar garin suka dakile harin bayan arangama da suka yi da juna.

Maharan sun sake yunkurin kai hari a garin amma mafarauta suka fatattake su, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna kauyen.

“Muna kwana da ido daya a bude saboda fargabar yiwuwar kai hare-hare duk da cewa mafarauta ba sa barci suna gadin sa’o’i 24 a duk kofofin shigowa kauyen nan,” in ji wani mazaunin garin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna