Mafarauta sun harbe kyarkecin da ke cinye shanu da awaki a Rasha

A cikin makon nan ne wasu hotuna suka dauki hankalin  mabiya shafukan sada zumunta na zamani, yayin da wadansu mafarauta suke kokarin daga wani babban kyarkeci da suka harba. Wannan kyarkeci an ruwaito cewa, mafarautan sun harbe shi ne a kauyen Aleksandrobka da ke Gundumar Blagobeshchensk a Jamhuriyyar Bashkortostan, a wani waje da aka kebe don […]

Mafarauta sun harbe kyarkecin da ke cinye shanu da awaki a Rasha

A cikin makon nan ne wasu hotuna suka dauki hankalin  mabiya shafukan sada zumunta na zamani, yayin da wadansu mafarauta suke kokarin daga wani babban kyarkeci da suka harba.

Wannan kyarkeci an ruwaito cewa, mafarautan sun harbe shi ne a kauyen Aleksandrobka da ke Gundumar Blagobeshchensk a Jamhuriyyar Bashkortostan, a wani waje da aka kebe don adana namun daji, inda aka ajiye kyarkecin bayan wani lokacin sai daya daga cikin kyarkecin ya fara addabar jama’ar yankin. Wadansu mazauna yankin sun ce ba su ga wannan kyarkecin ba sama da shekara 40, bayan sauyin yanayin sanyi da aka samu sai ya fara shigowa cikin gidajen jama’a.

Karnuka da dama ne aka ce kyarkecin ya raunata a cikin makonnin da suka gabata, sannan kimanin shanu 20 da tumaki da awaki da dama ne kyarkecin ya cinye. Sakamakon barnar da kyarkecin ke yi wa jama’a wasu karnukan da ke yin gadi, sun dawo ba su iya yi wa kyarkecin haushi don ankarar da jama’a ko kuma su tunkari kyarkecin

“Karnukan cikin unguwa sun komo ba su yin haushi, sai dai idan sun hango kyarkecin su boye. Ban san dalili ba? Ni ba mafarauci ba ne, ban san dalili ba. Suna fargaba,” kamar yadda wani mazaunin yankin Aleksandrobka mai suna Mikhail Dementob, ya sanar.

Jama’ar Lardin Blagobeshchensk sun kasance cikin damuwa, lokacin mafarautan suka harbe kyarkecin ya mutu, yayin suka ga an wallafa hotunan da aka dauko kyarkecin, hakan ya sa mabiya shafukan sadarwa na zamani a kasar Rasha suka yi ta muhawara.