Mafarauta sun tsinci gawar ’yan bindiga a dajin Kaduna

An gano gawarwakin a safiyar ranar Asabar

Mafarauta sun tsinci gawar ’yan bindiga a dajin Kaduna

Kimanin mako guda bayan da aka gano gawarwakin mutane uku da ake zargin ’yan bindiga ne da suka fara rubewa a dajin Nasarawa-Azzara da ke karamar hukumar Kachia bayan da sojoji suka kai samame a maboyar ’yan bindiga, an sake gano wasu gawarwaki biyu a dajin Kuchimi da ke makwabtaka da karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Da yake tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin a ranar Lahadi, wani mazaunin garin, Danjuma Saleh, ya ce mafarauta ne suka gano gawarwakin a safiyar ranar Asabar.

Saleh ya ce, “Mafarauta da suka gano gawar sun zo suka kai rahoto ga basaraken kauyen.

“Da jin haka wasu mutanen kauyen ne suka tattaru zuwa dajin, suka ga gawarwakin da tuni sun rube.”

Zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ballantana ya tabbatar da faruwar lamarin.