Mafarki: Ma-farin-aiki

Kusan kullum sai Haurobiyawa sun yin a-kasa, don kada su kasa, a kasa, a kwashi kasha, amma abin tambaya a nan shi ne, wane irin mafarki suke yi? Sanin kowane mai kyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya cewa, na sha yin batutuwa a game karatun jakin dawa da na gida, don ta […]

Mafarki: Ma-farin-aiki

Kusan kullum sai Haurobiyawa sun yin a-kasa, don kada su kasa, a kasa, a kwashi kasha, amma abin tambaya a nan shi ne, wane irin mafarki suke yi? Sanin kowane mai kyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya cewa, na sha yin batutuwa a game karatun jakin dawa da na gida, don ta haka ne ake iya fasko abubuwan da suka damfaru a cikin kwanyar gama-garin al’umma da shagabanninsu.
Gama-garin Haurobiyawa kullum suna karanta wasikar jakin dawa da na gida kan yadda za su shirya aljannar duniya, ba tare da sun yi gumi ba; shu kuwa shagabnnin Haurobiyawa kullum sun himmatu ne, wajen tsuwurwurta dabarun kwashi-kwaraf, ta yadda za su ci gaba da tsayawa a mukamin ‘Alu-ja,’ su kuma tunkuda talakawan zuwa mukamin ‘Mi’ara koma-baya.’ A batu a ingarman karfen arafa, ba don kada ku jefa mini azargagiyar zargi ba, ai yau da sai na zayyano alamomin na zayyanar kolon Malam. Ban cika son ambaton sunayen manyan kwandalar Haurobiya ba, amma a wani yanayin al’amarin yakan zamato sai an doka misali, kowa zai iya fasko watangaririyar da miyagu suka jefa mu a ciki. Mu kuwa gama-gari lalaci ya kwantar da mu mun ki yin azama, ta yadda koda a mafarki ne mu wassafa yadda za mu wancakalar da tsarin tsirfar kassara al’umma; mu tsiro da tsirin tsire tsarin tsandaurain tsugudidin masu mulkin mulaka’u.
To kada dai in cika ku da surutu rututu kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ko kuwa in yi ta afa batutuwa kamar AP da AFP. Al’amuran ci gaban al’umma sun kankama a daukacin sassan duniya, mu kuwa mun rasa makama. Na yi muku faskaren ma’anoni, amma har yanzu ban ga wanda ya fasko jirgin Gudun-lokon da ake yi da Haurobiyawa ba. In-gwangwaje-in-wala, ta baje-kolin Hauro a hada-hadar camamar Hukuma ta shekara dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, inda aka haifar da wawakeken gibi tsakanin Arewatawa da Kudawan Haurobiya, amma ban ga wanda ya daga mata kara ba. Masanin Sisi-da-sisi ya yi ikrarin samartakar kusu da aka yi wa damin Hauro tiren-taliya madambaci a Kamfanin man tunkuza na kasar Haurobiya, babu wanda ya yunkuro, don kwato wa Haurobiyawa hakkinsu.
Ni dai na yi mafarki, a n yi min bushara, na zamo wani gwarzo a cikin harkokin tijjara. Kuma zan yi muku irin wannan albishiri ne, idan kun karkata akalar karatun wasikun jakunanku zuwa mafuskantar da ta dace.
Alal misali, duk da dai ba na wasa da Man-kaza na bayan kango, ai kun ga wancan dan dugwi-dugwi din mai makon ya yi ta ’yan leke-leke a kan Katanga, kamata ya yi a ya fara sana’ar na-duke, don wadata Haurobiya da kayan dundume kururu, amma kun ga kullum sai biye wa ’yan sharholiya yake ta yi. Bari dai in daina kada GizBaba ya kai karata, ya ce wai ina hantararsa. Ko kadan ba haka nike nufi ba. Ni abin da kawai nike tsoratar masa kada ya rika sha’awar dabi’un su Akuyar-maman-daudu da Baudadden Joji da Banga-Banga Tukururu da daukacin jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wadanda suka dade suna yunkurin jirkita kasar nan.
’Yan makarantarmu ta Dodorido, ya kamata ku fasko cewa Mafarki na nufin ma-farin-aiki, ga wanda ya yi mai kyau, a lokacin da mutum ya lume a cikin na-kasa; wanda kuwa ya ga mummuna, ko kura ta biyo, yana ta gudun ceton rai, to ma-farin-aika-aika yake yi. Hujja kuwa, ita ce, na ji wasu kalamai na Turawan Ingilishi na cewa, ‘Madaukakan al’umma, su ne masu mafarki,’ don haka nike ganin ban tafka ta’asa a kwanon tasa ba, matukar na furta cewa, “Makaskantan al’umma su ne masu ma-farin-aika-aika.’ Kun ga ke nan babu tantama, duk wanta yake mafarkin watsattsake da buda wagagen littattafai zai samu kansa a cikin makaranta; wanda kuwa yake fantamawa a cikin kango, to tabbas zai samu kansa a cikin dandalin GizBaba. Shi kuwa Baba irin ’yan gayun nan, ‘idan Baba ya kai makura a harkar babancewa, sai kawai mu kira shi babe na mijin fara.Haurobiyawa mu rika mafarki mai kyau. Mu daina mafarkin Damo-da-kura-da-diyya.
Duk wanda ya ga Santalla kwaiduwa a mafarkinsa, sai ya roki Mai-duka kada Loma-a-murde ya murde shi. Wanda kuwa ya ci karo da Samun-Bom-Da-Sauki, to akwai yiwuwar ya shiga dar-dar irin na zaman Haurobiya; ko kuma a kai masa hari irin wanda aka kai wa Malam Na-dandume. Idan kuwa ka yi sa’ar ganin Dogon Daurama, to akwai yiwuwar ka sha mai kararrawa, ka yi ta fafutikar Burin-huriyyar al’ummar Haurobiya.
Zan so a ce masu wasan Samson-siyasa-siya da kwakwalenmu, kwanyarsu ta damfaru da mafarkin shugaban masu saurautar Sara-da-daukar-dawainiya, wato Ahmadu Jikan Nana; da na Tafawa balewa abin faharin al’umma. Don ta haka ne kawai za mu hau mukamin ‘Alu-ja’ babu ja-in-ja, akasin haka kuwa shi ne, ‘Mi’ara koma-baya. Sai mu yi zungur kada mu yi zugum!