Mafarkin budurwa

Wata budurwa ce tana barci sai ta yi mafarkin an yi mata aure kuma ga shi har ta samu ciki, ta dawo gida domin haihuwa. Ta ci gaba da mafarkin cewa har ma an kai ta asibiti. Kan haka sai ta ji malamar asibiti tana cewa: “Yunkura sosai, yi nishi sosai.” Ita kuma ta yi, […]

Mafarkin budurwa
Mafarkin budurwa

Wata budurwa ce tana barci sai ta yi mafarkin an yi mata aure kuma ga shi har ta samu ciki, ta dawo gida domin haihuwa. Ta ci gaba da mafarkin cewa har ma an kai ta asibiti. Kan haka sai ta ji malamar asibiti tana cewa: “Yunkura sosai, yi nishi sosai.” Ita kuma ta yi, sai ta ji ta haifi yaro daya. Ta ji an ce ta kara yunkurawa, ta yunkura, ta haifi yaro na biyu. Ma’aikaciyar ta kara ce mata: “Akwai sauran yaro, yunkura.” Tana kokarin yunkurawa ke nan sai ta ji kawarta tana tayar da ita, tana cewa: “Ke Hadiza, tashi, kin yi kashi; duk kin bata shimfidar!”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi 08098157899