Mafarkin Gizago: Yadda na gana da wasu fitattun mutane game da shugabancin Najeriya
Tuna baya shi ne roko, inji Hausawa. Wannan rubutu mai take a sama, na yi shi ne a shekarar 2011, gab da lokacin da za a gudanar da zaben Shugaban kasa, wanda daga bisani “aka ce” Goodluck Jonathan ne ya yi nasara. Akwai abubuwan tarihi masu ban sha’awa da suka bayyana kansu a zaben da […]
Tuna baya shi ne roko, inji Hausawa. Wannan rubutu mai take a sama, na yi shi ne a shekarar 2011, gab da lokacin da za a gudanar da zaben Shugaban kasa, wanda daga bisani “aka ce” Goodluck Jonathan ne ya yi nasara. Akwai abubuwan tarihi masu ban sha’awa da suka bayyana kansu a zaben da aka gudanar a bana, idan aka kwatanta da wancan zabe na 2011. Dalili ke nan ma ya sanya na bijiro da wannan rubutu a yanzu. A karanta a tsanake, domin tantance darussan da muke son nusarwa:
Tun daga safiyar Litinin da ta gabata na fara gane cewa lallai wannan rana akwai wasu al’amura da ke bayyana kansu a matsayin baki a gare ni. Kafin wayewar safiya, na dade da sanin cewa an dage ranakun zaben da aka kuduri gudanarwa a ranar, don haka na sakankance zan fita wurin aiki, kamar yadda na saba a kowace rana irinta.
Da na isa wurin aikin, na samu kaina cikin kasala, musamman saboda matsanancin zafin rana da na bari ya yi ta dukana. Don haka, koda na koma gida da maraice, bayan na kammala sallolina na Magriba da isha’i, kuma bayan na yi jibi, babu abin da ya rage mini sai barci. Kuma abin da na yi ke nan, tun ma kafin in kammala kallon labarun duniya na karfe tara a talabijin.
Ina tsakar sharar barci ne, sai na ga Dodorido ya tunkaro ni, hankalinsa a tashe, ko sallama bai yi mini ba. Ni kuwa na tsaya ina kallon ikon Allah. Koda na gan shi a cikin wannan siffa, na yi zaton ko dai an bugo masa waya ne, aka sanar da shi cewa an fasa aurensa da Dodanniya. Domin kuwa na tabbata, a wannan lokacin, babu abin da ke cikin ran Dodo idan ba maganar aurensa da Dodanniya ba. Ya shaku da kaunarta, don haka ya kosa a kammala bikinsa da ita. Na gane haka ne a sanadiyyar yadda yake son ya ji batunta. Da wannan na rika yi masa wayo. Da zarar na ga alamar yana da Nairori, sai in ce masa “A gaishe da Dodo mijin Dodanniya!” Sai ka ga ya fara tsalle, yana zagaye-zagaye, daga wannan tebur zuwa wancan. Idan na kara ambata wannan kirari, sai ka ga ya zura hannu ya dauko ganyen shayi ko biskit ya mika mini. Idan ma aljihunsa da kauri, sai ka ga ya miko mini Dalar Amurka ko takardar kudin Yen, ta mutanen kasar Sin. Domin ya taba gaya mini cewa shi fa Dodo ne uban dodanni, ya fi karfin rike Nairar Najeriya, daga Dala sai Fam sai kuwa Yen da Yuro. Ni kuwa na ce ba dole ba, Dodo ai ba mutum ba ne, don haka aljanunsa za su iya tafiya su sato masa irin wadannan kudade. (Ku yi hakuri, na kauce daga labarin da nake ba ku).
Da Dodo ya iske ni, bai yi mini sallama ba, sai ya ce da ni: “Gizago, Giz-Baba, don Allah taso ka raka ni, wani mutum ne ya neme mu, wai zai gana da mu.”
Na ce masa, amma kai wane irin kidahumi ne? Wa ya gaya maka na damu da wani mutum, da za ka shigo mini gida babu sallama, kuma a wannan talatainin dare?
“Af to, na mance. Assalamu alaikum! Taso mu tafi don Allah. Mutumin yana waje yana jiran mu.” Inji Dodo, wai yana yi mini biyan bashin sallamar da na yi masa korafi a kanta. Na amsa masa sallamar, sannan kuma na gaya masa cewa ni ya kyale ni, domin ba ni da lokacin ganawa da wani mutum, komai girmansa, komai mukaminsa.
“Haba Giz-baba, don Allah kada ka yi mini haka, ka taso mu tafi, mutumin nan fa ba karami ba ne, yana da kima a idon al’ummar Najeriya.”
Dodorido dai ya matsa mini. Ni kuwa na ja wata doguwar hamma, na sanya tafin hannuna na dama, na rufe baki. Daga nan na motsa, na tashi daga kan shimfidar da nake kwance. Na sanya hannu na murje idanuna, sannan na mike tsaye, na dauko wata farar jallabiya na sanya. Na ce masa mu tafi.
Bayan mun isa kofar gida, sai na iske wani mutum fari kuma gajere, dan kimanin shekaru hamsin; yana jingine da wata mota kirar Honda-Jif. Fuskarsa rufe take da wani farin tabarau, wanda ke nuna kwayoyin idanunsa garai. Na yi masa sallama, ya amsa. Shi kuwa Dodo ya gabatar da ni zuwa gare shi.
“Alhaji, wannan shi ne Malam Gizago, ga shi nan na fito maka da shi.”
Na kalli fuskar mutumin a karo na biyu, na ga yadda ya washe baki, bayan Dodo ya gabatar da ni gare shi. Ya sake miko mini hannu don mu gaisa. Bayan na amshi hannun ne sai ya ce: “Sunana Nasiru El-rufa’i, na san kila ka taba jin sunan, koma ka taba ganina.”
Yana fadin haka sai na kara kallon shi sosai, domin kuwa na tuna da lokacin da yake rike da mukamin Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya. Daga nan na fara tunanin to me ya hada shi da Dodo da kuma har zai kawo shi gidana? Kamar ya san abin da nake riyawa a zuciyata, sai ya katse mini tunani, inda ya ce:
“Kada ka yi mamakin gani na a gidanka, domin kuwa ina dauke ne da wani muhimmin sako. Na dade ina bibiyar ayyukanku, kai da Dodorido a cikin jaridar Aminiya. Binciken kungiyarmu ya nuna mini cewa kuna da muhimmiyar rawar da za ku iya takawa don ci gaban kasar nan. Mun ankara da cewa ku cikakkun ’yan kishin kasa ne. A takaice, ni da sauran membobin kungiyarmu, wacce muka kafa da nufin nema wa kasarmu mafita, shi ya sanya muka gayyace ku, domin mu je mu zauna, mu yi nazarin mutumin da za mu zaba a wannan zabe da za a gudanar a kasar nan.” Ya dan sarara da bayaninsa, ya ci gaba da murmushi. Daga nan ya ci gaba da magana. “Muna da hakkin ceto kasarmu daga balbalcewa, don haka, da ni da ku da sauran matasa ’yan kishin kasa, za mu zauna mu yanke hukuncin wanda za mu zaba, daga cikin mutanen nan guda hudu da ke takarar shugabancin Najeriya. Ina maganar Mai Malfa da Sukari Ba Ka Yi Farin Banza Ba da Limamin Sahu da kuma danfulani.”
Za mu kammala makon gobe in Allah Ya so