Mafarkin Gizago: Yadda na gana da wasu fitattun mutane game da shugabancin Najeriya (2)
Tuna baya shi ne roko, inji Hausawa. Wannan rubutu mai take a sama, na yi shi ne a shekarar 2011, gab da lokacin da za a gudanar da zaben Shugaban kasa, wanda daga bisani “aka ce” Goodluck Jonathan ne ya yi nasara. Akwai abubuwan tarihi masu ban sha’awa da suka bayyana kansu a zaben da […]
Tuna baya shi ne roko, inji Hausawa. Wannan rubutu mai take a sama, na yi shi ne a shekarar 2011, gab da lokacin da za a gudanar da zaben Shugaban kasa, wanda daga bisani “aka ce” Goodluck Jonathan ne ya yi nasara. Akwai abubuwan tarihi masu ban sha’awa da suka bayyana kansu a zaben da aka gudanar a bana, idan aka kwatanta da wancan zabe na 2011. Dalili ke nan ma ya sanya na bijiro da wannan rubutu a yanzu. A karanta a tsanake, domin tantance darussan da muke son nusarwa:
Bayan mun shiga wannan mota da tsohon Minista, Malam Nasir El-rufa’i ya zo da ita, kyakkayawar tafiyar minti goma sha biyar ta aje mu a bakin wani gida kayatacce, wanda ban san mamallakinsa ba. Muka shiga harabar gidan, inda kuma muka doshi wani zauren taro, wanda aka kayatar da shi da ingantattar shimfida.
Muna shiga muka iske hamshakan mutane, wadanda suka shahara a Najeriya, sai dai yawancinsu daga Arewacin Najeriya suke. Kadan daga cikinsu, akwai Alhaji Magaji dambatta da Alhaji Lawal Kaita da Alhaji Adamu Chiroma da Janar Ibrahim Babangida da Alhaji Atiku Abubakar da Janar Abdussalam Abubakar da Kanar dangiwa Umar da Malam Adamu Adamu da Dokta Aliyu Tilde da Muhammad Haruna da sauransu. Tun ina kidayawa ma har na fara gajiya.
Da na kalli Dodo, sai na ga ya razana, musamman saboda ganin kwarjinin muhimman mutanen da ke cikin zauren taron nan. Ni kuwa da na ga haka, sai na ce a raina, kada fa mutumin nan ya ba mu kunya, bari in yi masa kirari, kila ya dawo cikin hayyacinsa. Na ce: “Kai Dodo mijin Dodanniya, ba da kanka a sare, ka je gida ka ce ya fadi!” Nan take ya yi zumbur, ya jajirce, ya wartsake. Da ma na gaya muku, duk abin da ake ciki, idan ka ambata sunan Dodanniya, Dodo zai fuskance ka. Bayan an nuna mana kujeru mun zauna a tsakiyar hamshakan mutanen, sai aka bude taro da addu’a, sannan mai gabatarwa ya gabatar. Ya nuna mana cewa, an shirya wannan taro ne da zimmar zaben mutum guda tsakanin Mai Malfa da Sukari Ba Ka Yi Farin Banza Ba da Limamin Sahu da kuma danfulani, wanda za a tasa gaba daga Arewa, domin ya kasance Shugaban kasa a wannan karon.
An ware masana guda goma, ciki kuwa har da ni Gizago da Dodorido. Aka rika kiranmu daya bayan daya, muna antayar da dalilanmu na zabin wanda muka ga ya dace. Dodorido, shi ne mutum na tara da ya bayyana zabinsa, inda daga bisani aka kira sunana, aka ce in yi bayanina.
Koda aka kira sunana, sai na mike tsaye, zauren ya kaure da sowa da “tafi, raf, raf, raf!” Shi kuwa Dodo sai ya fara yi mini kirari, yana cewa: “Malam Gizago ba ka da sabo, Giz-Baba mai Nigawa, namijin majigin Haurobiya. Malam Abokin Indiyawa gami da Larabawa…!”
Bayan an mika mini makirfo, sai na yi hamdala ga Sarki Allah, na yi gabatarwa, sannan na fara antayar da bayanina kamar Audu Kwamandan Gwari. Na ce: “Kafin in fitar muku da zabina, bari in fara yin jirwaye mai kamar wanka, zan bi ’yan takarar nan daya bayan daya, in fito da dacewa ko rashin dacewarsu ga shugabancin Najeriya. Daga karshe, sai ku ba kowa maki daidai da abin da na zayyana game da su.” Na gyara murya, na ci gaba da magana: “Bari mu fara bayani game da Mai Malfa, wanda a halin yanzu shi ne ke rike da mulkin kasar nan. Kuna kiran shi da sunan Mai Nasara, ni kuwa na ga ya fi dacewa da a kira shi da Tauraruwa Mai Wutsiya, Ganinki Ba Alheri Ba. Dalili kuwa shi ne, bai taba tsayuwa da kafafunsa ba, sai dai ya jingina da wani, kuma duk wanda ya jingina da shi, sai wata annoba ta saukar masa. Kamar yadda wata majiya ta sanar da ni, tun yana yaro a makaranta, ya taba yin Mataimakin Monita, Monitan ya mutu, shi kuma ya dare mukaminsa. Ya taba yin Mataimakin Shugaban dalibai, wanda shi ma ya mutu, aka mika masa mukaminsa. Ya yi Mataimakin Gwamna, annoba ta fada wa Gwamnan, aka sauke shi, aka mika masa mukaminsa. Ya yi Mataimakin Shugaban kasa, wanda shi ma ya mutu, aka mika masa mukaminsa. Yana hawa ya fara lalata dukiyar kasar nan. Ya haddasa kabilanci da bambancin addini. Ya dauki rijiyoyin mai guda tara ya mika ga ’yan yankinsa. Ya dakatar da yashe Kogin Kwara, wanda aikin zai amfani al’ummar Arewa. Ya dakatar da kwangilar shimfida hanyar jirgin kasa na zamani, daga Kaduna zuwa Abuja. Sannan kuma ya yi ta barnata dukiyar kasar nan ta yadda ya ga dama. Akwai alkawarin da ya dauka cewa, muddin ya samu darewa mulki a wannan karon, zai wulakanta sarakunan Arewa, zai wulakanta duk wani mai daraja daga yankin nan, sannan zai mayar da Najeriya tamkar yadda Kamaru take a yau. Ga tambaya, shin kun yarda a zabi irin wannan mutumin a matsayin shugaban Najeriya?” Nan da nan zauren ya kaure da cewa: “Ba mu so! Ba mu so!!” Sai mutum na biyu, wato Limamin Sahu: Ni a gani na, wannan mutum bai shirya shugabancin kasa kamar Najeriya ba, domin kuwa yana da rauni babba. Duk da cewa ya samu nasarar gudanar da mulkin hamshakiyar jiha na tsawon shekara takwas, ya kasance mai lalura, domin kuwa ya cika sanyi, musamman idan al’amari ya taso na tsawatarwa. Mutumin da ma’aikacinsa ko kwamishinansa zai tabka barna, maimkaon ya hukunta shi sai dai ya ce masa Allah Ya isa? Irin wannan mutum, ta yaya zai iya tunkarar azzaluman barayi a kasar nan, idan ya zama shugaban kasa?” Nan ma sai mutane suka kama sowa, suna cewa: “Ba mu so, Ba mu so!”
Na dan dakata da magana, sannan na ci gaba da cewa: “Sai kuma danfulani. Shi wannan mutum yana da halaye nagari, yana da kwazo da kakkarfar zuciya da himma. Hakika zai iya fada da duk wani azzalumi komai girmansa da karfinsa a kasar nan. Illa guda yake da ita, akwai kuruciya tare da shi. Ina ganin da zai kara hakuri, ya bari ya sake yin kwas na mu’amala da jama’a, da zai fi dacewa. Nan gaba sai ya sake neman fitowa takara. Ko kuwa yaya kuka gani?” Mutane suka ce: “Haka ne, haka ne!”
“Idan ta bi daga-daga, na kurya ka sha kashi. Yanzu kuma, bari mu duba Sukari Ba Ka Yi Farin Banza Ba.” Nan take na ji zauren ya kaure da fadin: “Canji, Canji! Sai Baba, sai Baba!” Ni kuwa na kara gyara murya, na saki wani murmushi na gamsuwa da abin da ke gudana a zauren. Na ci gaba da jawabina.
“Mu fara duba halayen Sukari Ba Ka Yi Farin Banza Ba, domin mu gane yadda yake, domin kuwa masu hikimar magana sun ce, halin mutum jarinsa. Shi wannan bawan Allah, bayanai gamsassu sun tabbatar da cewa, tun yana yaro, mutum ne shi mai kamala da natsuwa. Bai iya karya ko yaudara ba. Idan ya ce gabas, gabas zai nufa ba yamma ba. Idan ya ce baki, ba zai nufi ja ko shudi ba. Mutum ne mai tsayar da magana, mai cika alkawari. Haka kuma abokansa sun tabbatar da cewa yana da tsantsani da kyamar duk wani abu na rashin gaskiya. Ba ya shan inuwa daya da mugu ko azzalumi. Haka kuma, mu duba ayyukan da ya gudanar a rayuwarsa. Ya taba yin Ministan Fetur, amma har ya gama ba a taba kama shi da almundahana ba. Ya taba yin Gwamna, amma har ya sauka ba a taba ce masa Allah wadai ba. Ya yi shugabancin kasar nan na dan takaitaccen lokaci, amma gaskiyarsa da kishin kasarsa sun bayyana a duk fadin duniya. Ya tabbatar da da’a a zukatan al’umma. Ya sanya harsashi mai inganci na gina kasar nan. Ya daura yaki da zalunci da azzalumai. Haka kuma, ya taba rike hukumar PTF, inda da rarar Naira biyu kacal ya kawo ci gaba a kasar nan. An samu ingantattun hanyoyi da asibitoci da magani da makarantu da sauransu. Ko kun san wani abu? Duk da haka, mutumin nan gida uku kacal ya mallaka a duniya. Bai tara dukiya a kasashen waje ba, bai mallaki kamfani ko daya ba a gida ko a waje. Bai mallaki rijiyar mai ba. Kuma har zuwa yau din nan, babu wanda zai ce ga inda ya taba yin wata rashin gaskiya ko algushu. Shin cikin mutanen nan hudu, wa ya fi dacewa ya shugabanci Najeriya a wannan lokaci?”
Nan da nan zauren ya kaure da sowa da kururuwar kiran sunan Sukari Ba Ka Yi Farin Banza Ba, suna cewa: “Sai Baba Sukari, Sai Mai Gaskiya!” Wannan kururuwa, ita ta tada ni firgigi daga barci. Nan na gane cewa ashe ma duk mafarki ne nake yi!