Mafi Ƙarancin Albashi: Muna kan buƙatarmu ta N250,000 — NLC
Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta zaɓi tsarin dimokuraɗiyya wajen warware buƙatun ’yan ƙwadagon.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce har yanzu tana nan kan bakarta dangane da buƙatar mafi ƙarancin albashi da ta miƙa wa Gwamnatin Tarayya.
Ƙungiyar Ƙwadagon ta ce kawo yanzu babu wani takamaiman adadi na sabon mafi ƙarancin albashi da ta amince da shi a tattaunawar da ke gudana tsakaninta da Gwamnatin Tarayya.
NLC ta faɗi hakan a matsayin martani ga iƙirarin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
- An kuɓutar da yaro daga hannun masu garkuwa da mutane a Yobe
- Atiku ya yi wa Tinubu jajen auna tsautsayi a Eagle Square
A jawabin da ya yi wa ’yan Nijeriya albarkacin bikin Ranar Dimokuraɗiyya a safiyar wannan Larabar, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi ƙarancin albashin da aka daɗe ana tafka muhawara tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyoyin ƙwadago.
Shugaban ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba zai aika da wani ƙudurin doka ga majalisar dokokin ƙasar domin ta amince da sabuwar yarjejeniyar mafi ƙarancin albashin ma’aikata a kasar.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta zaɓi tsarin dimokuraɗiyya wajen warware buƙatun da ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar.
Sai dai a wata sanarwa da muƙaddashin Shugaban Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Prince Adewale Adeyanju ya fitar, ya ce babu wata yarjejeniya da kwamitin ɓangarorin uku suka cimma kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata a lokacin da aka kammala tattaunawar a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni 2024.
Adeyanju ya ce, “Buƙatarmu har yanzu tana nan a kan Naira 250,000 kuma ba a ba mu wasu ƙwararan dalilai na sauya wannan matsayi ba wanda muke ganin babban rangwame ne da ma’aikatan Najeriya suka yi a lokacin tattaunawar ɓangarorin uku.”
Ya bayyana cewa tilas ne su ƙara matsin lamba kan buƙatar mafi ƙarancin albashin ga shugaba Tinubu da ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki suka sani.
NLC ta ce “da alama waɗanda suka yi wa Tinubu bayanin sakamakon da aka yi a tattaunawar da aka yi tsakanin ɓangarorin uku ba su faɗa masa haƙiƙanin halin da ake ciki ba.”