Mafi karancin albashi: Ba za mu karbi kasa da N350,000 ba —NAAT

Sun ce dole ne mafi karancin albashi ya zama wanda zai iya rike ma’aikaci da masu dogaru da shi, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa

Mafi karancin albashi: Ba za mu karbi kasa da N350,000 ba —NAAT

Zanen wani da ke kallon dan albashinsa da aka kirkira da fasahar zamani.

Ma’aikatan jami’a sun sanya Naira 350,000 a matsayin mafi karancin albashin da ma’aikata za su iya lallabawa da shi a kasar a halin yanzu.

Kungiyar Ma’aikatan Jami’a ta Najeriya (NAAT) ta sha alwashin cewa ba za su karbi kasa da N350,000 ba a matsayin mafi karancin albashi, lura da tsadar kayan masarufi, sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin kasar ta yi.

Shugaban kungiyar, Kwamred Ibeji Nwokoma, ya ce “jazaman ne mafi karancin albashi ya zama wanda zai iya rike ma’aikaci da masu dogaru da shi, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa.

“Wasu kasashen Afirka sun dauki kwararan matakai wajen tabbatar da cewa albashin ma’aikaci zai iya ba shi damar samun yin rayuwa cikin rufin asiri da wadata.

“Shi ya sa nake cewa N350,000 shi ne mafi karancin albashin da ya dace a Najeriya a wata,” in ji shi a a lokacin taron deliget din kungiyar na kasa karo na 5 a Jami’ar Abuja.

Game da bashin albashin da ma’aikatan jami’a ke bin gwamnati kuwa, Kwamred Nwokoma ya ce “wannan babban abin takaici ne saboda ya kara jefa mu cikin matsi tare da kashe mana kwarin gwiwar yin aiki.