Dambarwar Albashi: Wa’adin tattaunawan NLC da Gwamnati ya cika

Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu sun amince da N62,000 amma NLC ta dage cewa sai N250,000 za ta amince a matsayin mafi karancin albashi.

Dambarwar Albashi: Wa’adin tattaunawan NLC da Gwamnati ya cika

Litinin din nan ce ranar karshen tattaunawar kungiyar kwadago da gwamnatin Najeriya kan mafi karancin albashi.

A halin da ake ciki, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) na jiran jin matsayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dauka kan tayin Naira 250 da ta yi gwamnati a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Hakan ba zuwa ne bayan a ranar Juma’a kwamitin tattaunawa kan dambarwar mafi karancin albashin ya kammala tattaunawa da kamfanoni masu zaman kansu inda suka amince da Naira 62,000 a matsayin mafi karancin albashin.

A daya bangaren kuma NLC ta dage a kan N250,000, bukatar da ake ganin idan gwamnati ba ta biya mata ba za ta janye

A makon jiya ne NLC ta dakatar da yajin aikinta da mako guda bayan gwamnatin ta yi alkawarin kara mafi karancin albashin daga N60,000 wanda kungiyar ta ki amincewa da shi.

Sai dai kuma, kungiyar wadda ita ma ta sassauta daga N495,000 da take nema, ta ce ba za ta amince da karin da ba mai tsoka ba ne a kan N60,000 din daga gwamnati.