‘Mafi yawan hadurra kan faru sakamakon marisar direbobi’

Gwamna Babatunde Fashola Raji na Jihar Legas ya ce binciken da gwamnatin jihar ta gudanar a toshohin mota ya nuna direbobi 162 sun sha hodar ibilis da tabar wiwi. Haka nan an gano cewa direbobi 996 suna yin tuqi a buge, saboda kwankwadar barasa da shan wasu miyagun qwayoyi.Gwamna Fashola ya yi wannan furuci ne […]

‘Mafi yawan hadurra kan faru sakamakon marisar direbobi’
‘Mafi yawan hadurra kan faru sakamakon marisar direbobi’

Gwamna Babatunde Fashola Raji na Jihar Legas ya ce binciken da gwamnatin jihar ta gudanar a toshohin mota ya nuna direbobi 162 sun sha hodar ibilis da tabar wiwi. Haka nan an gano cewa direbobi 996 suna yin tuqi a buge, saboda kwankwadar barasa da shan wasu miyagun qwayoyi.
Gwamna Fashola ya yi wannan furuci ne yayin wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya da ma’aikatar lafiya da sufuri ta shirya tare da hadin gwiwar kamfanin sarrafa barasa na Guiness, wanda aka gudanar a tashar New Garrage da ke unguwar Bariga.
Ya ce, “Kimanin direbobi 162 da ke tashoshi biyu na jihar aka gano cewa sun sha hodar ibilis da tabar wiwi, sannan direbobi 996 da aka yi wa gwaji, an gano sun bugu da giya”.
Ya bayyana cewa gwajin da aka gudanar a kan direbobi 988 da ke tashar Oyingbo ya nuna cewa direbobi 59 sun sha hodar ibilis, sannan gwajin da aka gudanar a kan direbobi 1,025 da ke tashar unguwar Iyana-Ipaja ya nuna direbobi 103 sun sha hodar ibilis da tabar wiwi.
Ya qara da cewa gwajin da aka yi wa direbobi 884 da ke tashar Ojota ya nuna cewa direbobi 239 suna dauke da cutar hawan jini; sannan guda 86 suna dauke da cutar siga; guda 60 sun sha miyagun qwayoyi; sannan guda 287 sun sha giya.
Gwamna Fashola ya buqaci direbobin su guji shan duk wani abu da zai iya bugar da su domin, bincike ya nuna cewa mafi yawan hadurran da ake samu kan faru ne sakamakon shan abubuwan da ke bugar da direbobi.
Kwamishinan sufuri na jihar, Mista Kayode Opeifa ya buqaci direbobin su kori duk wasu masu sayar da barasa da muggan qwayoyi da ke tashoshinsu domin yin hakan zai taimaka musu wajen nisantar shaye-shaye.