Mafi yawan ’yan fim din Hausa jahilai ne kan harkar fim – Gidigo
Mikail Isah Bin Hassan, wanda aka fi sani da Gidigo jarumi ne, furodusa ne, kuma darakta ne. Shi ne shugaban kamfanin One Eleben Media Communications Ltd. A kwanakin baya ya yi tattaki har kasar Nijar, inda ya shafe kwana 70 yana daukar fim din Warisha. Aminiya ta tattauna da shi kan matsalolin da ya fuskanta […]

Mikail Isah Bin Hassan, wanda aka fi sani da Gidigo jarumi ne, furodusa ne, kuma darakta ne. Shi ne shugaban kamfanin One Eleben Media Communications Ltd. A kwanakin baya ya yi tattaki har kasar Nijar, inda ya shafe kwana 70 yana daukar fim din Warisha. Aminiya ta tattauna da shi kan matsalolin da ya fuskanta yayin aikin daukar fim din, nasarorin da ya cin ma wa da sauraran batutuwan da suka shafi masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. Ga yadda hirar ta kasance:
A kwanakin baya ka shafe watanni a Nijar wajen aikin daukar fim din Warisha, yaya aikin ya kasance?
Na samu gagarumar nasara, domin na samu damar daukar sassa 26 na fim din, inda hakan babbar nasara ce ga Kannywood, domin fim na farko ke nan a matsayin fina-finan jere (series) a masana’antar. Na dauki tsawon lokaci a kan aikin fim din, domin na yi wata 10 ina shirye-shiryen daukarsa, a yanzu kuma na dauki sassa 26 cikin 100.
Yawanci jigon labaran fina-finan Kannywood a kan soyayya ne, ko fim din Warisha ya zo da sabon salo ta bangaren labari?
Fim din Warisha labari ne a kan tabarbarewar al’amuran rayuwa ta bangaren mata. Labari ne a kan ’yan mata daga shekara 18 zuwa 25, inda suke fada wa aikata miyagun laifuka, wadansu su shiga karuwanci. A fim din an nuna abubuwan da suke jefa wadannan ’yan mata zuwa ga aikata miyagun ayyuka, har wadansu su fada karuwanci.
Wadanne matsaloli ka fuskanta yayin daukar fim din?
Kai ma ka sani duk lokacin da aka ce ka bar kasarka ka kuma tafi wata kasa don daukar fim dole ka fuskanci matsaloli, ba wai don al’ada ko addini sun bambanta ba, amma ka shafe fiye da kwana 70 kana daukar fim ka san dole za a fuskanci matsaloli. Ni na dauki nauyin samar da wurin kwana da abincin jarumai da sauran ma’aikatan da suke yi mini aiki tsawon wadannan kwanaki.
Nijar tana daya daga cikin kasashen da suke magana da Faransanci, yaya ka gabatar da aikinka cikin nasara, sannan an dauki wannan fim din da wane yare ne?
Mun dauki fim din da Hausa, amma za a yi masa fassara da Faransanci da Turanci da Swahili, domin na yi fim din ne don kasuwar fina-finai ta duniya.
A bangaren ’yan wasa, ko ka zabo manyan jaruman da duniyar Kannywood take ji da su ne?
Ban cika mayar da hankali kan shaharar jarumi ba, abin da na fi amanna da shi shi ne, karfin jigon labari, kashi 80 cikin 100 na jaruman da suka fito a fim din ’yan Nijar ne, inda sauran kashi 20 suke daga Najeriya, amma a bangaren sauran ma’aikata kuma kashi 98 cikin 100 daga Najeriya suka zo, kashi 2 ne kawai daga Nijar.
A bangaren kasafin kudi fa?
A gaskiya an kashe kudi wajen abinci da muhallin da ’yan wasa suke kwana da zirga-zirga da wuraren daukar fim da kayayyakin da aka yi amfani da su da kuma na’urorin da muka yi amfani da su, akalla na kashe Naira miliyan 23.
Ganin irin wannan kudi da aka kashe, a ina aka samu kudin? Kamfani ne ko gwamnati suka dauki nauyin shirya fim din?
Babu wani kamfani ko gwamnati, da kudina na dauki nauyin shirya fim din, kamfanina One Eleben Production ne ya yi dawainiyar komai da komai.
Yaushe kake burin fitar da wannan fim din?
Na shirya fim din ne don a rika nunawa a gidan talabijin, amma za a sake shi daga na kashi daya zuwa na biyar, kowane kashi zai kunshi sashi 20, za a nuna fim din a gidajen talabijin da ke Najeriya da kuma kasashen da suke magana da harshen Faransanci, sannan a kuma nuna shi a gidajen talabajin da ke sauran kasashen duniya.
Bayan fim din Warisha me kuma masu kallo za su tsumaya daga gare ka?
Ina da burin sake daukar wani fim, amma a yanzu ina jira in ga yadda masu kallo za su karbi sabon aikin da na zo musu da shi. Burina a ce wannan fim ne ya sake bude wa masu ruwa da tsaki a Kannywood ido don su rika shirya fina-finan da za su hada kafada da sauran fina-finai a duniya.
Yawancin masu shirya fim a Kannywood suna korafin satar fasaha ta hana su rawar gaban hantsi, yaya kake tunanin za ka kare da masu satar fasaha musamman da yake ka kashe kudi masu yawa wajen shirya fim dinka?
Idan ba ka manta ba, na sanar da kai ba wai burina in saki fim din a kasuwa ba, za a nuna fim din a gidajen talabijin ne, ka ga masu satar fasaha ba matsalata ba ce, a wurina ban yarda masu satar fasaha ba ne suka hana Kannywood sakat ba, akwai masu magana da harshen Hausa kimanin miliyan 170 a kasashen Yammacin Afirka, don haka ’yan kasuwarmu ne ba su da dabarun kasuwancin da dillancin fim a wadannan kasashe, sun tsaya ne kawai a kasuwannin Najeriya, don haka babu inda za a je.
Yaya kake ganin za a magance matsalar satar fasaha?
Ya zama dole daidaiku su daina kasuwancin fina-finai, mutum ya fahimci ba zai yiwu a ce shi ne zai yi fim, shi ne zai tallata shi, shi ne zai yi dillanci da kasuwancinsa ba, hakan ba zai taba yiwuwa ba, taura uku ko hudu ba za ta taunu a baki ba. Dole a hada kai, a samu kamfanoni masu karfi wadanda za su tallata fina-finai, su yi kasuwancinsu.
A bara kana daya daga cikin ’yan fim da suka ziyarci Amurka don yin bita a kan harkar fim. Yaya kake tsammanin wannan ziyara taka za ta amfani Kannywood?
kwarai, ina daya daga cikin ’yan fim da aka gayyata wannan bita, ni kadai ne daga Yammacin Afirika, mun ziyarci wurin shirya fim na Unibersal Studios da ke Kalifoniya a Amurka. Hakan ya kara bude mini ido a kan harkar shirya fim, na gane ban san komai ba a da, na koyi yadda ake amfani da kyamara wajen daukar fim mai inganci, na koyi yadda ake siddabaru yayin daukar fim, na kuma koyi dabarun daukar fim cikin sauki. Bayan na dawo gida na zauna da wadansu masu ba da umarni a Kannywood, na sanar da su abubuwan da na koya, inda a yanzu ga shi suna ci gaba da amfani da su a lokacin da suke daukar fim, ina alfahari da hakan.
A ra’ayinka, wacce hanya kake ganin za a bi don daukaka darajar Kannywood a idon duniya?
Hanya ta farko ita ce mu daina tunanin mun iya komai a harkar fim. Idan muka gane hakan, to mun hau hanyar daukaka Kannywood a idon duniya. Mu sa a ranmu ba mu san komai a bangaren daukar fim ba, daga nan mu fara tunanin hanyar da za mu bi don mu koyi sana’ar, zan iya cewa kashi 98 cikin 100 na masu harkar fim din Hausa ba su da ilimin yadda ake daukar fim mai inganci, don haka ya zama dole mu koma makaranta ciki kuwa har da ni.