Mafi yawan ‘yan majalisar Afirka ta Kudu ba sa tare da Jacob Zuma

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi kememe kan kiran da ake yi ya sauka daga mulki duk da cewa jam’iyyarsa ta ANC ta kaddamar da kudurin rashin goyon bayansa a Majalisar kasar. A shekaranjiya Laraba ne Zuma ya ce ba zai sauka daga mulki ba, inda a jiya Alhamis Jam’iyyar ANC ta […]

Mafi yawan ‘yan majalisar Afirka ta Kudu ba sa tare da Jacob Zuma

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi kememe kan kiran da ake yi ya sauka daga mulki duk da cewa jam’iyyarsa ta ANC ta kaddamar da kudurin rashin goyon bayansa a Majalisar kasar.

A shekaranjiya Laraba ne Zuma ya ce ba zai sauka daga mulki ba, inda a jiya Alhamis Jam’iyyar ANC ta fara shirin tsige shi daga mulki sai har zuwa lokacin hada wannan labarin, Aminiya ba ta samu labarin tsige shi.

Shi dai Shugaba Jacob Zuma ya dade cikin tsaka- mai-wuya a kasar, inda mafi yawan  ’ya’yan jam’iyyarsa ta ANC suka bukaci ya sauka cikin mutunci. 

Babban Ma’ajin Jam’iyyar ANC, Paul Mashatile ya ce suna so su kawo canji ne a kasar domin mutanen kasar sun nuna cewa canjin suke bukata shi ya sa suke so Zuma ya sauka. 

Sai dai kuma Shugaba Zuma a nasa bangaren ya ce shi fa ba zai sauka daga mulki ba domin bai yi laifin komai ba.

A wancan karon da aka kada kuri’ar yi kin amincewa da Shugaba Zuma a karo na 8 da majalisar ta yi a ranar 8 ga watan Agustan bara, daga cikin ’yan majalisa 384, 177 daga cikinsu sun nuna rashin amince da Zuma, yayin da 198 suka ci gaba da goyon bayansa, sannan 9 ba su yi zaben ba. Wannan ya nuna cewa ko a wancan lokacin, sama da rabin majalisar ba sa son Zuma ya ci gaba da mulki sai dai yawansu bai kai wadanda ake bukata ba kafin su iya tsige shi. 

A wannan makon an ruwaito cewa an ba Shugaban kwana biyu ya yi murabus daga mukaminsa.   Cyril Ramaphosa wanda shi ne sabon Shugaban Jam’iyyar ANC,  shi ne ke kan gaba wajen ganin a kawar da Shugaba Zuma daga mulki domin shi ne ake kyautata zaton ya maye gurbinsa. Amma kuma yadda Jacob Zuma ya ki sauka daga mulkin na iya raba jam’iyyar gida biyu, domin har yanzu ya kafe cewa ya kamata a bar shi ya ci gaba da mulki na wasu mako ko watanni masu zuwa.