Mafificiyar Shari’ar Ubangiji
Barkanmu da sake saduwa a cikin makon farko na watan Disamba. Kafin mu shiga bincike a kan muhimmancin Kirsimeti a wannan wata, bari mu karanta wannan shafi daga Littafin Zabura a kan mafificiyar shari’ar Ubangiji. “Masu farin ciki ne marasa laifi cikin zamansu, Wadanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji. Masu farin ciki ne wadanda […]
Barkanmu da sake saduwa a cikin makon farko na watan Disamba. Kafin mu shiga bincike a kan muhimmancin Kirsimeti a wannan wata, bari mu karanta wannan shafi daga Littafin Zabura a kan mafificiyar shari’ar Ubangiji.
“Masu farin ciki ne marasa laifi cikin zamansu, Wadanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji. Masu farin ciki ne wadanda suke bin umarninSa, Wadanda suke yi masa biyayya da zuciya daya. Hakika ba su yin laifi, Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji. Kai Ka ba mu dokokinKa, Ka kuwa fada mana mu kiyaye su da aminci. Na sa zuciya zan yi aminci, Game da kiyaye dokokinKa! Idan na kula da dukkan umarninka, To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba. Zan yabe Ka da tsattsarkar zuciya, A sa’ar da na fahimci ka’idojinKa masu adalci. Zan yi biyayya ga dokokinKa, Ko kusa kada Ka kashe ni!
Biyayya ga Shari’ar Ubangiji
Kaka saurayi zai kiyaye ransa da tsarki? Sai ta wurin biyayya ga umarninka. Da zuciya daya nake kokarin bauta maKa, Ka kiyaye ni daga rashin biyayya ga umarninka! Na rike maganarKa a zuciyata, Don kada in yi maKa zunubi. Ina yabonKa, Ya Ubangiji! Ka koya mini ka’idojinKa! Zan tada murya, In maimaita dukkan dokokin da Ka bayar. Ina murna da bin umarninKa, Fiye da samun dukiya mai yawa. Nakan yi nazarin umarninKa, Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka. Ina murna da dokokinKa, Ba zan manta da umarninKa ba.
Farin ciki da Dokar Ubangiji
Ka yi mini alheri, ni bawanKa, Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarKa. Ka bude idona domin in ga gaskiyar shari’arKa mai ban mamaki. Zamana a nan duniya na dan lokaci kadan ne. Kada Ka boye mini umarninKa! Zuciyata ta kosa saboda marmari, A kowane lokaci ina so in san hukuncinka. Kakan tsawata wa masu girman kai, La’anannu ne wadanda suka ki bin umarninKa. Ka kubutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu, Domin na kiyaye dokokinKa. Ko da sarakuna za su taru su shirya mini makarkashiya, Duka da haka, ni bawanKa, Zan yi nazarin ka’idojinKa. UmarninKa suna faranta mini rai, Su ne mashawartana.
Kudurin yin biyayya ga Dokar Ubangiji
Ina kwance cikin kura, an yi nasara da ni, Ka wartsakar da ni kamar yadda Ka alkawarta! Na furta dukkan abin da na aikata, Ka kuwa amsa mini, Ka koya mini ka’idojinKa! Ka koya mini yadda zan yi biyayya ga dokokinKa, In kuma yi nazarin koyarwarKa mai ban mamaki. Bacin rai ya ci karfina, Ka karfafa ni, kamar yadda Ka alkawarta. Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya, Ta wurin alherinKa, Ka koya mini dokarKa. Na yi niyya in yi biyayya, Na maida hankali ga ka’idojinKa. Na bi umarninKa, ya Ubangiji! Kada ka sa in kasa cimma burina! Ina dokin yin biyayya ga umarninKa, Gama za Ka kara mini fahimi.
Addu’ar neman fahimi
Ka koya mini ma’anar dokokinKa, ya Ubangiji! Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci. Ka fassara mini dokarKa, ni kuwa zan yi biyayya da ita, Zan kiyaye ta da zuciya daya. Ka bisshe ni a hanyar umarninKa, Domin a cikinsu nakan samu fari ciki Ka sa ni in so yin biyayya da ka’idojinKa, Fiye da samun dukiya. Ka kiyaye ni daga maida hankali ga abin da yake marar amfani, Ka yi mini alheri kamar yadda Ka alkawarta. Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanKa, Irin wanda Kakan yi wa wadanda suke tsoronKa. Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro, Ka’idojinKa suna da amfani kwarai! Ina so in yi biyayya ga umarninKa, Gama Kai mai adalci ne, Ka yi mini alheri!
Dogara ga Dokar Ubangiji
Ka nuna mini yawan kaunar da Kake yi mini, ya Ubangiji! Ka cece ni bisa ga alkawarinKa. Sa’an nan zan amsa wa wadanda suke cin mutuncina, Domin na dogara ga maganarKa. Ka ba ni iko in iyar da sakonKa na gaskiya a kowane lokaci, Gama sa zuciyata tana ga hukuncinKa. Kullum zan yi biyayya ga dokarKa har abadan abadin! Zan rayu da cikakken ’yanci, Gama na yi kokari in kiyaye ka’idojinKa. Zan furta umarninKa ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba. Ina murna in yi biyayya ga umarninKa, Saboda ina kaunarsu. Ina girmama umarninKa, ina kuwa kaunarsu, Zan yi ta tunani a kan koyarwarKa.
Amincewa da Shari’ar Ubangiji
Ka tuna da alkawarin da Ka yi mini, ni bawanKa, Ka karfafa zuciyata. Ko ina shan wahala, ana ta’azantar da ni, Saboda alkawarinKa yana rayar da ni. Masu girman kai suna raina ni, Amma ban rabu da dokarKa ba. Na tuna da koyarwar da Ka yi mini a da, Sukan kuwa ta’azantar da ni, ya Ubangiji! Haushi ya kama ni sosai, Sa’ar da na ga mugaye suna keta dokarKa. Ina zaune can nesa da gidana na ainihi, Sai na kago wakoki a kan umarninKa. Da dare nakan tuna da Kai, ya Ubangiji! Ina kuwa kiyaye dokarKa. Wannan shi ne farin cikina, In yi biyayya ga umarninKa.
Tunani a kan Shari’ar Ubangiji
Kai kadai nake so, ya Ubangiji! Na yi alkawari in yi biyayya ga dokokinKa. Ina rokonKa da zuciya daya, Ka yi mini jinkai kamar yadda Ka alkawarta! Na yi tunani a kan ayyukana, Na yi alkawari in bi ka’idojinKa. Ba tare da bata lokaci ba, Zan gaggauta in kiyaye umarninKa. Mugaye sun daure ni tam da igiyoyi, Amma ba zan manta da dokarKa ba. Da tsakar dare nakan farka, In yabe Ka saboda hukunce-hukuncenka masu adalci. Ina abuta da dukkan wadanda suke bauta maKa, Da dukkan wadanda suke kiyaye dokokinKa. Ya Ubangiji! Duniya ta cika da madawwamiyar kaunarKa, Ka koya mini umarninKa!
Amfanin Shari’ar Ubangiji
Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji! Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanKa. Ka ba ni hikima da ilimi domin ina dogara ga umarninKa. Kafin Ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya ga maganarka. Managarci ne Kai, Mai alheri ne kuma, Ka koya mini umarninKa! Masu girman kai sun fadi karairayi a kaina, Amma da zuciya daya nake biyayya ga ka’idojinKa. Wadannan mutane ba su da ganewa, Amma ni ina murna da dokarKa. Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarninKa. Dokar da Ka yi muhimmiya ce a gare ni, Fiye da duk dukiyar duniya.”
(Zabura 119)