Mafita daga zalunci da kunci (2)
Babu shakka rashin adalci ne sababin rugujewar daulolin da suka gabata. An fada cewa zaluncin sarki ko shugaba na shekara dari bai kai zaluncin da talakawa ke yi tsakaninsu na shekara daya ba. Sai dai kuma an fada cewa idan talakawa na zaluntar junansu, sai Allah Ya dora a kansu wani mugun sarki ko Shugaba […]
Babu shakka rashin adalci ne sababin rugujewar daulolin da suka gabata. An fada cewa zaluncin sarki ko shugaba na shekara dari bai kai zaluncin da talakawa ke yi tsakaninsu na shekara daya ba. Sai dai kuma an fada cewa idan talakawa na zaluntar junansu, sai Allah Ya dora a kansu wani mugun sarki ko Shugaba wanda zai hana su sakat. Don haka sai talakawa sun gyara tsakaninsu sannan za su samu adalin shugaba.
Haka kuma an fada a cikin tarihi cewa, wata rana an aika wa da Hajjaju bin Yusuf da wata takarda wadda aka rubuta a jikinta, kamar haka: ‘Ka ji tsoron Allah, ka daina zalunci a kan bayinSa.’ Yayin da ya karanta wannan takarda sai ya hau kan mumbari, domin akwai shi da iya huduba da jawabi. Ya ce, “Ya ku mutane! Ku sani Allah Ya dora ni mulki bisa kanku daidai da ayyukan da kuka kasance kuna aikatawa ne.”
Ya kara da cewa ‘Kuma ko da na mutu a yau din nan ba za ku kubuta daga zalunci ba, saboda mugun nufinku. Domin Allah zai halicci wani kamar ni da ma wadanda suka fi ni, su ci gaba da musguna muku. Idan ni ban kasance mai zalunci da girman kai da yawan sharri da tsananin fushi ba, to wanda zai zo bayana zai zama tamkar haka, ko ma fiye, saboda haka mawaki ma yana cewa:
“Babu mai iko face Allah Mai girma,
Babu azzalumi sai an dora wani kansa.
“Azzalumi na bayyana ne domin magani,
Na wani zalunci da ake yi a bayan kasa.”
Ya ci gaba da bayaninsa yana cewa, zalunci abin tsoro ne, adalci shi ne abin da kowa yake so, amma ba zai samu ba sai kowa ya gyara halinsa. Muna rokon Allah Ya ba mu dacewa da adalci.
Daga wadannan hikayoyi guda biyu da muka gani, abubuwa biyu suka fito fili karara, su za mu bi daya bayan daya mu ga ko za su nuna mana turbar halin da muke ciki a yau na rashin fita daga kuncin da muke samun kanmu.
Mu soma da batun tsohuwa da take cewa:
“Sai dai ka kara da lura, ka kuma kula, su ma jama’ar wannan zamani ba su zaman tamkar na baya ba. Yanzu ana wani irin zama ne a tsakanin jama’a mai cike da zargi da karya da rashin cikakkiyar magana. Yanzu zamani ya zamana kowa so yake ya azurta kansa da karya ga kuma kekasasshiyar zuciya da ta mamaye mafi yawan al’umma.
Ta ce ana biye wa son zuciya a halin yanzu, ana aiwatar da adawa da kiyayya. Duk sarki ko shugaba da ya zama haka, ko mutanensa suka kasance cikin wannan yanayi, to sai dai neman tsari a wajen Allah daga gare su.
Babu shakka rashin adalci ne sababin rugujewar daulolin da suka gabata. An fadi cewa zaluncin sarki ko shugaba na shekara dari bai kai zaluncin da talakawa ke yi tsakaninsu na shekara daya ba. Sai dai kuma an fada cewa idan talakawa na zaluntar junansu, sai Allah Ya dora a kansu wani mugun Sarki ko Shugaba wanda zai hana su sakat. Don haka sai talakawa sun gyara tsakaninsu sannan za su samu adalin shugaba.”
Shin wannan tsokaci bai kasance gaskiya ba a irin halin da muke ciki? Shin wane irin zalunci ne ba ma yi a tsakaninmu, a matsayin talakawa da kuma shugabanni? Shin me zai hana ke nan mu samu kanmu cikin irin wannan hali? Me zai hana ba za mu kasance cikin kunci da tashin hankali ba?
Mu dau karamin misali, a yau ba sai an kai batun da nisa ba, tsakanin mai awo da wanda ke aunawa a cikin kasuwa abin nan ne da za a iya cewa na kura, ga tsoro ga ban tsoro, ko kuma na ka-san-na-sani, amma a maimakon a rika cewa ka-san-na-bari sai abin ya zama, ba a bari, ba a kuma da niyyar bari.
A yau zamantakewa tsakanimu ta cuta da cutarwa ce, da niyyar cuta muke zuwa awo a kasuwa, shi kuma mai awon da niyyar cuta yake tashi da safe ya tafi kasuwa, ya kuma tabbatar ya aiwatar da wannan niyya. In kuma shi mai zuwa awon da ya zo da jabun kudi domin cuta ya yi nasara kan mai awon, sai abin ya kasance dillin ce ta harbi dillin.
Haka abin nan yake tsakanin mai sayar da man gyada ko manja da masu saye: algushu da manakisar ciniki. Haka abin yake ga mai faci ko gyaran mota ko keke ko babur ko direba ko kuma mai askin baba.
Idan ka sake lekawa tsakanin masu aikin hukuma, ba abin da za ka gani sai cin zali da dulmiyar da al’umma cikin tashin hankali da damuwa. Masinja ko sakatare a kowane mataki na hukuma a kasar nan ba kyalle ba ne wajen baba-kere da sama-da-fadi da cuta da cutarwa.
Haka shugabanni a kowane mataki, na karamar hukuma ne ko jiha ko tarayya, ba abin da suka mayar da hankali kai face sace arzikin kasa da talauta kansu da sauran al’umma.
Kansila makashi ne! Ciyaman mai zarar ciyawa ne! Gwamna ai gwami ke nan wajen rarraba kan jama’a da diba a boye. A can kuwa Gwamnatin Tarayya ai rijiya ce ta masu gugar asali.
Haka abin yake tsakanin sarki da hakimai, tsakanin amarya da ango da kwarin gida. Tsakanin liman da ladan da duk wani shugaba a coci ko wata sana’a a cikin kasa.
Saboda haka idan ka auna, ka duba sai ka ga cewa duk kanwar ai ja ce, wata sa’a jazur take. Ke nan jawabin Hajjaju da ke cewa ‘Kuma ko da na mutu a yau din nan ba za ku kubuta daga zalunci ba, saboda mugun nufinku. Domin Allah zai halicci wani kamar ni da ma wadanda suka fi ni, su ci gaba da musguna muku. Idan ni ban kasance mai zalunci da girman kai da yawan sharri da tsananin fushi ba, to wanda zai zo bayana zai zama tamkar haka, ko ma fiye.” Ta zo kan gaba! Idan yau dukkan azzaluman shugabannin da muke da su a ko’ina cikin kasar nan (na cikin gida ko addini ko gargajiya ko hukuma ko na sana’a) za su mutu ko su kau daga doron kasa ba wani sauki za a samu ba, domin Allah Ya riga Ya halicci wani azzalumin da ke jiran hayewa kan gadon mulkin domin ya ci gaba da tursasa wa al’umma a kowane irin fasali ko tsari. Kila ma in ba a yi hankali ba, wadanda za su hau su kasance sun fi wadanda suka wuce iya zalunci da tursasawa, domin al’umma na tafiya ne da irin shugabannin da ta samar wa kanta, ba wai daga wata kasa za a shigo da su ba!
Ke nan matsalar kasar nan ba ta shugabanni ba ce kadai, matsala ce ta kowa da kowa! Don haka sai talakawa sun gyara tsakaninsu sannan za su samu adalin shugaba.
Za mu ci gaba