Mafita ga rashin aikin gwamnati
Hakikanin gaskiya illimi wani sinadari ne wanda wasu kan kira da gishirin zaman duniya. Lallai ya zama dole ga iyaye su zage damtse wajen illimin yaransu. Duk wani nau’in illimi da muka sani a duniya, yana da amfani matuka idan har anyi shi yadda ta kamata. Na tsaya na yi tunani mai zurfi, kuma na […]
Hakikanin gaskiya illimi wani sinadari ne wanda wasu kan kira da gishirin zaman duniya. Lallai ya zama dole ga iyaye su zage damtse wajen illimin yaransu. Duk wani nau’in illimi da muka sani a duniya, yana da amfani matuka idan har anyi shi yadda ta kamata. Na tsaya na yi tunani mai zurfi, kuma na lura da cewa yawancin iyaye sun fi maida hankali wajen zava ma ‘ya’yansu abin da za su karanta bayan sun kammala Sakandari. Hakan abu ne mai kyau sosai, sai dai a wani vangaren dole ne mu tsaya mu duba cewa kowane dan Adam akwai baiwar da Allah Ya yi masa, wanda ke kevanta gareshi. Wannan baiwa za ta taimaka wajen karatun da za su yi a jami’a. Hakan kuma zai taimaka wajen ba su dama kawo wani sabon al’amari bisa wannan baiwar da suke da ita. Amman idan aka turasu karatun da ba su da sha’awa ko kuma ba su da iko ko baiwar yin sa, to lalli za a samu matsala gurin aiwatar da karatun.
Ya zama dole ga iyaye su maida hankali wajen fahimtar baiwar da ‘ya’yasu ke da ita wajen saka su a hanyan karatun gaba da sakandare. Iyaye ko masu kula da ‘ya’ya dole ne su yi tunani sosai wajen yanayin rayuwar da ‘ya’yansu za su shiga ko kasancewa bayan karatun da suka yi a jami’a. sanin kowane yanzun a kasar nan akwai matsala na aikin gwamnati. Dole ne ‘ya’yanmu tun suna da karancin shekaru ko makaranta a nuna musu wata hanya da za su iya rayuwa a kanta ba dole sai sun yi dogaro da aikin gwamnati ba. Idan muka duba vangaren jami’o’i, za mu ga cewa duk shekara ana yaye dalibai dubu daruruwa, kuma gwamnati ba ta da inda za ta saka su, duk suna zama ne ba aikin yi. Tambaya a nan ita ce, wane ne za a ba aikin, kuma wa za a hana? Dole ne mu mike tsaye wajen tunani a kan abin da ka iya faruwa da yaranmu a nan gaba. Idan kuna tunanin cewa yau ko yanzun akwai damar daukar aiki, ba kusan abin da zai faru ba anjima ko gobe. Don haka dole iyaye su nema masu mafita tun a yanzu. Kun ga idan Allah Ya sa an samu aikin gwamnati, abu ya yi kyau ke nan, idan kuma ba a samu ba to kun ga sai a yi amfani da abin da ke a kasa.
kari a kan wannan kuma ya zama wajibi ga ‘yan makaranta su rikaa shiga kungiyoyi na makaranta ko kuma wasu harkoki. Duk da yake karatu ne ya kai su makaranta, amma ba shi kadai ba ne abin da za su iya karuwa da shi. Idan muka duba da dama akwai mutane manya a kasarmu wadanda harkokin da suke yi ba wai karatun da suka yi ba ne a jami’a ya kai su matsayin. Saboda haka ya zama dole su rika sa kansu cikin wandannan abubuwan saboda ci gaba. Idan ban mantaba, akwai lokacin da Ministan Lafiya ya je yayen dalubabn wata jami’a, inda ya basu irin wannan shawarar a matsayinsa na Farfesa a Najeriya. Don haka dole su rika shiga harkokin makaranta da yawa. dalibi zai iya zavan wani abu guda daya ko biyu da zai rika yi baya ga karatun da ya kawo shi. Daga ciki akwai shiga kungiyoyi na dalubai, harkokin wasanni da dai sauransu.
A karshe kuma ina mai jan hankalin iyaye da kada su mayar da hankalinsu wajen tunanin cewa karatun boko ne kadai ya zama hanyar da suke ganin yaransu za su zama wani abu a duniya. Ya kamata a kara musu da wasu abubuwan. Idan a matsayinka na baban yaro, kai dan kasuwa ne, lokacin hutu abar yaran ya je kasuwa domin wannan zai sa shi ya samu horo a harkar. Idan kuma a wani ofishi kake aiki, to kana iya zuwa da shi don ya ga yadda abubuwan suke tafiya a nan, kuma zai iya taya ka kanana ayyukana, kamar su tura sakonnin ko aike, da dai sauransu.
Dafatan wannan makalar za ta amfani iyaye da ‘ya’yansu.
Aliyu Khalid 08038597907.