Mafitar Arewa a Dokar Harajin Tinubu

Abubuwan da suka ya kamata shugabannin Arewa su yi don bunƙasa tattalin arziki da kuɗaɗen shigan cikin gidan jihohinsu da kuma uwa uba, tabbatar da cewa ba a ƙwari yankin ba a sabuwar dokar harajin Shugaba Tinubu

Mafitar Arewa a Dokar Harajin Tinubu

A yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan ƙudurorin sabuwar dokar haraji a Nijeriya, shin me ya kamata shugabannin Arewa su yi domin bunƙasa tattalin arziki da harajin cikin gidan yankinsu, da kuma uwa uba, tabbatar da cewa ba a ƙwari al’ummar yankin ba?

Al’ummar Arewa, musamman gwamnoni da sarakuna da ’yan majalisar dokoki dai na zargin akwai wata ƙullalliya a cikin sabuwar dokar da ke ƙokarin fifita jihohin Legas da Oyo da Ribadu da Abuja, da kuma ƙwarar yankin Arewa da sauran jihohi.

Aminiya ta tattauna da masana tattalin arziki da kuma fannin tattara haraji daga yankin Arewa inda suka bayar da shawara kan matakin da ya kamata jagororin yankin su ɗauka kan wannan lamari mai cike da ruɗani, ta yadda ba za su zama kurar baya ba.

Dambarwar dokar haraji:

Kudurorin sabunta dokar haraji da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 3 ga watan Satumba na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce tare da fuskantar tirjiya musamman daga Arewa, da ke zargin tsarin da rashin adalic ga al’ummarsu.

Kwamitin da shugaban ƙasan ya nada a ƙarƙashin jagorancin wani masanin tattara haraji mai suna Taiwo Oyedele don samar da gagarumin sauyi a tsarin tattara haraji, da gudanar da shi da kuma rarraba shi ya samar da ƙudurin sabuwar dokar.

A ranar 28 ga watan Oktoba a garin Kaduna, ita ma Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa da ta ƙunshi daukacin gwamnonin ƙasar nan 36 a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima, ya bayar da shawarar janye ƙudurin dokar na wucin gadi don bayar da damar ƙarin tuntuɓa da kuma warware taƙaddamar da ke cikinsa.

Amma shugaban ƙasa ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga ya yi watsi da buƙatar inda ya nemi majalisar ta bar majalisar dokoki ta gudanar da aikinta a kai.

“Shugaba Tinubu ya sami saƙon Majalisar Tattalin arzikin Ƙasa na kan janye ƙudurin dokar haraji daga majalisa don ba da damar ƙarin tattaunawa, ya kuma yaba wa majalisar musamman mataimakinsa Kashim Shettima da gwamnoni bisa wannan shawara.

“Ama ya yi imani da cewa tsarin majalisar dokoki ya bayar da wannan dama, a saboda za a iya yin sauye-sauye ba tare da an janye ƙudurin ba,” inji shi.

A nata ɓangaren majalisar dattawa ta ci gaba da tattauna lamarin, inda a ranar 27 ga watan Nuwamba mataimakin shugabanta, Sanata Barau Jibrin ya yi watsi da buƙatar sanatoci kamar Ali Ndume da Abdul Ningi na hana wata tawaga shiga majalisar don yi mata bayani a kai duk da cewa ziyarar ba ta cikin jadawalin ranar.

Bayan zazzafar muhawara a kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar ya bai wa tawagar damar shiga zauren tare da yin bayanin. Washegari bayan kammala kammala karatu na biyu a kan ƙudurin, majalisar ta umarci kwamitinta na kudi ya tattauna lamarin tare da sauraron shawarwari a kai, ya kawo rahoto cikin kwanaki shida.

Sai dai bayan an yi Allah wadai da shi, musamman daga jiharsa ta Kano, Sanata Barau ya dakatar da kwamitin daga aikin a ranar 4 ga wannan wata na Disamba, ya nada sabon kwamiti mai mambobi daga yankunan siyasa shida na ƙasar nan a ƙarƙashin jagorancin Sanata Abah Moro daga jihar Benuwai, domin tattaunawa da ɓangaren shugaban ƙasa a ƙarƙashin Ministan Shari’a Lateef Fagbemi don warware ɓangarorin da ake da taƙaddama a kai.

Washegeri shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele ya soki ƙudurin a yayin zama da shugaban majlisar Sanata Godswill Akpabio ya jagoranta, cewa majalisar ba ta cimma wata matsaya kan dakatar da kwamitin kudi daga aiki a kan ƙudurin ba, don haka kwamitin na cigaba da gudanar da aikinsa da niyyar kawo rahoto.

Sanata Akpabio ya bayyana cewa da zarar ƙuduri ya tsallake karatu na biyu, to lallai ya wuce matakin a janye shi, don haka abin da ya rage shi ne kawai kwamitin kudin ya fara aikinsa na tuntuɓar jama’a da kuma sauraron bahasinsu a kan lamarin.

Fargabar ’yan Arewa

Ɗaya daga cikin manyan fargabar ’yan Arewa kan sabuwar shi ne, rage kason harajin da jihohin yankin ke samu, a yayin da jihohi da ke da masan’antu da hedikwatocin kamfanoi irinsu Legas da Ogun da Ribas da kuma Abuja, za su samu ƙarin kudaden shiga.

A sabon tsarin dokar, jihohin da aka tattara kudin harajin sayen kayayyaki (VAT) ta wajensu, za su koma amsar kaso kashi 60% saɓanin tsarin yanzu na kashi 20. Shugabannin Arewa na zargin cewa idan dokar ta tabbata za ta ƙara kason da jihohi ukun can da Abuja za ke samu, na sauran jihohi irin nasu zai ƙara raguwa.

Mi’ara koma-baya

Amma wani tshohon ministan kudi, Dokta Yerima Lawal Ngama ya ce masu tsara dokar sun fito sun ƙaryata kansu da kansu, inda suka ce a sabon tsarin, za a yi la’akari ne da wruin da aka yi sayayyan kayan da aka karɓi harajin a kansu, a maimakon wurin hedikwatar masana’anta ko kamfaninsa yake.

Ya ce hakan na nufin abin da jihar Legas da kuma takwarorinta ke samu a tsarin yanzu, zai ragu sosai.

Tsohon ministan wanda ya danganta bayanin nasu da addu’o’in jama’ar Arewa, amma ya ce abin da ya rage a yi shi ne a shigar da bayanin nasu a rubuce cikin sabuwar dokar, don gudun fuskantar taƙaddama a gaba.

Karɓar harajin dukiyar gado:

Haka kuma ana zargin dokar na shirin ɓullo da tsarin karɓan haraji a kan dukiyar da mamaci ya bar wa magada, da kamar kashi 25 na dukiyar gadon.

Ɗaya daga cikin masu wannan zargi shi ne Farfesa Kabiru Isa Dandago na jami’ar Bayero da ke Kano. Ya ce a baya tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya kafa dokar harajin gadon a lokacin da ya yi mukin soja, kafin daga bisani gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha ta soke.

Rushe Hukumar TETFund

Akwai kuma zargin cewa sabon tsarin na da aniyar soke hukumar tallafa wa manyan makarantu (Tetfund) da wasu takwarorintata.

A yanzu dai hukumar ta Tetfund na samun kudinta ne ta hanyar amsar kashi 2% na ribar da kamfanonin ƙasar nan ke samu.

Malamin jami’ar ya yi zargin cewa, a tsarin sabuwar dokar hukumar Tetfund za ta riƙa karɓar kashi 50% ne kawai na abin da take samu a yanzu daga kasafin kudi na shekarar 2025 da ke tafe. Idan sabuwar dokar ta samu shiga kuma, ragowar kasha 50 din za a raba shi ga hukumin NITDA da NASENI, kafin a soke hukumomin uku dungurugum a shekara ta 2030, don karkatar da daukacin kudin ga asusun dalibai da shugaban ƙasa Tinubu ya ƙirƙiro.

Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) tuni ta yi tir da lamarin tare da barazanar yajin aiki matuƙatar ƙudurin soke Hukumar ta Tetfund ya zama doka.

Amma dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin shirin ruseh hukumomin, ta baikin mai taimaka wa shugaban ƙasa a ɓangaren yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga.

Mafitar Arewa 

Aminiya ta zanta da wani tsohon muƙaddashin babban akanta na tarayya Alhaji Idris Augie da kuma wani masanin tattalin arziki, Dokta Yushau Aliyu, inda daukacin masanan suka ce ƙudurin sabuwar dokar ba lamari ne da ya kamata a yi masa gaggawa a majalisar dokoki ba, kamar yadda shugaban ƙasa Bola Tinubu ke nema.

Alhaji Idris Augie ya ce dole ne al’ummar Arewa ta nuna godiyarta ga Sanata Muhammad Ali Ndume da sauran takwarorinsa da suka zaƙe kan ganin buƙatar gaggawa wajen yin dokar bai wuce ba har sai an yi masa cikakken nazari tukuna.

“Idan da an bi ta su Sanata Barau da a yanzu ana maganar yi wa ƙudurin doka ne kawai,” in ji tsohon Akantan.

Masanin ya buƙaci jagororin Arewa da su nemi masana daga ɓangarensu don yin dogon nazari a kai tare da gabatar masu da wuraren da ke buƙatar yin gyara a kai.

Shi ma a zantawarsa da Aminiya, masanin tattalin arziki, Dokta Yushau Aliyu, ya ce “lallai babu makawa ƙasa na buƙatar haraji, amma dole ne a tsaya a yi nazari a kan yadda za a tattara shi da kuma wadanda za su gudanar da aikin, ba wai a miƙa shi ga ’yan kwangila kawai ba, wadanda za su riƙa karɓa tare da kwashe wani adadinsa mai yawa da sunan ladar aikinsu.”

Ya ce akwai kuma abubuwa masu kyau da fa’ida a cikin ƙudurin dokar kamar wanda ya shafi dauke wa masu ƙaramin samu da kuma ƙananan kamfanoni biyan haraji, da kuma hana karɓar haraji barkatai.

Ya ce, “Allah Ya albarkaci yankin Arewa da girman ƙasa da arzikin ma’adina da ya kamata yankin ta ci gajiyar su ta hanyoyi daban-daban, a maimakon ƙarfafa dogaro ga asusun tarayya kadai.”

Hakan in ji shi, zai samar da aikin yi ga al’ummar Arewa da kuma samar da kudin shiga ga gwamnati tare da rage matsalar rigingimu da yankin ke fuskanta.

“Ina dalilin da za ariƙa daukar amfanin gona tare da dabbobi kamar shanu ana kai su kudu ba tare da an sarrafa mafi rinjayensu a nan Arewa ba?

“Sannan ina dalilin da za a dauki haraji kamar na wannan waya da nake yi da kai a nan, a kai harajinsa ga Legas saboda kawai a can ne hedikwatan kamfanin ya ke?

“Dole ne gwamnonin jihohin Arewa su tashi tsaye su dauki ƙwararru a wannan ɓangare don yin nazari a kan dokokin da kuma ba su shawara a kai, inji masanin,” in ji shi.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra