Magaji dambatta ya rasu
Allah Ya yi wa Alhaji Magaji dambatta, daya daga cikin dattawan Arewa,Alhaji Magaji dambatta rasuwa, shekaranjiya Laraba, a wani asibiti da ke Abuja. Marigayin, wanda jiya Alhamis ne aka yi jana’izarsa, bai dade dawowa daga wani asibiti ba, a Landan. Wakili ne a taron kasa daga Jihar Kano, da aka kammala kwanan nan ya shiga […]
Allah Ya yi wa Alhaji Magaji dambatta, daya daga cikin dattawan Arewa,Alhaji Magaji dambatta rasuwa, shekaranjiya Laraba, a wani asibiti da ke Abuja.
Marigayin, wanda jiya Alhamis ne aka yi jana’izarsa, bai dade dawowa daga wani asibiti ba, a Landan.
Wakili ne a taron kasa daga Jihar Kano, da aka kammala kwanan nan ya shiga jerin wadanda suka mutu a wajen taron, wanda a daidai lokacin da jami’an Babban taron kasa ke shirin karkare ayyukansu, sai aka samu labara mai tayar da hankali na rasuwar daya daga ciikinsu, wato wakili daga Jihar Kano, Alhaji Magaji dambatta.
Alhaji Magaji dambatta, yana wakiltar kungiyar kyautata zamantakewa da al’adu, daga yankin Arewa maso Yamma, ya rasu ne a asibitin Garki da ke Abuja, inda aka kai shi bayan da ya dawo daga kasashen waje, inda aka duba lafiyarsa.
An haifi Alhaji Magaji dambatta a shekarar 1931. Ya halarci Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya yi aiki a matsayi wakili da kuma Editan yanki na Cibiyar Yada Labarai ta Najeriya (NBC). Ya zama Babban Jami’in Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Arewa, sannan ya zama Babban Jajmi’in Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Yankin a shekarar 1961.
Marigayin, wanda ya taba zama Jami’in Yada Labarai na Yankin Arewa, kuma wakili da Editan Jaridar Daily Comet a Kano, tsakanin shekarun 1950 zuwa 1953. Sannan ya zama minister a ofishin Jakadancin Najeriya da ke Washington ta Amurka, a tsakanijn shekarun 1973 zuwa 1978, kuma ta taba zama dan hukumar guidanarwar jaridar Daily Times.
Marigayin kwararren dan jarida ne, wanda ya yi aiki da gidan Rediyon Jihar Kano da Kamfanin Buga Jaridu na Triumph da Hukumar Samar da Gidaje ta Tarayya da Kuma Rediyon Nagarta.
Ya taba zama Shugaban Hukumar Amintattu ta kungiyar Dattijan Arewa, sannan ya kasance daya daga cikin wadanda suka kungiyar NEPU. An karrama marigayin da lambobin yabo da dama, wadanda suka hada da ta Gwamnatin Masar a shekarr 1961; sannan ya taba zama daya daga cikin ’ya’yan kwamitin bai wa shugaban kasa shawara (PAC), wadda aka kaddamar a shekarar 2010.
Shugaban Taron kasa, Mai Shari’a Idris Kutigi, ya nuna matukar alhininsa bisa ga wannan labara mai sosa zukata, don haka a madadin sakatariyar taron, kutigi ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Alhaji Magaji dambatta. Sannan ya yi addu’a Allah Ya kyautata makwancinsa.