Magaji Isa, Jalingo
Alumman Hausawa mazauna garin jihar Edo suna ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Isah Adamu Sarkin Hausawa Benin. Alhaji Isah Adamu ya rasune daren wayewar gari na ranar Asabar da ta gabata a wani asibitin babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya na tsawan lokaci. Sarkin Hausawan ya rasu yana da […]
Alumman Hausawa mazauna garin jihar Edo suna ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Isah Adamu Sarkin Hausawa Benin.
Alhaji Isah Adamu ya rasune daren wayewar gari na ranar Asabar da ta gabata a wani asibitin babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya na tsawan lokaci.
Sarkin Hausawan ya rasu yana da shekaru 80 a duniya kuma ya yi shekara hamsin da bakwai (57) yana shugabancin jama’a amatsayinsa Sarkin Hausawa Benin ya dare wannan kujera ta Sarkin Husawa ne bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Adamu wato tun daga shekara ta 1958-2015 kuma ya bar matan aure daya da ‘ya’ya maza shida (6) da ‘ya’ya mata shida (6) da jikoki acikin ‘ya’yansa din akwai wanda yake aiki da ofishin INEC dake Abuja sai kuma dayan wanda yake koyarwa a wata makaranta a Ilorrin jihar kwara.
Babban dansa Adamu Isah Adamu ya siffanta halayyar sarkin da ce wa sarkin mutumne mai kyakkyawar dabi’a kuma mai hakuri da sanin ya kamata na iya zama da jama’a  “A matsayi na na Babba a cikin ‘ya’yansa guda goma sha biyu (12) ban taba jin yana sa-in-sa da wani ko wasu mutaneba a cikin gida ko a waje  kuma mutum ne mai kulawa da adininsa ba yi da wani nuna banbanci acikin aikinsa na shugabancin jama’a da muka tashi muka sameshi yana yi  kuma mai hakuri da juriya akan sha’anin abinda da ya shafi rayuwa da kuma harka da jama’a har Allah ya sa mutuwa ta zo ta rabamu da shi sai dai muce Allah ya gafarta masa ya sa aljanna ta zama makomarsa’’ Kuma tunin har anyi suturansa a Abuja kamar yadda addinin musulunci ya tsara  Allah ya jikansa.