Magana Zarar Bunu Ce
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin rassan jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna da suka hada da na unguwanni da kananan hukumomi da kuma ta jiha sun hallara a dakin taro na Marigayi Umar Musa ‘Yar’aduwa a ranar Asabar da ta gabata don ganawa da Gwamna Nasir Ahmed el-Rufa’i su sanar masa sun amince shi da […]
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin rassan jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna da suka hada da na unguwanni da kananan hukumomi da kuma ta jiha sun hallara a dakin taro na Marigayi Umar Musa ‘Yar’aduwa a ranar Asabar da ta gabata don ganawa da Gwamna Nasir Ahmed el-Rufa’i su sanar masa sun amince shi da kuma Shugaba Muhammadu Buhari ne za su tsayar a zabubbukan gwamna da na shugaban kasa. Bayan haka nan kuma sai Gwamna ya rusuna gabansu, ya nemi gafara bisa abin da ya kira kura-kuran da ya yi, ya kuma kara da cewa idan a cikinsu babu wanda zai ce ga shi ya saba mar, har ya zuwa karshen wannan ranar, ba zai sake neman gafarar kowa ba.
Malam Nasiru el-Rufa’i ya nuna cewa fada fa da shi ba dadi, domin wanda duk ya buga sai ya fadi, kamar yadda marigayi Shugaba ‘Yar’ Aduwa ya ja da shi, ya kuma kwanta dama, haka nan kuma Goodluck Jonathan ya fafata da shi, shi ma hakan ya sa ya tuntsuro daga mulki, ya koma can kauyensu Otueke, ya tsuguna. Wadannan ba kalamun da suka kamata su fito daga bakin shugaba ne ba, kuma a gaban wasu shugabannin jam’iyya.
Bisa ga dukkan alamu dai iska na wahalar da mai kayan kara, kuma giyar mulki na bugar da Gwamna Nasiru, domin kuwa ana iya cewa rusunawar da ya yi gwiwar rani ce, ba ta neman sulhu ba ce, ta ci gaba ce da fito-na-fito shi da abokan siyasarsa a jam’iyyar APC wadanda yake nema ala kulli-halin ya yakice su daga cikin jam’iyyar, ya kuma yi ba tare da su ba. Abin mamaki game da haka shi ne Gwamna Nasiru na kokari ne ya mayar da jam’iyyar APC kamar tasa ce shi kadai, sai yadda ya ga dama zai karkata akalarta, ya manta cewa dimokuradiyya ake yi a kasar nan, ita ce kuma ta ba shi damar zamewa gwamna har aka ce shi ne jagorar jam’iyyarsa a jiharsa. A yanzu dai a jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta fara ne da Gwamna Nasir ta kuma kare da Malam el-Rufa’i. Shi ne kadai tsuntsu a cikin keji, kuma tilas ne kowa da kowa ya yaba masa ya kuma rera wakarsa. To, ya kamata a sanar da shi cewa zai jagoranci jam’iyyar ne zuwa ga wani wagegen rami a hakan, idan bai hankaltu ya yi karatun ta-natsu ba, ya kuma san annabi ya faku.
Idan ya yi dambarwa da wanda ya riga mu gidan gaskiya, inda kowa ma zai je, ya kuma fafata da wanda yace hakan ne sanadiyyar komawarsa kauyensu ya tsuguna, sai ya tuna a Jihar Kaduna yake, jihar da ke cike da ‘yan duniya da ‘yan boko wadanda suka dame shi, suka shanye a dukkan fannonin da yake takama da su. Ana masa ganin wani sabon shiga ne a harkar siyasa, wanda ke tinkaho da wani mutum guda, wanda idan babu shi dukkan al’amuransa za su rurrushe kamar tubalin toka. kar fa ya manta cewa jam’iyyar da yake tinkaho da ita a kasar da kuma nan Jihar Kaduna dagogo-rigo ce ko kuma a ce tamkar teburi ne mai kafafuwa uku, wanda ba wuya ya kife da zarar an dan taba shi.
Takamar Gwamna Nasiru dai ba ta wuce jam’iyya ba, to ya tuna ita ce daya ba ya yin daji, haka nan kuma duk yadda ya so da mallakarta sai ya hada da wasu. To, a halin da ake ciki babu wasu muhimman shugabannin jiha da aka zaba. a maimakonsu ne Gwamna Nasiru ya doddora wasu jeka-na-yi-ka, wadanda babu abin da suke iya turzawa sai abubuwan da Gwamna Nasir ke so. Haka nan kuma a sauran rassan jam’iyyar na kananan hukumomi da na unguwanni an yi dauki-dorar shugabanni ne domin ba a yi zaubbukan congress ba a wadancan wuraren, haka nan ake kara-zube. To muddin aka tashi yin tarurrukan congress a Jiha da kuma kananan hukumomi da unguwanni, idan uwar jam’iyya ta bayar da umurni a gabatar nan gaba kadan, babu ta yadda za a yi Gwamna Nasiru ya hana wadancan mutanen da bai yi da su taka muhimmiyar rawa wajen zaben sababbin shugabanni, kuma ba zai hana a kwace jam’iyyar daga gare shi ba cikin ruwan sanyi.
Idan har aka kwace jam’iyyar daga hannunsa saboda ana gudanar da ita bisa rashin adalci da biye son zuciya a halin yanzu, ta ina ke nan zai tattaka ya kai ga biyan bukatunsa nan gaba? Jama’a ne dai jam’iyya, su ne kuma suka taru suka rirrike masa tsanin da ya hau ya kai ga mukamin gwamna. To idan bayan ya hau, ya sanya kafafu ya shure wancan tsanin da jama’a suka saka masa, a ina zai samu wanda zai taka ya sauko nan gaba? Jama’a dai su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba, tilas a bi ra’ayinsu, domin muryar jama’a na gaba da komai, karfi ke gare ta kamar shari’a.
To, an ji Gwamna Nasiru ya rusuna ya nemi gafara: shi ke nan sai a bi shi zoi-zoi, magana ta kare ke nan, kuma banbance-bambancen da suka kai ga rashin jituwa sun wanye ke nan? Ai a bisa akida ne aka nuna wa Gwamna Nasiru kura-kuransa wadanda aka nemi a gyara don a ji dadin tafiya tare, to shi ke nan sai a mance da su a ci gaba da bin Nasiru ido rufe don yana gwamna? Wannan ne fa abin da dimbin ‘yan jam’iyyar APC ke ganin ba ta sabuwa, domin kuwa duk sulhun da za a yi sai ya kunshi tattaunawa don a fahimci juna, a kuma warware duk wata takaddama da rashin fahimta da ke tsakaninsa da ‘ya’yan jam’iyya.
Babu wanda ke son jayayya da shi ta yadda za a buga har sai wani ya bakunci barzahu kamar yadda ya yi da marigayi ‘Yar’aduwa, ko kuma a yi ta kai ruwa rana da shi har sai ya koma kauyensu na Daudawa, kamar yadda ya sanya wando kafa guda da Goodluck Jonathan har ya ya kai shi komawa kauyensu na Otueke.
Ya dai kamata Gwamna Nasiru ya sani siyasa dai ta jama’a ce, babu wanda zai yi waran gwanki ya yi nasara, haka nan kuma wanda duk aka mayar saniyar ware ba zai kai labari ba. To kada Gwamna Nasiru ya yarda ya rabu da jama’ar da nan gaba zai neme su da kokon bara domin kuri’unsu. Magana zarar bubu ce, baki kuma shi ke yanka wuya.