Maganar da shugaba Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan Najeriya ragwaye ne gaskiya ce ko akwai gyara?

A makon da ya gabata ne aka jiyo Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cewa mafi yawan matasan Najeriya ragwaye ne. Maganar ta haifar da cece-kuce da muhawara mai zafi a tsakanin al’ummar Najeriya, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa. Duk da cewa mataimakin shugaban kasar, Femi Adesina ya bayyana cewa ba a faminci bayanin shugaban […]

Maganar da shugaba Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan Najeriya ragwaye ne gaskiya ce ko akwai gyara?

A makon da ya gabata ne aka jiyo Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cewa mafi yawan matasan Najeriya ragwaye ne. Maganar ta haifar da cece-kuce da muhawara mai zafi a tsakanin al’ummar Najeriya, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa. Duk da cewa mataimakin shugaban kasar, Femi Adesina ya bayyana cewa ba a faminci bayanin shugaban bane, wasu suna ganin cewa lallai shugaban ya yi kuskure, wasu suna suna ganin ya yi daidai. Wanan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma amsoshin da suke bayarwa:

 

Ba a fahimci maganar Buhari ba ne – Sulaiman Saminu

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Sulaiman Saminu: “A gaskiya a kasar nan akwai cima zaunen wadanda ba su son motsawa ko kuma mu ce masu raina karamar sana’a, to shi Shugaba Buhari da irin wadannan mutane yake. Amma kowa ya san mu ’yan Arewa mutane ne masu neman na kansu. Ba mu jiran sai wani ya ba mu ko kuma mu zuba gwamnati ido sai ta sama mana aiki don mu karbi albashi.”

 

Akwai gyara a maganar – Abdullahi Alhassan

Daga Jamilu Adamu, Abuja 

Abdullahi Alhassan: “A ra’ayi na akwai gyara, dalilina a nan kuwa shi ne babu yadda za a yi matashi ya je ya yi karatu a karshe ace shi rago ne, bayan mafi yawancin matasa sun bata lokacinsu a wurin neman ilimi domin cigaban rayuwarsu da ta al’umma baki daya, amma Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza kulawa da matasan da suka yi karatu akan sha’anin ayyuka da abubuwan yi, don haka kulawar gwamnati ga matasa shi ne zai sa duk matashin da bai da niyyar neman ilimi ya mike tsaye. Toh idan ya ga gwamnati na taimakawa dalibai wurin neman ilimi, dole wanda bai da niyyar neman ilimi ya tashi ya nema don ganin tallafin ya zo gare shi. Amma rashin taimakon dalibai da gwamnati ba ta yi a harkar ilimi ya sa gwamnatin take ganin matasan ragwaye ne.”

 

Babu mamaki akwai abin da ya gani – Hussaini Tata

Daga Amina Abdullahi, Yola

Hussaini Tata: “Babu mamaki akwai abin da ya gani ne shi ya sa ya yi wannan furucin. Amma ni ba zan kira kaina rago ba tunda ina da aikin yi. Koda ban samu aiki a nan ba, na kan je wani gurin neman aiki kamar su kwashe shara da sauransu. Kin ga ko ni ba rago bane. Amma akwai wadansu matasan da ke zaune a gida wadanda babu abin da suke yi sai dai su zauna a basu ko kuma su kasance masu roko. Babu mamaki Shugaba Buhari ya alakanta wannan furucinsa ne ga irin wadannan matasan.” 

 

Akwai kuskure a maganar Buhari – Murtala Abdurahman

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Murtala Abdurahman: “Wannana maganna da Shugaba Buhari ya yi ba daidai ba ce, domin a yanzu idan aka ce wani kamfani ko wata ma’ikata ta gwamnati za ta dauki ma’aikata 100, to sai ka samu mutum sama da 1,000 sun je neman aiki.  A wurin nan ar wasu za su iya rasa ransu domin kokarin ganin zun smai aikin yi, to irin wadanna mutane ne za a kira da cima zaune? Inda cima zaune ne da ba za su fito s shiga wanann wahala ba. A gaskiya mu ‘yan Najeriya ba cima zaune ba ne. Mafi yawan matasanmu masu kokarin neman na kansu ne. wannan Magana ta Buharoi akwai kuskure a cikinta.”

 

Maganar gaskiya ce – Malam Abdullahi Isah Kurfi

Daga Jamilu Adamu, Abuja.

Malam Abdullahi Isah Kurfi: “A ra’ayi maganar Shugaba gaskiya ce, saboda mafi yawan matasan Najeriya sun fi son su ci a sama, hakan ya sa wasu matasan ke bin ’yan siyasa ko kuma su bige da bangar siyasa a lokacin zabe, matasan Najeriya ba sa son koyon sana’o’i sannan ko karatu matashi ya yi ya fi so ya samu babban aiki a guraben gwamnati wato wuri mai tsoka, idan kuma bai samu ba sai ya yi ta zaman kashe wando ba tare da wata sana’a ba sai maula a ofisoshin ’yan siyasa.

Sannan a bangaren gwamnati ta duba matasan da ke da hazaka a fannin sana’o’i don ba su tallafi hakan zai kara masu kwarin gwiwa a fannin da suka sa a gaba, kuma zai ragewa matasa dogaro da ayyukan gwamnati tare da rage bangar siyasa.”

 

Ban ga laifin maganar  ba –Sani Abdullahi

Daga Amina Abdullahi, Yola

Sani Abdullahi: “Ban ga laifin maganar da ya fada ba. Domin akasarin matasa idan an je waje da yawa za a same su cikin shaye-shaye da wasu harkoki da bai kamata ba. Ai bai ce duka matasa ba, wadansu ya ce. Idan aka duba kashi 75% na matasa a cikin gari, za a samu cewa akwai irin wadannan ragwayen matasan da yake nufi. Rashin ayyuka da karatu na matasa, shi ya kawo mana matsaloli kamar su rikicin Boko Haram da fadace-fadace. Idan an duba wadansu wajan za a ga cewa matasan na sace-sace ko fashi. A gefen Kudu kuma banda wadanda suka yi karatun in ban da damfara da suke yi a bankuna da wadansu wajaje, ba abin da suke yi. Duk matasa ke aikata su ba manya ba. Dole ne idan mutum ya ga irin wadannan ababen zai ji zafi. Don haka ni ban ga laifin shugaba Buhari ba.”