Maganar magabata kan dunkule Najeriya ta tabbata

Juma’a, 28 ga watan Fabrairun shekarar 2014, rana ce  da aka yi bukin tunawa  da illar da Turawa suka yi  wa kan hadin kasar. An dai zabi wannan ranar ce don bikin murnar cikan shekaru  dari cif-cif da dunkule yankunan Kudanci da kuma Arewacin Najeriya a matsayin kasa guda daya don a zama al’umma daya, […]

Maganar magabata kan dunkule Najeriya ta tabbata
Maganar magabata kan dunkule Najeriya ta tabbata

Juma’a, 28 ga watan Fabrairun shekarar 2014, rana ce  da aka yi bukin tunawa  da illar da Turawa suka yi  wa kan hadin kasar. An dai zabi wannan ranar ce don bikin murnar cikan shekaru  dari cif-cif da dunkule yankunan Kudanci da kuma Arewacin Najeriya a matsayin kasa guda daya don a zama al’umma daya, wacce Turawan mulkin  mallakan kasar Birtaniya suka yi don samun saukin gudanar da mulki don rashin wadatattun kudi ko kwararrun jami’ai daga nahiyar Turai.
Wannan al’amari kuwa ya faru ne shekaru kusan 14 bayan sun kafa daularsu a Kudancin kasar nan; kaman shekaru 11 bayan sun ci nahiyar Arewa da yaki. Ko a wancan lokacin ma al’ummomin wadannan nahiyoyi guda biyu sun nuna matukar rashin amincewarsu da haka domin kuwa abin da aka yi ya kasance tamkar gamin-gambiza ne wacce ba a yi amanna da ita ba. Da farko dai mutanen Kudanci sun soki lamarin hada su da wadanda suka kira masu yakin jihadi, wadanda ba su da ilmi irin wanda Turawan suka dade da kawo wa yankinsu tun a shekarar 1860, sa’ilin da Turawan kamfanoninsu suka kakkafa sansanin kasuwanci a yankunan Ikko da Kalaba. Su ma jama’ar Arewa sun nuna rashin gamsuwarsu game da wannan yunkurin hade su da al’ummomin da suka nuna cewa al’adunsu da addininsu da kuma kyakkyawan tsarin zamantakewarsu sun sha bamban da na wadanda ake son a gwama su wuri guda. Dukkan al’ummomin dai sun nuna cewa ai kare da biri ba su jera gami, kuma yin haka tamkar kayan aras ne za a dorawa gwami.
Amma da yake ba shawarsu aka nema game da haka ba sai aka ki jin batunsu, aka kuma jefa su a kwandon shara, aka ci gaba da abin da Turawan ke bukata. Ilai kuwa hakan ya zamanto tamkar saka ce da mugun zare Turawan suka yi, domin har ya zuwa lokacin da suka mayar da mulki ga al’ummomin kasar nan, bayan shekaru 46 cikin zaman kuncin da aka jefa su, ba a daina korafi ba game da haka, kuma matsalolin da hakan ya haifar ne  har yanzu ke addabar kasar nan, su ne kuma ke hana ta zaman lumana da ci gaba.
Babbar illar da ta fi fitowa fili game da haka kuwa ita ce ta raunana hadin kan jama’ar kasar nan, abin da ya samo asali daga rashin hakuri da juna da kuma sakamakon bambance-bambancen siyasa bisa tafarkin kabilanci da kuma gani-ganin da al’ummomin Najeriya ke yi wa juna saboda bambancin addini. Har gobe jama’an kasar nan suna fadin hadin kai ne kawai da fatar baki, ba su kwatanta ayyukan da za su nuna haka.
To amma sai ga shi nan a ranar Juma’ar da ta gabata tsofaffin shugabannin kasar nan masu rai, musamman ma na Arewa wadanda a gida kawunansu na rarrabe, wasunsu ba su ko-ga-maciji da juna, sun taru wuri guda, suna ta fara’a a gaban Maimalfa, kaman ba su ne suke ke yi wa juna bi-ta-da-kulli ba,  suna kokarin nunawa duniya cewa kawunansu na hade, alhali kuwa ba haka ba ne. Kuma idan da taron hadin kan ‘yan Arewa ne don a yi magana da murya guda ba za su taru kaman haka ba.
Wasunsu sun biye wa masu son zuciya, sun gwammace yin amfani da addini don rarraba kawunan jama’a ta yadda za su ji dadin mulki cikin sauki. Shi ya sa tsoffin shugabannin kasar nan, musamman ma daga Arewa ba su da hadin kai, sun gwammace su yi ta zaman ‘yan marina, kowa da inda ya mayar da gabansa. To, ashe ana iya cewa wargi wuri yake samu, da gangar ne wadancan tsofaffin shugannin kasar ke bari ana amfani da su don wargaza  kawunansu, domin ta haka ne ake kai wa ga rarraba hankulan ‘yan kasa, a yi masu mummunar ta’asa ko muguwar munakisar da za ta hana su samun ingantaccen shugabancin da zai ba su daman cin moriyar arzikin kasarsu.
A yanzu ga shi nan da ake so a yi amfani da tsoffin shugabannin don aiwatar da manufar da ba za ta amfani kasar da komai ba, ai lallashinsu aka yi don su halarci wannan gagarumin bukin da aka yi wanda manufarsa ita ce ci gaba da tallafawa Turawa da makarrabansu na nan cikin gida  don su kara karfafa dabarun kwarar jama’ar Najeriya.
Dalilai da yawa sun tattabar da haka.  
Da farko dai shi wannan buki ba a tsire shi bisa manufar kawar da abubuwan da ke kawo rarrabuwar kawunan al’ummomin kasar nan ba bisa wadancan korafe-korafen da kakkanninsu suka yi tun can farko don nuna rashin dacewar hadewar. Haka nan kuma ba a dauki kwararan matakan karfafa zumunci da dangantaka tsakanin mutanen Arewa da Kudu ba, ta yadda za a cusa kauna da kiyaye hakkokin juna don a samar da ingantacciyar zamantakewa mai dorewa tsakaninsu, sai aka tsaya sharholiyar wofi da dukiyar talakawa.
To ga shi nan an yaudari al’ummomin Najeriya cewa wancan tsari na Turawa don dunkule kasar ya yi tasiri, alhali kuwa kowa ya san cewa hakan ya gurgunta hadin kan ‘yan Najeriya ne, musamman ma na Arewaci. To Allah ya sa  shugabannin Arewa sun fahimci haka, kuma hadin kan da aka tilasta musu yi na  kwana guda zai dore don amfanin jama’arsu.