Maganar Sarkin Kano daidai ne – Alhaji Musa Saye

  Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bichi Alhaji Musa Saye ya ce maganar da sarkin Kano ya yi dangane da karbo bashin dala biliyan talatin daidai ne idan aka dubi irin halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki a duniya. Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da wakilin mu, inda ya […]

Maganar Sarkin Kano daidai ne – Alhaji Musa Saye

 

Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bichi Alhaji Musa Saye ya ce maganar da sarkin Kano ya yi dangane da karbo bashin dala biliyan talatin daidai ne idan aka dubi irin halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki a duniya.

Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da wakilin mu, inda ya nuna cewa mai martaba sarkin Kano ya fadi gaskiya musamman idan aka dubi matsayin sa na kwararre a fannin tattalin arziki da matsalolin da ke tattare da ciwo bashi a kasa kamar Najeriya.
Alhaji Musa Saye ya kuma bayyana cewa kudin da shugaban kasa ya ke son karbuwa suna da yawa, sannan wa’adin da aka yi tunanin biyan bashin ya yi kadan, idan aka dubi tsarin karba da biyan bashin da kasashe ke karbowa wanda hakan ce ke jefa kasa cikin yanayi na takura, inda ya yi fatan cewa gwamnatin tarayya za ta bunkasa hanyoyin samar da kudaden shiga ta ta yadda za ta cimma manufofin ta maimakon karbo wannan bashi.
Da ya juya kan jam’iyyarsu ta PDP kuwa, Alhaji Musa Saye ya sanar da cewa matakan da ake dauka na inganta jam’iyyar suna yin tasiri musamman ganin yadda jam’iyyar take kara farfadowa bisa kwazo da jajircewar shugabannin ta na kasa da na jihohi da kananan hukumomi har ma da mazabu 774 da ake da su a kasar nan, tare da yin godiya ta musamman ga daukacin ’ya’yan jam’iyyar da ke fadin kasar nan saboda goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar tun bayan faduwa zabe.
Sannan ya yaba wa ’ya’yan jam’iyyar na karamar hukumar Bichi saboda juriyar da suke nuna wa da yadda suke kokari wajen sake hade kan ’yan jam’iyya duk da cewa ba su da gwamnati, wanda hakan ya nuna da cewa akwai PDP a karamar hukumar, tare da tabbatar da cewa shugabancin sa zai kara bullo da sabbin hanyoyi na bunkasa jam’iyya a kowane lungu da sako na karamar hukumar tare da hadin gwiwar magoya bayan ta.