Maganar Shehu Sani ba sabuwar magana ba ce- Majalisar Dattawa
Majalisar Dattawa ta ce maganar da sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, sanata Shehu Sani ya yi na cewa suna karban makudan kudade ba sabuwar magana ba ce domin kuwa duk bayanan suna kunshe a cikin kasafin kudin majalisar. Mai magana da yawun majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya sanar da hakan […]

Majalisar Dattawa ta ce maganar da sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, sanata Shehu Sani ya yi na cewa suna karban makudan kudade ba sabuwar magana ba ce domin kuwa duk bayanan suna kunshe a cikin kasafin kudin majalisar.
Mai magana da yawun majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya sanar da hakan a shafinsa na facebook a ranar Litinin.
Aliyu Sabi ya kara da cewa, “kusan wani mai rike da mukamin siyasa yana da wasu kudi da aka ware masa domin tafiyar da ofishinsa.”