Maganar yawan mutane

A ’yan kwanakin nan, wasu daga cikin manyan jami’an Gwamnatin Tarayya sun nuna damuwarsu bisa yadda yawan mutanen Najeriya ke karuwa. Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Minsitar Kudi Zainab Ahmed sun yi magana a taron da ya gudana kwanakin baya na Tattalin Arzikin Kasa a kan bukatar a lura da yadda yawan mutane ke […]

Maganar yawan mutane
Maganar yawan mutane

A ’yan kwanakin nan, wasu daga cikin manyan jami’an Gwamnatin Tarayya sun nuna damuwarsu bisa yadda yawan mutanen Najeriya ke karuwa.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Minsitar Kudi Zainab Ahmed sun yi magana a taron da ya gudana kwanakin baya na Tattalin Arzikin Kasa a kan bukatar a lura da yadda yawan mutane ke karuwa a Najeriya. Osinbajo ya ce suna kokari wajen rage yawan karuwar mutane a Najeriya da kusan rabi.

Mataimakin Shugaban Kasa ya ce talauci da rashin ababen more rayuwa na kara bayyana ne saboda yadda mutane suke karuwa da kusan kashi 3 a shekara. Najeriya za ta iya zama kasa ta uku mafi yawan mutane a duniya a shekarar 2050, inda mutanenta za su kai kimanin miliyan 400. Kashi 60 na mutanen a wannan lokacin kuma za su kasance matasa ne. Lallai Osinbajo ya yi gargadin cewa za a iya samun matsala idan ba a shirya ba kafin lokacin, a wani taro da malaman addini a watan jiya.

A nata bangaren, Hajiya Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin Tarayya tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakuna da malaman addini domin bayar da shawara a kan tazarar haihuwa. Yadda mutanen sukai ta cece-kuce jim kadan bayan bayanin Ministar, ya sanya dole ta fito fayyace abin da take nufi a bayaninta. Da take jawabi a taron Majalisar Zartarwa na makon jiya, ta ce ba wai gwamnati za ta kayyade yawan ’ya’ya ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, amma tana nufi ne za a ba iyayen shawara da su rika yin tazarar haihuwa. Ya bayyana shirin gwamnatin ta farfado da tattalin arzikin kasar na [ERGP] wanda ya nuna cewa, “lura da yanayin karuwar yawan mutane yana da muhimmanci wajen cigaban kowace kasa.”

A wani rahoton da Jaridar Daily Trust ta buga a ranar Alhamis na makon jiya, 25 ga watan Oktoba, ya nuna cewa mutanen Najeriya sun karu daga miliyan 45.1 a shekarar 1960 da muka samu ’yancin kai zuwa miliyan 200 bana. Rahoton ya kara da cewa mutanen Najeriya ne kashi 2.57 na mutanen duniya biliyan 7.6. Sannan suna zaune a kasa mai fadin kilomita 910.770.

Saboda dalilan addini da al’ada, wasu daga cikin ‘yan Najeriya sukan yi tofin Allah tsine a duk lokacin da aka ambaci maganar kayyade iyali. Kalmar “kayyade iyali” tana cikin kalmar da ke jawo muhawara mai zafi a yawancin garuruwa masu tsatstsauran ra’ayi a Najeriya. Amma kuma tazarar haihuwa sai ya zanto matsakaicin kalma da wasu ‘yan Najeriya suka yi amma da shi.

Duk da haka, wasu daga cikin masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum suna tunanin cewa yawan mutane ba matsala ba ne, inda suka ce yadda gwamnati ta yi amfani da yawan mutanen shi ne matsala. Wani masanin tattalin arziki ya ce, “Idan kasa na da mutane da yawa masu kirkiri, masu kirkira wajen samar da kudin shiga, to yawan mutane zai zama riba ga kasar.” Amma dai a yadda ake ciki yanzu, kirkirarmu sai a hankali; yawanmu ya ninninka yadda tattalin arzikinmu ke habaka, wanda hakan ya sa kullum muke kara shiga cikin talauci.

Yawancin mutanenmu ba su da fasahar kirkira kamar yadda ita kanta gwamnatin ba ta da isasshen tanadi na lura da muhimman bukatar mutanenta. Wannan lamarin a bayyane yake idan ka lura da alkaluman kasar kamar rashin aikin yi wanda yake a kashi 12 da kuma yadda tattalin arzikin kasar ba ya habaka daidai da yanayin karuwar mutane. Masu sharhi suna cewa ko an samu tattalin arziki mai kyau, kudin shiga da wuya ya biya muhimman bukatar mutanen kasa idan har mutane suna karuwa barkatai. Don haka idan har kasa na bukatar cigaba, dole ya kasance tattalin arzikinta ya fi karuwar mutanenta.

Yanayin yawan mutane, yanayin fadin kasar da suke bukata domin ayyukan yau da kullum kamar noma. Karancin kasa zai iya jawo rashin abinci. Ko rikicin manoma da makiyaya ma yana da alaka da fafutuka a kan kasa. Rashin tazarar haihuwa yana jefa uwa da da cikin wani hali, sannan kuma karuwar mutanen yana kawo tsaiko ga ababen more rayuwa da ma yin rayuwa mai kyau.

Batun kayyade iyali ba karamin lamari ba ne a yawancin bangarorin kasar nan, amma ya kamata gwamnati ta assasa tattaunawa na kasa baki daya a kan maudu’in tunda an hango akwai matsala nan gaba. Kada mu tsaya sai lokacin ya kure.