‘Maganarmu ta karshe da dana kafin masu garkuwa su kashe shi’
Makwabta sun hada baki aka sace yaron, aka kuma kashe shi bayan karbar kudin fansa.
Mahaifin wani yaro dan shekara shida da makwabtansa suka yi garkuwa da shi kuma suka kashe bayan karbar kudin fansa, ya ce masu garkuwar sun ba shi yaron sun yi yi magana kafin daga baya su kashe shi.
Alhaji Mohammad Kabir Magayaki, ya ce kwanaki kadan kafin su kashe yaron, ya yi magana da marigayin ta tarhon masu garkuwar, inda yaron ya bukaci ya kawo kudin fansa saboda za su kashe shi.
- ’Yan fashi sun tare motar banki, sun daka wa kudin cikinta wawa
- Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
- Mazauna gari sun kama ’yan fashi da makami biyu a Kano
- Ana mika Daliban Afaka ga iyayensu
“Na ce masa Muhammadu ka yi hakuri zan ba su kudin, sai ya sake cewa da ni ‘Baba kashe ni fa za su yi.’ Na ce ba za su kashe ka ba sai kwananka sun kare.
“Na ce ya fada masu zan ba su kudin. Na fada masa ya ba su wayar hannunsa mu yi magana da su, amma suka ki amsar wayar a ranar.
“Karshen maganata da shi ke nan.”
Aminiya ta ziyarci gidan mahaifin yaron da ke Unguwar Badarawa, Kaduna domin jin ta bakinsa da kuma alakarsa da wadanda ake zargi da kashe dansa amma bai yarda ya yi magana ba, saboda wadanda ke kusa da shi sun hana shi yin magana.
Sai ya bukaci wakilinmu ya je ya saurari hirar da ya yi a wani shafi na Yutube inda ya yi bayanin yadda aka kashe dansa, duk da cewa ya ba masu garkuwar kudin fansar da suka bukata.
Yadda aka kama masu garkuwar
Da yake bayani a bididyon kan yadda aka kama wadanda ake zargi da kisan dansa a ranar da ya biya kudin fansar, ya ce da shi ne da dansa da kuma wadansu matasa biyu suka tunkari daya daga cikin wadanda ake zargi bayan ya shigo unguwar.
“Na ce da shi Sani kai ne kuka sace min yaro kafin ya yi wata-wata ’yan sanda sun karaso aka yi gaba da shi.
“Daga bisani ya tabbatar wa ’yan sanda sun kashe yaron a Kano.”
Makure shi muka yi har ya mutu – Galadima.
Sani Adamu wanda aka fi sani da Galadima wanda tsohon soja ne, ya ce shi ne ya rike kafafun yaron, shi danyan wanda ake zargin kuma ya rufe wa yaron hanci har sai da ya mutu kafin suka je suka jefar da gawarsa a cikin wani kwatami a Kano.
Ya bayyana haka ne a lokacin da aka gabatar da su a hedikwatar ’yan sandan Jihar Kaduna bayan an kama su hudu kan zargin kisa da kuma sace yaron.
A cewarsa, Umar Mainasara wanda ke sana’ar ruwa shi ne ya rufe hancin marigayin da hannunsa.
Sai kuma Nazifi, wanda makwabcin mahaifin yaron ne, kuma wanda ake zargi da kitsa yadda aka sace marigayin duk kuwa da su biyun sun musanta zargin da ake musu na kashe yaron.
Sai budurwar Sani wacce aka ajiye yaron a gidanta a Kano.
Ya bayyana cewa ita karya ya yi mata cewa yarn dan yayansa ne da ya rasu, kuma ta san yayan nasa da ke Kano kafin ya rasu, saboda haka ta amince ta ajiye yaron, ba ta san sato shi aka yi ba.
A cewar Galadima, Nazifi ne ya tuntube shi da zancen garkuwa da yaron saboda wai mahaifin yaron na da kudi.
Kuma Nazifin ne ya aiki yaron inda shi Galadima yake domin ya sace shi. Haka kuma aka yi, “Don a dauke shi sai na kai shi Zariya daga nan sai Kano.
“Na kuma tuntubi abokina Umar, domin ya rika tattaunawa da mahaifin yaron,” inji Galadima.
Aminiya ta tambaye shi ko mahaifin yaron ya taba taimakon sa da kudi kamar yadda ake fadi sai ya ce, “a’a.”
‘Ni na tattauna da mahaifin har aka kawo kudin fansa’
Shi ma Umar da ke sana’ar sayar da ruwa ya ce shi ne ya rika tattaunawa da mahaifin yaron har aka karbi kudin fansa. Amma shi bai san wanda ya kashe yaron ba.
“Ni ban san wa ya kashe yaron ba a cikinsu. Ni dai an dauke ni domin in tattauna da mahaifin yaron, na kuma yi, aka ba ni Naira dubu 150 daga cikin kudin fansar da aka karba,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko ya rufe masa hanci kamar yadda Sani ya zarge shi, sai ya ce ba gaskiya ba ce domin bai bi Sani zuwa Kano da yaron ba.
Ban san komai ba – Nazifi
Shi kuwa Nazifi ya musanta cewa da hannunsa a cikin garkuwa da kuma kashe yaron da aka yi.
Ya ce ya dade rabonsa da ganin yaron duk da kasancewar katanga ce a tsakaninsu da gidan mahaifin yaron.
Ya ce shi sana’ar sayar da bulawus yake yi a Abuja. A cewarsa, ko magana ba sa yi da Galadima saboda ba sa shiri amma sai yake neman kulla masa sharri.
“Gaskiya Allah Ya sani ban san komai ba domin ni ma a unguwa nake jin cewa an sace yaron,” inji shi.
Gwamnati ta dauki mataki kansu
Yayan wanda ake zargi mai suna Murtala Galadima, ya nemi gwamnati ta dauki mataki a kan wanda ake zargi da kisan yaron domin a cewarsa ba su ji dadin abin da suka aikata ba na kashe yaron da bai ji ba, bai gani ba.
“Akwai bukatar gwamnati ta hukunta masu aikata irin wannan aika-aika domin mun yi tir da wannan abu da ake zargin ya aikata a matsayinmu na ’yan uwansa.” inji shi a wata hira da ya yi da manema labarai.
Sun amince sun aikata laifin -’Yan sanda
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin musamman Nazifi da Sani da Umar sun amsa laifin da ake zarginsu, don haka za a ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu.
Ya kuma ce ’yan sanda sun kwato Naira dubu 840 daga cikin kudin fansar da suka karba na Naira miliyan daya daga hannun wadanda ake zargi.
Ya kara da cewa Sani ne ya kai ’yan sanda inda suka jefa gawar yaron a cikin wani kwalbati a Kano.