Magance furfura a cikin sauki

A kodayaushe mukan yi shafukan kwalliya domin matasa. A yau ina son na tabbatar wa iyayenmu cewa, a harkar ado suma ba a bar su a baya ba. Musamman a lokain da tsufa ya zo musu, furfura kan dada wa mutum tsufa. Wasu kuma halittace ba wai tsufan suka yi ba. Hadin tsawon gashi a […]

Magance furfura a cikin sauki

A kodayaushe mukan yi shafukan kwalliya domin matasa. A yau ina son na tabbatar wa iyayenmu cewa, a harkar ado suma ba a bar su a baya ba.

Musamman a lokain da tsufa ya zo musu, furfura kan dada wa mutum tsufa. Wasu kuma halittace ba wai tsufan suka yi ba.

Na kawo muku hanyoyi da dama wanda za a bi don magance wannan furfura, domin samun gashi baki mai sheki.

•Ana wanke gashi da shamfo mai dauke da sinadarin Aloebera. Yin hakan na dada karfin gashi da kuma saka shi baki.

•Za a iya amfani da lalle a gashi, don yana gusar da furfura. A yi amfani da asalin lalle na gargajiya, sai a hada da koffi na shayi.

Ko kuma za a iya tafasa ganyen shayi sai a kwaba su da lallen kafin a shafa a gashi, sai a wanke gashin bayan sa’a daya.

•Idan ana son gashi ya yi baki sosai a sa konanniyar tafarnuwa a hadin.

Idan an yi amfani da wadannan hanyoyi, za a ga canji domin ba shi da wani illa ga gashi.

•Man zaitun na daya daga cikin ababen da ke dada wa gashi baki da kuma sheki. A dage wajen shafa man zaitun a inda furfurar take za a samu sauki in sha Allah.

  • A samu bawon dankalin turawa sannan a busar da shi a daka a tankade sai a kwaba shi da man zaitun a rika shafawa a gashi har sai ya yi baki.

Tags