Magance rikici tsakanin manoma da makiyaya a Binuwai

Tun kafin a kai ga rantsar da shi kwanakin baya, Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya jagoranci wata tawaga a watan jiya, suka ziyarci Shugaban kasa (mai jiran gado a lokacin) domin su sanar da shi irin rikice-rikicen da suke faruwa tsakanin al’ummar manoma da kuma makiyaya. Wannan ziyarar ta bijiro da irin kalubalen da […]

Magance rikici tsakanin manoma da makiyaya a Binuwai
Magance rikici tsakanin manoma da makiyaya a Binuwai

Tun kafin a kai ga rantsar da shi kwanakin baya, Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya jagoranci wata tawaga a watan jiya, suka ziyarci Shugaban kasa (mai jiran gado a lokacin) domin su sanar da shi irin rikice-rikicen da suke faruwa tsakanin al’ummar manoma da kuma makiyaya. Wannan ziyarar ta bijiro da irin kalubalen da ake samu a jihar na tsawon shekarun da suka gabata. Hasali ma, a yayin da wannan tawaga ke kan tafiya zuwa Abuja, sai ga rahoto na bayyana Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Biniwai, Mista Hyacinth Dogara yana cewa an zargi makiyaya da kashe mutane 25 a wasu kauyuka da ke karamar Hukumar Logo. Mutanen kauyukan ma sun ce yawan mutanen da aka kashe sun haura wannan adadi, domin kuwa su da kansu sun binne mutane 100 a kabarin bai daya.

Wani jami’in gwamnati da ke zaune a yankin, Chif Joseph Amawah ya bayyana cewa makiyayan da ake zargi, sun bayyana ne da sanyin safiya, suka far wa sansanin ’yan gudun hijira da ke Ukara, Gafa, Per da kuma Gusa, inda suka kwashe kusan awa shida suna kashe-kashe da lalata gidajen mutane.
Ko a watan jiya ma, an kashe mutane uku, a lokacin da makiyayan da ake zargi suka kai farmaki garin Seneb a yankin karamar Hukumar Gwer, a yayin da kuma aka kashe wasu mutane 14 a hanyar Gboko da ke karamar Hukumar Tarka, makonni biyu bayan faruwar wancan kashe-kashen na baya.
Duk dai wadannan rikice-rikice, na bayan da kuma wadannan ke faruwa yau da kullum, an samu tabbacin suna afkuwa ne a sakamakon dadaddar rashin jituwa da ke tsakanin manoma da makiyaya dangane da burtaloli da kuma wuraren noma.
Al’amari ne mai sanya takaici ganin duk da irin kokarin sasanci da magance matsalar da wasu hukumomi a Jihar Biniwai ke yi amma duk da haka matsalar sai kara ta’azzara take yi. Abin takaici ne yadda ake ta samun salwantar rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da an kawo karshen haka ba.
A kokarin al’umma, na ganin an magance rikice-rikicen, an samu tattaunawa daban-daban bisa jagorancin kwamitocin addinai amma dai ba a samu nasara gamsassa ba. Haka kuma ba a samu sahihin bayanin tasirin da kwamitocin hadin gwiwa da gwamnatin baya ta kafa tsakanin al’ummar Tibi da ta Fulani suka yi ba, kasancewar wadannan kabilu biyu ne aka fi dora wa alhakin faruwar rikice-rikicen. Kwamitin kuma da ya hada har da bangaren jami’an tsaro na jihar.
Ala ayyi halin dai, ya kamata gwamnati ta kara kaimi, musamman ma ga sabuwar gwamnati ta shigo. Bai kamata Gwamna Ortom ya bata wani lokaci ba wajen hada hannu da duk sassan da suka kamata wajen tunkarar magance rikice-rikicen nan gaba daya kowa ya huta.
Haka kuma ya kamata su sassan da ke gaba da juna su san cewa babu makawa, ya zama tilas a zauna da juna cikin lumana, don haka wajibi ne a dauki matakan zaman lafiya da juna. Su sani kuma, daukar matakin ramuwar gayya ko yin arangama da juna ba zai magance rikice-rikicen ba, sai ma dai ya kara rurruta wutar gaba da haifar da rashin sukuni da zullumi, wanda kuma zai kara haddasa munanan rikice-rikice da asarar dukiya da bayyana fatara da talauci ga al’umma a jihar.
Kwamitin nan na sasanci, wanda ya kunshi membobin kungiyar Jama’atu Nasril Islam da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, bai kamata su yi sanyi ba wajen samar da shawarwari masu muhimmanci ga sassan da ke gaba da juna, sannan su bayar da tallafi na kai tsaye a inda ake bukata. Haka kuma ya kamata a hada da kungiyar Makiyaya ta Miyatti Allah a cikin kwamitin. Su ma sarakunan gargajiya, ya dace su kasance suna fadakar da al’ummominsu, su fahimta da muhimmancin zaman lafiya. Ya kamata kuma a karfafa jami’an tsaro da dukkan kayan aikin da suke bukata, domin magance matsala tun tana jaririya, ba su bari har sai al’amari ya ta’azzara ba.
Mutanen da ’yan sanda suka kama da hannu a rikicin kuwa, ya dace a dauki matakan bincike da shari’a yadda ya dace, sannan a hukunta duk wanda aka samu da laifi, domin hakan ne zai zama darasi ga na gaba. Gwamnati kuma ya dace ta ba sansanonin ’yan gudun hijirar da rikicin ya shafa kyakkyawan tsaro da kulawa, domin gudun kada su zama cikin barazana da tsoron sake afka musu.