Magance tabon fatarki

Akwai hanyoyi da dama wanda za a bi don magance tabo a fata amma a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki domin magance tabo a fata. Idan tabo ya yi yawa a fatar mace, yana boye kyawunta ,don haka ya kamata a kula da fatar jiki sosai. Ga abubuwa biyar da za a yi […]

Magance tabon fatarki
Magance tabon fatarki

Akwai hanyoyi da dama wanda za a bi don magance tabo a fata amma a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki domin magance tabo a fata. Idan tabo ya yi yawa a fatar mace, yana boye kyawunta ,don haka ya kamata a kula da fatar jiki sosai.

Ga abubuwa biyar da za a yi amfani da su domin magance tabo a fata kamar haka:
•Kurkum: A sami kurkum sai a hada shi da madarar ruwa yadda zai yi kauri sannan a shafa a kan tabo. A bar shi kamar tsawon minti biyar zuwa goma sannan a wanke. A ci gaba da shafa wannan hadin sau biyu a rana kamar tsawon watanni uku ko hudu.
•Lemon tsami: A yanka lemon tsami gida biyu sannan a yaryada masa siga sannan a dirza shi a kan tabon na tsawon minti biyar.
•Ganyen ‘Aloe bera’: A matse ruwan da ke cikin ganyen ‘aloe bera’ sannan a shafa a tabo na tsawon lokutan da za a iya bari, sannan sai a wanke. A rika yin hakan kamar sau biyu ko uku a rana . Sannan za a iya ci gaba da yin hakan har tsawon watanni uku.
•‘Baking soda’: Za a iya samun wannan a kantunan da a ke sayar da kayan hada ket. A hada garin da zuma a kwaba sannan a shafa a tabo a bari ya jima na tsawon minti biyar zuwa goma sannan a wanke da ruwan dumi. Za a iya yin wannan hadin kamar sau uku a sati.
•Man ‘Almond’: Yana na dauke da sinadarin bitamin E kuma yana taimakawa wajen goge tabo. A shafa wannan man a tabo har sai fatar wajen ta shanye man sannan a bar shi tsawon minti biyar zuwa goma. Sannan a sa auduga a goge, sai a wanke washe gari da safe.