Magance tozarta aure
Ina wannan rubutu ne a lokacin da zuciyata take cike da kunci, take cikin wani yanayi na tafarfasa kuma ruhina ya dimauta… kalaman da ke fitowa daga bakin kowa a yanzu shi ne na abin takaicin nan da ya shafi wata mace – matar aure kuma uwa da ake zargi da kashe mijinta sakamakon takaddama […]
Ina wannan rubutu ne a lokacin da zuciyata take cike da kunci, take cikin wani yanayi na tafarfasa kuma ruhina ya dimauta… kalaman da ke fitowa daga bakin kowa a yanzu shi ne na abin takaicin nan da ya shafi wata mace – matar aure kuma uwa da ake zargi da kashe mijinta sakamakon takaddama a tsakanin ma’auratan wadda ta koma abin kaico.
Ina cike da kaduwa da bakin ciki game da zarge-zargen da ake yi, kuma a matsayina ta ’yar kallo ko fiye da haka raina ya yi matukar baci. Eh, ya baci sosai!
Kamar yadda masu tsegumi suka fada dalilin aukuwar wannan abin kaico shi ne…
Matar amarya ce kuma uwar ’ya’ya ga mijin da yake da ’ya’ya takwas. A ranar da lamarin ya faru ta shiga gidansu na aure kwatsam ta iske shi (mijin) yana magana da budurwarsa a tarho, kuma bisa rashin damuwa ko izza yana maganar ce, sifikar tarho din a bude; dukan kalaman nuna soyayya da kwarkwasa da suke yi suna shiga kunnen matar. Shin abin mamaki ne matar ta ji zafi ta kuma fusata? Kuma a kokarin ta kwace wayar daga gare shi ne ya cije ta a hannu, daga nan sai kokuwa ta kaure kuma a kokarinsa na ya kwace wayar daga hannunta, kila ta hanyar nuna karfi da kokuwar da suke yi ne ya fado ko kuma bisa kuskure ta turo shi daga saman bene. Faduwa ce da ta zo da mugun hadari inda ya rasa ransa. A nan zan nanata cewa ba wai ina goyon bayan tashin hankali kowane iri ba ne ko ta kowace irin fuska ko yanayi ba, kuma ba na goyon bayan daukar ran wani ko a dauki namu. Allah Madaukaki Ya ce a cikin Alkur’ani: “Saboda haka muka hukunta a kan Bani Isra’ila cewa wanda ya kashe rai daya ba tare da hakki ba, ko watsa barna a bayan kasa (kamar fashi da makami ko satar mutane ko ta’addanci), to kamar ya kashe mutanen duniya ne baki daya; kuma wanda ya ceci rai daya kamar ya ceci rayukan mutanen duniya ne baki daya.” (K:5:32).
Ina tsaye kyam wajen nuna matukar adawa da cin zarafi ko tozarci a tsakanin ma’aurata daga kowane bangare. Abin da yake girgiza ni sosai game da wannan lamari shi ne tunzurarwar da aka yi wa wannan mata. Ta yiwu tana sane da cewa duk da mijinta yana da mata biyu da ’ya’ya takwas yana kuma da wadansu ’yan mata a waje. Wani faifan murya na uwargidansa ya tabbatar da cewa ya saba magana da ’yan mata a gabansu.
A wannan rana amaryar ta ji haushi sosai inda ta sauko kasa ta shaida wa uwargidanta, wadda ta ba ta baki cewa ta kyale shi ta yi hakuri kawai. Sai dai kuma a wannan bakar rana ta kasa jurewa.
Don haka ta koma saman benen kuma ta iske yana ci gaba da nuna isarsa a gabanta, cin mutuncin ya ishe ta, kuma ga alama hakan ya tunzura ta, ta zo har wuya. Fushi da bacin rai da zafin wulakanci suka sa ta mayar da martanin da ta mayar, kuma babban abin takaici, sai wannan abin bakin ciki ya biyo baya.
Na rubuto wannan ne ba don in yi wa shari’a riga malam masallaci ko katsalanda ba. An riga an rasa rai, kuma bayan bincike da bin diddigi, doka za ta yi aikinta. Na rubuto wannan ne saboda abin ya jefa ni cikin dogon tunani kan halin da al’umarmu ke ciki, kuma hakan yana matukar ba ni mamaki… wace irin al’umma ce za ta goyi bayan wani mutum ya rika aikata ba daidai ba kuma ta yi shiru a kan haka? Amsar tana kada ni, tare da ba ni tsoro.. saboda an aikata haka ne a kan mace. Ga dukan maza da kuma matan da suke kirana a yanzu cewa NI BA CIKAKKIYAR MAI KARE HAKKIN MATA BA NE, ina shaida musu cewa na yi imani har cikin zuciyata Allah cikin hikimarSa Ya kafa wasu tsararru kuma ayyanannun dokoki da ka’idoji ga dukan jinsunan biyu, kuma tilas ne su bi su kamar yadda Ubangiji Ya shirya musu. Kuma saboda Ya ce: “Maza masu tsayuwa ne a kan mata saboda abin da suke ciyarwa a kansu.” (K:4:34), ba yana nufin maza ta ko’ina sun fi mata ba ne.
Allah Suuhanahu Wa Ta’ala Ya sake cewa: “Ya ku mutane! Lallai ne Mun halicce ku daga namiji da mace, Muka sanya ku dangogi da kabilu domin ku san juna. Lallai ne mafificinku a wurin Allah, shi ne mafi takawarku…” (K:49:13).
Na yi imani Allah Ya halicci jinsunan nan biyu kowane da irin karfi ko gazawarsa da kyawawan halaye da munana da wasu kananan abubuwa na gazawa. Kuma na yi imani Allah Ya halicci mace da namiji a matsayin daidai suke da juna. Mafi kusanci da Shi kamar yadda Ya ce, su ne wadanda suka fi karfin imani, to me ya sa a al’ummarmu take kallon mace a matsayin rabi marar karfi, mai matukar rauni?
Mun taso shekara da shekaru ana rainanmu mu rika tunanin muna duniya ce kawai don mu rika kula da maza, abin da kawai za mu yi shi ne mu gamsar, mu girmama mu bi tare da biyayya gare su. Iyayenmu mata sun koya mana abin da aka koya musu kamar yadda aka koyar da nasu iyaye mata. An takaita mu a haka. Kuma irin hakan muke koya wa ’ya’yanmu mata masu kazar-kazar. Mun kwace musu ’yancin tunani na kashin kansu ko hangen nesa ko kwazo mun mayar da su dolaye wasu sandararrun halittu da za a rika juya su yadda aka so a mayar da su tamkar bayi.
Daga cikin abin da aka koyar da ni, na amince kacokan da abin da ake kira GIRMAMAWA. Duk matar da ta samu miji nagari mai mutunci hakika ta samu babban alheri. Zai kasance karfinta, mai tallafa mata kuma ya taitaye ta domin yana jin ita bangare ne na jikinsa. Kashin bayan kowane aure shi ne a samu cikakkiyar girmamawa a tsakanin juna. Aure ba zai tabbata ba in babu haka. Na dasa haka ga ’ya’yana. Ma’ana na koyar da su GIRMAMA KOWA.
Lokaci ya yi gare mu da za mu yi wadannan tambayoyi: Nawa ne daga cikinmu muke tarbiyyantar da ’ya’yanmu maza kan wannan hanya? Nawa ne daga cikinmu muke koyar da ’ya’yanmu maza su girmama mata? Shin miji da mace ba rabin juna ba ne? Yaya za a yi a yi aure ba tare da miji da mata ba? Shin aure ba haduwar tunani da jiki da ruhi ba ne? Idan haka ne, ashe matsayin abokan zaman aure ba daya ne da na dayan ba? Mutum yana iya gina gida da dukiyarsa, amma sai ya kasance fanko, har sai mace ta cika shi da soyayya, murmushi da farin ciki, sannan ta mayar da shi gidan zama.
Lokaci ya yi a kanmu mu mata a matsayinmu na iyaye, yayin da muke koyar da ’ya’yanmu mata kan kada su yi kaza, mu kuma koyar da ’ya’yanmu maza kan yadda za su yi kaza. Wajibi ne mu raini ’ya’yanmu maza su kasance maza na hakika. Namiji na hakika ba ya daukar kansa wani zaki da zai cutar da matansa, ta hanyar yi musu ihu ko nuna karfi. Miji na hakika ba ya jin dadi a duk lokacin da matarsa take jin zafi. Miji na hakika ba ya son tattake matarsa, ya fi son su rika tafiya kafada-da kafada.
Don haka mu tarbiyyantar da ’ya’yanmu maza su san soyayya. Su girmama mata, su ma su girmama su. Su tafiyar da karfin jikinsu yadda ya dace kuma su san cewa a lokacin da miji ya ba matarsa girman da ya kamata, za ta ba shi zuciyarta har abada.
Mu raini maza masu tasowa su tsaya kan kafafunsu ba wai saboda su rika take raunana ba, amma domin su ciccibo su. Ya kamata nan da kankanen lokaci ya zamo ba a samu wani mutum da gangan yana musguna wa wata mace ba saboda kawai zai iya, ko saboda ta riga ta shiga gidansa. Kuma kada wata mace ta rika jin ita mai rauni ce don haka ba ta san kimarta ba. Kada wata mace ta kasance abokiyar gaba ga wadansu. Mu hadu gaba daya mu karfafi juna. Kada mu rika jin tsoro wajen fadada burinmu da cimma manufofinmu; wajen kara neman ilimi don tsayawa da kafafunmu.
Mu yi dukan wadannan ’yan uwa maza da mata; mu hadu mu gina wani abin kirki na girmama juna, soyayya da tausayi da jinkai domin ’yan baya masu tasowa da wadanda za su biyo bayansu
Hajiya Maryam ta rubuto wannan mukala ce daga Kano