Magance yawan saki: Za mu kafa makarantar koyar da zaman aure – Sheikh Umar Fagge

Aminiya: Allah gafarta Malam watannin baya ka taba yin bayanin yadda za ku kafa makarantar horar da masu niyyar yin aure, ko yaya lamarin yake: Sheikh Umar Fagge: Bismillahir rahmanir rahim. Alhamdulillahi rabil alamin. Bayan haka dangane da mutuwar aure da ake samu a kasarmu, abin ya dame ni sosai kuma na san tun zamanin […]

Magance yawan saki: Za mu kafa makarantar koyar da zaman aure – Sheikh Umar Fagge

Aminiya: Allah gafarta Malam watannin baya ka taba yin bayanin yadda za ku kafa makarantar horar da masu niyyar yin aure, ko yaya lamarin yake:

Sheikh Umar Fagge: Bismillahir rahmanir rahim. Alhamdulillahi rabil alamin. Bayan haka dangane da mutuwar aure da ake samu a kasarmu, abin ya dame ni sosai kuma na san tun zamanin da Janar Gowon yake mulki ya nemi wadansu daga cikin manyan malaman jami’a da suka karanta fannin halayyar dan Adam “Sociology” a kan su ba da shawarwarin da za a rage mutuwar aure da yawan shari’a a kotuna inda za ka ga tsakanin wanda ya auri ’ya da surukar da ta haifi matarsa sun tsaya a gaban alkali suna fadi in fada. A wancan lokacin yana Shugaban kasa ya ce wannan abin ya kamata a duba shi, ya yi iya nasa, amma ba abin da aka yi. Sai na ga wani shiri na Aljazeera da suka yi, inda suka dauko matsalolin kasar Malesiya wadda suka bude wata cibiya da ke ilimantar da wadanda suke da niyyar yin aure maza da mata a dauki watanni kamar uku ana ba su horo su gama a bai wa kowa shaidar kammala samun horo. Daga fara yin wannan shiri, sai kididdiga ta nuna cewa kashi 37 cikin 100 na mutuwar aure ya tafi. A nan ne na san cewa akwai nasara a wannan shiri. Sannan a Saudiyya suna da cibiya ta kula da irin wannan inda in aka gama wannan karatu suke bai wa mutane takardar shaida, har da kyaututtuka. Sai muka yi kokarin ganin mun samu na Saudiyya, kuma an duba a cikin shafinsu na Website, aka samu wasu abubuwa, don haka muka ga kanu-kanu suka bayar.

Saboda haka su kuma Malesiya da muka tashi sai muka yi amfani da wani dalibi dan Najeriya dan Kano da ya tafi karatun digiri na uku Ph.D. Sai na gaya masa cewa ya bincika, da ya je ya bincika bai samu ba. Da ya kara zuwa ya bincika sai ya samu, amma ya ce ya fahimci cewa su Malesiya ba mutanen da suke son sakin abinsu kowa ya sani ba ne. Sun tabbatar masa cewa ana yi, suka rubuta wani abu, wanda ba zai iya kashe kishin ruwa ba balle yunwa ba. Wato sun ce masa ana yi, amma suka yi dungu; ba su fito da ainihin tsare-tsaren ba. Wannan dai ya sanya muka ga cewa ya kamata a duba wannan, sai muka tashi tsaye. 

Aminiya: Yaya Malam ke ganin za a warware matsalolin da ke kawo matsala a aure?

Sheikh Umar Fagge: A Kano aka taso ana cewa ya kamata a yi dokoki kan yawan0 mutuwar aure, inda muka zauna da Majalisar Malamai aka duba aka ga cewa wannan bai zai warware matsalar ba. Matsalar a jikin mutane take. Sai an sake yi wa mutane zubi da tarbiyya sun san mene ne hakkokin aure sun samu horo a kai, sannan za a samu sauki. Wannan ya sanya na yi kokarin rubuta littafi, wanda shi za a koyar da yadda za a yi auren; mazan da matan. Akwai abubuwan da suka shafi mace ko namiji. Akwai abubuwan da maza suka shafa; akwai abubuwan da mata suka shafa, mun ware su. Muka yi su kashi-kashi.

Sannan mun rubuta manhaja, wadda ita za a bi, wajen koyar da su wannan darasi. Sai muka yi tsari na gudanar da al’amura, wato yadda za a buga takardun shiga da yadda za a shiga da kuma shugabannin gudanarwa wadanda za su kula da yadda ake tafiyar da al’amarin. Mun ware mata, akwai makarantu da muke da su, wadanda mata su kadai ne, su ne wadanda za mu zauna da su a ba su horarwa su kansu matan. A nuna musu ga abin da ake so, ga littafiin wanda shi za su bi. Haskensa za su bi su rika karantawa, a rika koyar da su yadda zaman aure yake. Kowace kafin a yi mata aure da wata uku. Watan farko za a fara nusar da ita abin da ake so.To wadannan abubuwan guda uku su muka yi. Sannnan in an yi mako uku a na hudu, sai a tara su gaba daya, mu zaunar da su mu yi musu lacca ta baki daya wadda za mu ga abin da muka dora su a kai ko sun fahimta. Mu kara kawo musu abin da zai zo nan gaba. Shi ma wata na biyu in ya zo, za mu tara su a rufe shi da wannan. Sai a wata na uku in ya gama sai mu rufe da wannan, sai a ba su shaidar kammmalawa. Maza su ma haka za a yi. Sannan malaman da za su koyar an zauna da su, an tattauna da su sun fahimci abin da ake tafiya a kai da abin da litttafin ya kunsa game da aure da muhimmmancinsa; ina girma yake, ina daraja take; ina girmamawa take; ina cude ni, in cude ka yake; ina neman lada wajen Ubangiji Tabaraka wata’ala yake; ina yadda ake iya rike harshe; ina yadda ake iya yin hakuri. Duk dai yadda namiji zai san mene ne aure, mace ta san mene ne aure, har yadda za a rubuta bayanan katin gayyatar aure da tsara yadda za a yi shi, saboda katin gayyatar aure ya zama sha-ka-tafi; in mace ko saurayi za su yi aure ba sa sanin me gidajensu ke ciki. Mu a tsarinmu kowane gida akwai irin tsarinsa akwai shugabanci. In za a saka suna ko lakabin da za a rubuta a jikin katin aure, kawai iya abin da ta sani shi take gaya wa ango, shi ma in ya tashi haka zai je ya yi in sun tashi sai su je su rubuta abinsu, in abin ya fitto in mahaifinta babba ne a zuriyarsu sai ya ji kunya; sai su ce ya yi gaban kansa ya dauki sunansa ya bai wa ’yarsa ta bayar wanda shi kuma bai sani ba. To shi ya sa muke son nusar da su duk wadanda za su yi sai a koma wajen iyaye su ce ga abin da suke so a rubuta, wato iyalan wane kaza-kaza, suna yin kaza da kaza. Sannan  ranar da za a yi da daidai lokacin da za a yi da muhallin da za a yi ya zamana iyaye ne za su fitar sannan su ba su su je su buga. Duk mun shirya wadannan abubuwan yadda ya kamata a rika yin su.

Aminiya: Akramakallah, shin wanda ya taba yin auren zai kyautu ya sake halartar wannan makarantar don shi ma a ba shi wannan shahada?

Sheikh Umar Fagge: Wanda ya taba yin aurre in yana so zai shiga makarantar ai karuwa ce, zai karu da abubuwa irri-iri. Wanda ya taba yin aure in wata matar zai kara ana iya ba shi wani abu wanda ya shafi wannan shi ma, a nusar da shi ga yadda zai yi. Ita ma matar inda za ta je in da kishiya sai an kokkoya mata yadda za ta zauna da kishiyar. Ga yadda za ta zauna da ita lafiya, ga yadda za su zauna da mijinsu lafiya. In shi ne kuma ga yadda zai kula da mata. Ba yadda suke zama kamar gwalando ba, kowane da an taba shi ba zai iya hakuri ba. Duk sai an nusar da shi wadannan al’amura. Saboda haka dai shi ma zai iya.