Maganin hana tsufa
Wata yarinya ce da ta samu gurbin karatu a kasar China, za ta karanta kimiyya. A cikin bincikenta sai ta gano wani magani da yake mayar da tsoho ya koma yaro. Sai ta aiko wa da iyayenta wannan magani tare da rubutacciyar wasika game da bayanin yadda za a sha maganin. Ta ce: “Baba da […]
Wata yarinya ce da ta samu gurbin karatu a kasar China, za ta karanta kimiyya. A cikin bincikenta sai ta gano wani magani da yake mayar da tsoho ya koma yaro. Sai ta aiko wa da iyayenta wannan magani tare da rubutacciyar wasika game da bayanin yadda za a sha maganin. Ta ce: “Baba da inna, a sakamakon karatun da kuka tura ni, na samu ci gaba sosai. Shi ne na ga ya dace a ce na aiko muku da maganin hana tsufa. Cokali daya kadai kowannenku zai sha. Kada fa ku manta, cokali dai-dai nace kowa ya sha.”
Da suka amshi magani, sai maigida ya ce wa matarsa ta fara sha ya gani. Da ta sha sai ta dawo ’yar shekara 23, ga kyau. Ganin hakasai kishi da kyashi suka kama shi, ya fizge kwalbar maganin daga hannunta, ya zuke shi gaba daya. Bayan shekara biyu, yarinya ta dawo hutu gida, sai ta samu innarta tana goye da jariri. Ta ce mata: “Inna kin haihu ne, ina baba yake?” Innar ta yi dariya , ta amsa da cewa: “Wannan yaron da nake goye das hi, babanki ne, ya koma haka, saboda ya shanye kwalbar maganin nan duka, wai don yana so ya fi ni kyau da kuruciya.”
Daga Buhari Liman Kudan.