Maganin kada a ji dai, kada a yi
’Yan Najeriya sun saba jin yadda ake zargin shugabanninsu na siyasa, wadanda ke rike da madafun iko, ko kuma suke bisa kujerun wakilci a majalisu, kuma sun tabbatar da cewa irin wadannan mutanen ba su damuwa game da haka, domin a wajensu abin kunya gaba suke ba shi, ba baya ba. Ai gindin kura ya […]
’Yan Najeriya sun saba jin yadda ake zargin shugabanninsu na siyasa, wadanda ke rike da madafun iko, ko kuma suke bisa kujerun wakilci a majalisu, kuma sun tabbatar da cewa irin wadannan mutanen ba su damuwa game da haka, domin a wajensu abin kunya gaba suke ba shi, ba baya ba. Ai gindin kura ya saba da raba, domin kuwa babu wani abin da zai ba talakawa mamaki, ko ya dada su da kasa game da zarge-zarge, musamman ma wadanda a halin yanzu manyan shugabannin Majalisar Wakilai ke yi wa junansu game da cuwa-cuwar da suka tattafka a cikin kasafin kudin bana, wanda a Turance ake kira Padding, kalmar da Shugaba Muhamadu Buhari ya ce bai taba jin ta da kunnensa ba, domin kuwa wata sabuwar shegantaka ce da aka bullo da ita don handamar dukiyar talakawa kamar shekaru shida da suka wuce. Kaico! Cuwa-cuwa iri-iri sun zame ababen ado a majalisar Wakilai.
To, ai ita ma dattijan majalisar da ake gani sun fi gaban kukan aski ba su tsira ba daga irin wadancan zambace-zambacen da ake tattafkawa don kwarar talaka. An dai tabbatar da cewa yin magudi a cikin kasafin kudi hakkun ne, kamar da kasa wai in ji mai ciwon ido. Wasu tsirarun dattijai, ko wakilan jama’a kan yi haka, ba kunya, ba tsoron Allah don biye son zukatansu. Hakan kuwa babban hadari ne ga dorewar dimokuradiyyarmu, domin babban alaifi ne da ke cutar da kasa da kuma hana ta yunkurawa don kai wa ga kasaita. Abu ne kuma da kowa zai yi tir da shi, kwarai kuwa, domin haka illa ce babba!
A ’yan shekarun baya an sha samun rahotanni game da zargin rashawa da cin hanci a cikin Majalisun biyu da kuma yadda wakilai ke shafawa fuskokinsu bula, suna dunkule manyan yatsun hannuwansu, suna ba hammata iska a gaban kyamarorin da suka tabbatar duniya na kallo, ciki har da mata da ’ya’yansu da surukansu, babu abin da zai dame su. Sau da yawa za ka ji an zargi wasu da yin zinace-zinace barkatai, a gida ko kuma a can ketare. Wadannan abubuwa ba abin damuwa ba ne a gare su, wadanda suka ji, ko suka gani ne za su ji kunya, su ba ruwansu, abin duniyan da ya kai su ga yin haka kawai suka fi damuwa da shi. To amma daga cikin wadancan fitintinun da ake cewa ’yan majalisa na janyo wa talakawa babu wanda ya kai munin cuwa-cuwar padding, domin ta haka ne ’yan majalisu ke bi, suna wawure dubban daruruwan miliyoyin Nairori da gwamnati za ta ganganda, ta yi wa jama’a ayyukan da za su fitar da su daga cikin kangin fatara da mayata. Idan ba ta haka ne ba, yaya dan majalisa, walau dattijonta ne, ko kuma wakilin fakiran talakawa, zai samu makudan kudin da zai yi ta bushasha da su kamar wanda bai san zafin nemansu ba, ko wanda ya ci fare da gau, domin a fayu ya same su? Ai ta haka ne shi ma dattijo, ko wakilin majalisa zai yagi nasa haram din daidai da yadda shugabannin siyasa da ke rike da madafun iko, ko manyan jami’an gwamnati ke kankarar tasu haram din daga dukiyar talakawa.
To, idan kuwa haka ne ana iya cewa ko wakilan jama’a a majalisun biyu na sane da yadda talakawan da suka tuttura su wakilci ke sa ran cewa za su yi musu ingantaccen wakilcin da zai tserar da su daga wahalhalun da ke addabarsu? Ina! Ai su tun da dai gani suke jifa ta wuce kansu, to ta fada can kan mai-uwa-da-wabi, su ba ruwansu. Labudda, dukkan kokarin da za a iya yi don a yi cuwa-cuwar da ba ta dace ba a cikin kasafin kudin da za a yi wa talakawa aiki da shi, kamar yadda ake zargin ’yan majalisa da yi a halin yanzu abin kyamata ne, domin kuwa hakan rashin imani ne, irin wanda zai kai ga cin amanar jama’a. Wajibi ne a tabuka wajen magance wannan muguwar dabi’ar ta hanyar hukunta wadanda duk aka samu da laifi bayan an gurfanar da su gaban kotu, a kuma yi musu hukunci mai tsananin gaske.
Dangane da haka ne talakwa ke bukatar yin cikakken binciken da zai kai ga zazzargo dukkan wadanda suka yi zarge-zargen da suke neman zubar da mutuncin shugabannin majalisar Wakilai. Dangane da haka ne ake gani zai fi kyau a kawo wasu can daban, ba shugabannin majalisar ba, don bin bahasin dambarwar da ake cabawa a cikin majalisa. Ta haka ne kawai za a tabbatar da gaskiyar al’amari, a kuma gano dabarun toshe kafafen afkuwar irin haka nan gaba. Wadannan zarge-zargen dai suna da nauyin gaske, kuma bai kamata ba a bankada gefen tabarma, a watsa su karkashinta ba, don boyewa. Ka da kuma a ce ai abin da ke faruwa a cikin majalisar al’amari ne na cikin gida ko kuma na abokan aiki, saboda haka nan a bari don a sasanta.
’Yan Najeriya dai na bukatar ganin wakilansu a kowace irin majalisa ce, walau ta jiha ce ko kuma ta tarayya, suna sane da irin nauyin jama’a da ke kansu, suna kuma kokartawa don saukewa, ba tare da sun barar ba. Abin takaici shi ne tun a ’yan shekarun baya, ’yan majalisa sun huda, sun ga jini game da cuwa-cuwa a cikin kasafin kudi, shi ya sa a yanzu muka ga yadda suke nuna hadamarsu a fili wajen yin sama da fadi da dukiyar jama’a don amfanin kawunanasu, su kadai. To, fa yanzu lokaci ya yi da za a bi a tottoshe dukkan ramukan gafiyoyin majalisa, inda suke tserewa da na bakinsu, suna adanawa. Kasafin kudi dai muhimmin aiki ne da ake gabatarwa don kai wa ga biyan bukatu a fannonin zamantakewa da tattalin arziki da kuma inganta halayyar rayuwar jama’a. Ashe ke nan bai kamata a mayar da kasafin kudin da aka amince da shi bai kamata a yi wa kasafin kudi giwa-ta-fadi ba bayan an amince da shi, ’yan majalisa su dinga fiddo da zabga-zabgan wukakensu suna ta yankan nama. An dai ce maganin kada a ji, kada a yi, to ga shi can ’yan majalisar wakilai na barbaza abin kunya tsakaninsu, jama’a kuma sun rasa ta cewa dangane da haka. To kar dai allura ta tono garma, ko ta kai ga hadiyar tabarya, a yi ta kwana a tsaye.