maganinfitinarshaawa1
Assalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani da zai amsa tambayoyin da da masu karatu matasa suka aiko kan yadda za su magance matsalar matsananciyar sha’awa da ta addabi rayuwarsu, da fatan Allah […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani da zai amsa tambayoyin da da masu karatu matasa suka aiko kan yadda za su magance matsalar matsananciyar sha’awa da ta addabi rayuwarsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Tambaya
Malama Nabila don Allah ki yi man bayani game da mutum mai yawan jin sha’awa kuma ga shi babu yadda za ai gidansu a yi masa aure saboda karatu ga shi kuma yana jin tsoron aikata fasikanci don ya san hukuncin wanda ya yi haka wurin Allah; don Allah wadanne hanyoyi zai bi don magance matsalar? Daga Haidar.
Amsa: Ga hanyoyin da matashi zai bi don yakar matsananciyar sha’awa ya kasance ba ta kai shi ga fada wa cikin halaka ba:
Fahimta Kyakykyawa: Abu na farko na maganin wannan matsala shi ne ta hanyar yi mata cikakkiya kuma kyakykyawar fahimta:
Ø Matsananciyar sha’awa wani yanayi da sha’awar mutum ke yawan motsuwa nan da nan kuma kusan kowane irin lokaci, musamman a lokuttan da ba ya bukatar motsuwarta. Wannan yanayi yana faruwa ga duka masu aure da marasa aure, maza da mata, kuma yana takurawa ga rayuwarsu, sannan yana jefa wasu ga yin zinace-zinace; zinar hannu da kallon fina-finan batsa, wadanda duk wasu muggan ayyuka ne da ba su kawo sauki ga matsalar sai dai su kara ruruta ta, sannan suna kawo bakantar dabi’ar masu aikata haka da raunana masu imaninsu.
Yana da kyau ga mai fama da matsananciyar sha’awa ya fahimci cewa, sha’awa ba komai ba ce illa daya daga cikin al’amuran gudanarwar jikin dan’adam da Allah Ya halitta shi da su. Kamar yadda wani ya fi wani tsawo; wani da saurin fushi wani kuma da sanyin zuciya, to haka sha’awa ta bambanta tsakanin mutane ta fuskoki daban-daban. Kamar yadda mai tsananin fushi Allah Ya hore masa iko da damar dannewa da hadiye fushinsa, to haka ma mai tsananin sha’awa yana da cikakken ikon da zai danne sha’awarsa, ya kasance sai lokacin da ya bukace ta ne kadai za ta yi tasiri a cikin rayuwarsa da harkokinsa na yau da kullum. Ka da mutum ya ce ai ni haka Allah Ya yi ni, don haka ya doge da savon Allah yana cutar kansa, Allah SWT bai halitta varna a cikin ko da daya ne daga cikin halittunSa ba, sai dai shi abin halittan ya jawo wa kansa varna da abin da Allah Ya halitta masa. Mu lura mu gani zuwa ga shukokin da Allah Ya azurta mu da su, kowace shuka Allah Ya aje ta a mafi dacewar waje da yanayinta, kuma Ya hore mata abubuwan da za ta girma ta yadu a wannan wajen. Don haka ko me Allah Ya ba mutum, shi ne daidai abin da zai yi amfani da shi ya girma, ya yadu, ya kuma yi nasara a duniyarsa da lahirarsa. Haka kuma tsananin sha’awar da Allah Ya ba wani na iya zama wata jarabawa ce da Allah Ya yi nufin Ya jarabci bawanSa da ita, in mutum ya yi hakuri ya jure, Allah Zai saka masa da mafi kyawun sakayya.
Ø Kasancewa cikin matsananciyar sha’awa na nufin yawan sinadarin sha’awar da ke cikin jini ya wuce yadda ya kamata. Abubuwa da dama, masu nasaba da juna ne ke haddasa matsananciyar sha’awa ga dan’adam:
1. Akwai wadda ke faruwa a dalilin yanayin halayya da yanayin tunane-tunanen da ke zirga-zirga cikin zuciya da ma’aikatar hankalin mutum, da yanayin dawwamammen tunanin da ke cikin ma’aikatar hankalin dan’adam. dabi’antu da yawan kallon matan da ba muharramai ba, da yawan tunane-tunane na alfasha, da kallon fina-finan batsa, duk ayyuka ne da ke rura wutar sha’awa cikin zuciya da jiki.
2. Haka kuma matsananciyar sha’awa na faruwa a dalilin faruwar rikirkicewa cikin jerin gwanon sinadaran da kwakwalwa ke yawo cikin jini musamman masu nasaba da sha’awa. Duk lokacin da adadin wani sinadari ya daga ko ya kasa adadin daidansa cikin jini, wannan zai haifar da faruwar al’amuran cikin jikin dan’adam sama ko kasa da daidai faruwarsu. Abubuwa da dama na haifar da rikirkicewar sinadarai cikin jini, kadan daga ciki sun hada da mugunyar gajiya (stress) da kuma kasancewa cikin tsananin huzni na iya rikitar da kwakwalwa har ta saki adadin sinadarin da ya wuce daidai cikin jini.
3. Tabbatuwa kodayaushe cikin kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa; na iya sa sinadaran sha’awa su yawaita cikin jini.
4. Wani ciwo ko wata cuta da ke damun daya daga cikin manyan namomin jikin dan’adam masu gudanar da al’amura, na iya haifar da karuwar sinadarin sha’awa cikin jini;
5. Haka nan wasu magungunan warkar da wata cutar na iya yin tasiri ga karuwar sha’awa cikin jiki.
6. Cin kayan dadi masu kara lafiya; yawan motsa jiki da yin ayyukan karfi na kara yawan sinadarin sha’awa (Testosterone) da ke cikin jini.
7. Ga matashi sabon balaga, yawan motsuwar sha’awa wani vangare ne na cigaba da girmansa, in ya daure ya jure, a hankali zai wuce wannan lokacin, amma in ya fara neman sauki da zinar hannu ko wani abu makamancin haka, to tsanantuwar sha’awarsa za ta yi ta karuwa ne kadai.
Sai sati na gaba in sha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.