Magatakardan Jami’ar BUK, Jamilu Salim ya rasu
Ya rasu yana da shekara 60 bayan gajeruwar jinya
Magatakardan Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) Jamilu Ahmad Salim ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
A safiyar Laraba aka gudanar da jana’izarsa, kana aka binne shi a Makabartar Dandolo da ke Kano.
Hukumar gudanarwar jami’ar BUK ta ce ya rasu ne bayan gajeruwar jinya.
Kafin rasuwarsa dai shi ne magatakardar BUK tun daga shekarar 2021, bayan maye gurbin Hajiya Fatima Bint Muhammad da ta shafe shekaru biyar kan matsayin.
An haife shi a ranar 21 ga watan Nuwamba a 1963 a unguwar Gwale da ke Kano, kuma ya kammala digirinsa na farko a Fannin Hausa/Islamic Studies a shekarar 1988.
Haka kuma ya yi babbar Difloma (Post graduate) a fannin Siyasa da Gudanarwa da kuma digirinsa na biyu a fannin Kasuwanci da Dokoki duk a Jami’ar Bayero ta Kano.
Malam Salim ya fara aiki da BUK a shekarar 1990, kuma ya shafe shekaru tara kafin komawa aiki da Hukumar Shirya Jarabawar (NECO) a 1999 inda ya shekara daya, sannan ya sake dawowa aiki da jami’ar a shekarar 2000.
Hakazalika ya yi aiki a bangarorin jamiar da dama kafin zamowarsa magatakardan jamiar a watan Oktoban 2021.
Da fatan Allah Ya ji kan sa, Ya kuma yi masa rahama. Amin.